Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 117

Chapter 117

Gidan Aro Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Ashe idan baki gode masa ba har zaki wulak’antasa.. Ke bandama taimakon Ubangiji ina zaki samu miji irin Mu’azzam.. Har kina wani gindaya masa sharud’a shi bai miki haka ba.. Tun wuri ki wuce kije ki duk’a ki bawa mijinki hak’uri tun kafin Ubangiji baiyi fushi dake ba.” Ta mik’e tana goge hawayenta. Tin kafin Ta zauna Umma Ta lek’o tana fad’in “Mu’azzam ka dena biye ma wann taurin kan nata, ta shirya maza ka d’auketa ku tafi bazata kuma kwana mana a nan ba..” Ya murmusa kad’an yace “A’a Umma ba damuwa ai tafiyar ma zai kai zuwa thursday in sha Allah.. Ai hak’uri Umma..” Ya fad’i yana duban Sadiya dake goge fuskarta da mayafinta. Umma Ta aika mata mugun kallo kafin tace “Kinci albarkacinsa.” Tai k’wafa kafin Ta janyo k’ofar parlorn ta basu waje. Sai goge hawayenta take ba tareda Ta dubesa ba. Ya k’araso ya kamo kafad’unta ya zaunarta saman kujera. Hannunta ya cire ya shiga goge mata hawayen nata da yatsun hannunsa “I didn’t mean for this to happen.. I believe Umma bata San wasa kike ba.. Mission d’inmu bazai tab’a k’arewa ba har mu koma ga Ubangijinmu... Every day is another mission for us to accomplished..” Ya k’arashe yana mai mak’aleta gefen k’irjinsa na dama. Bata iya furta komai ba Sai lamo da tai cikin k’irjin nasa tana ajiyan zuciya. Bashi ya bar gidan ba saida yaci Dinner, ko bayan da ya tafi ma Sabon fad’a Umma ta dingayi ma Sadiya. Ta yanda take shiga bata nan take fita ba. Har saida Aunty Larai ta k’waci Sadiya hannun Umma. Umma Ta mik’e tana furta “Wanda duk bai gode ma Allah ba zai gode ma azabarsa barikiji na fad’a miki..” Daga haka shigewa tai ta bar Sadiyar da Aunty Larai tana lallashinta “Haba Sadiya har yaushe zaki bud’I baki kice mijinki ya sakeki, kin kuwa San zunubin dake cikin yin hakan.. Mutumin da kullum rawar k’afa yake akanki yana sintiri a nan safe da dare bama muzguna miki yake ba balle ace eh ga dalili.. Kar fah ki mance Mu’azzam mata biyu ke garesa kuma wacce duk tafi kyautata masa cikinku itace zata zamto mai babban matsayi cikin zuciyarsa koda bai furta hakan ba dan zuciya tana san mai kyautata mata ne..” Cikin kuka tace “Aunty wllhi fah ba sona yake ba kawai mission d’insa yake dani.. Umma bazata fahimci haka bane..” Aunty Larai Ta murmusa kafin tace “Salon nasa soyayyar kenan Sadiya.. Kuma Kema na tabbata kina son mijinki kawai dai halin namu na mata ne kike d’an masa.. Hakan nada kyau dan mu mata saida aji koh.. Amma ai a hankali kar ya zarce kima.. Ki natsu ki karanci mijinki kisan wanene shi Ina nufin d’abi’unsa da halayyarsa.. Idan kika karanci wad’ann kika San yanda zakiyi mu’amala dashi ina mai tabbatar miki zaki samu mijinki zaki tafiyar da gidanki yanda kike so.. Ba Wai asiri bane ko tsafi yake sa a mallaki Zuciyar miji.. A’a babu boka babu Malam idan kinaso zaki zama sarauniya wajen mijinki.. Tsananin biyayya da iya kula da buk’atunsa shi ke sa mace ta samu wann d’aukaka a wajen miji.. Sannan kafin ki iya wann sai kin karanci wanene mijinki.. Shiyasa wasu lokutan sai kiji ana cewa wasu matansu sun asircesu.. Wlhi babu boka babu Malam kawai sanin makaman rayuwa ne. Quite alright akwai masu mallaka da asiri amma kuma akwai masuyi da dabaru irin namu na mata da Ubangiji ya hore mana.. Idan yace mission bishi a mission d’in, ki rikitashi da naki salon mission d’in kinji koh.. Yana jefo miki assignment capke ki solving masa tun kafin ya kuma jefo miki wani yanda zaki zamto kece wacce kike basa assignments d’in bashi ba.. Ko wane d’an adam akwai halinsa da yake nature ne, wad’ann natural d’in sai kiyi adopting nasu since we can’t change what’s natural. Mace ita take raya gidanta kuma ita take kashe gidanta.. Duk wasu makaman yak’in Allah ya mallaka miki kawai saidai idan baki San yanda zakiyi amfani dasu ba. Kina jina.. Ki saki jiki ki tarairayi mijinki Mu’azzam na matuk’ar k’aunarki koda wasa kar ki bari gidanki ya kufce miki a hannunki.. Kula da miji ba gajiyawa bane sannan yi masa biyayya ba kasawa bane. Wad’ann sune zasu d’aga martabarki da Kimarki a idanunsa kinji koh.. Idan nace haka ina nufin tsafta kwalliya kula da muhalli iya sarrafa kayan abinci da girkasu Duk suna cikin tattalin gida kinji koh.. Muhimmi kula da buk’atarsa, so goma idan zai nemeki kar ko gwada masa kin gajiya, ko a fuskarki kar ki bari ya gane haka, wnn ba k’aramin kima da martaba zai k’ara miki a idanunsa ba Sanna k’aunarki zai ninku cikin zuciyarsa.. Ki gyara masa kanki ciki da waje, idan nace ciki da waje Ina nufin jikinki da kuma matantakanki.. Gyara ko a musulunci nada kyau dik abinda kika san zaisa mijinki yaji dad’i ya kuma samu gamsuwa dake matuk’a bai kauce ma shari’a ba Sannan baya cutarwa kina iya amfani da abinki dan gyaran gidanki.. Abu na gaba ki girmama iyayensa mahaifiyarsa ‘yanuwansa ki nuna masa suma naki ne. Abokiyar zamanki ki zauna da ita zuciya d’aya da alkhairi..” Sadiya kam sadda kanta k’asa tai tana d’aukan karatun Aunty Larai kaman D’alibi gaban Malami. Aunty Larai da ta kula kunyarta take tace “Ki saki jikinki dani kinji koh.. Ki tambayeni dik abinda ya shige miki duhu kinji koh.. Ni da Allah ya bani d’iya haka zan zama very open da ita, kafin ta sani a wani waje ni zan koyar da ita ta hanyar da ya kamata.. Tinda Allah bai bani d’iya ba gaki nan ya bani.. Ki saki jiki dani kinji koh babu wani kunya yanda zaki inganta rayuwar gidanki da auratayyarki nake k’ok’arin fahimtar dake kinji koh.. Maza tashi kije ki wanke fuskarki anjima zamu ci gaba.” Ta jinjina kai a hankali kafin Ta mik’e ta nufi bathroom. Aunty Larai ta bita da kallo fuskarta d’aukeda murmushi, ta d’au alwashin kafin Mu’azzam ya d’auki matarsa sai ta gyara masa ita tsaf, irin gyararrakin da suka cancanci Ta samu. Kama daga wanda idanu ka iya gani harma wanda idanu bai gani. ** Washe gari aka sallami Assad sannan Mu’azzam ya karb’i takardan gwajin DNA da yai, result d’in bai matching da k’wayar halittar Musaddiq ba. Hakan na nufin hular bata Musaddiq bace.. Sosai hakan yasa zuciyar Mu’azzam yin sanyi.. Saidai ya rasa dalilin da yasa ya gaza samun cikakken natsuwa akan sakamakon gwajin. Baisan dalili ba amma can k’asar zuciyarsa yana jin bai yarda da sakamakon ba. Sauk’e ajiyan zuciya yai a hankali yana mai fuzar da fuci lokaci guda ya saka abin goge allo ya goge dogon arrow da ya zana daga hoton Danger zuwa B.A.T da ya rubuta da question mark. Dai dai lokacin Yusuf da Maleeka suka shigo. SameenaAleeyou📚 *GIDAN ARO* *44* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Marker ya kuma d’auka ya zana allon ya sake rubuta abinda ya goge. Maleeka tai masa K’uri tana dubansa, Toh ko bai yarda da sakamon gwajin bane.? Kodai shakku da kokonto ya fara..? Bata kai ga nemo amsar ba ta sinkayo muryar Yusuf yana fad’in “Sir menene B.A.T yake nufi if I may ask..?” Mu’azzam na fuskantar allon yana karantar hotunan mutanen dake mak’ale jiki

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});