Chapter 240
Chapter 240
musamman.” Abinda kawai ya iya fad’i kenan kafin wasu Dr’s guda uku suka k’araso suka janyesa suka nufi ER cikin sauri. Mu’azzam yai k’ok’arin bin bayansu yana tambayarsu saidai bai sami zarafin cimmasu ba dan tuni sun shige wasu nurses na k’ok’arin dakatar dashi. Shafe fuskarsa yai yana kuma tamke idanunsa lokaci guda yana jin k’afafunsa na barazanar gaza d’aukarsa. Musaddiq ne yai k’arfin hali ya janyosa ya zaunar dashi. Daidai lokacin su Daddy da Mamy suka k’araso kowa hankalinsa a matuk’ar tashe. Mu’azzam na ganinsu ya mik’e ya nufi mahaifiyarsa. Bai iya furta komai ba sai fad’awa jikinta da yai yana mai fashewa da wane irin kuka. Mamy Ta tallafosa tana jin hawayen na zuwa mata itama. “Kai hak’uri Mu’azzam. Kaita karanta Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un kaji..” Abinda take iya fad’i masa kenan cikin tsananin rawar murya itama. Daddy kaw gefe suka matsa da Musaddiq yana sanar dashi abinda ke faruwa cikin tsananin damuwa dan shima Musaddiq d’in kana ganinsa zaka fahimci k’arfin hali ne kawai. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un kurum Daddy Ke iya nanatawa yana rok’on Allah ya kawo masu d’auki. Can sukaga wasu nurses guda biyu sun fito cikin sauri Sun nufi wani d’akin Sun kuma dawowa gudu gudu. Mu’azzam ya mik’e ya nufesu saidai kafin ya k’araso sun shigo k’ofar glass d’in da ya raba tsakani ya rufe. Juyowa yai yana duban Daddy da ya take masa baya “Why aren’t they saying anything..? Ya kamata su sanar damu halinda suke ciki right Daddy..?” Yanda yake maganar zai tabbatar maka ba cikin hayyacinsa yake ba. Daddy ya kamosa yana k’ok’arin kwantar masa da hankali. Daidai lokacin wasu Doctors guda biyu suka fito d’ayan na zame nose mask d’in dake bisa bakinsa da hancinsa. Daga yanda yanayin Likitocin ya nuna suka fahimci akwai babban matsala. “Dr where’s my wife..? Tinda nazo nan ban ganta ba.. Dan Allah ku barni na ganta.” Mu’azzam ya fad’i cikin tsananin d’imauta. D’aya Dr d’in ya kalli d’ayan. Ganin irin duban da suke ma juna yasa Mu’azzam soma girgiza kai yana furta “No.. No please.. Ku sanar dani halinda suke ciki..” Yana maganar yana k’ok’arin nufan ER d’in. D’ayan Likitan yai saurin rik’osa Sai ya soma fuzgewa cikin tsananin huci yana k’ok’arin shak’o wuyan likitan “Ina matata.. Ina matata nace..?!” Daddy ya soma k’ok’arin janyesa “Mu’azzam mu saurari abinda likitocin zasu ce.. Kai hak’uri.” Girgiza kai yake yana duban Daddy cikin wane irin yanayi mai ban tausai “Daddy Maiyasa basu cewa komai.. Maiyasa bazasu barni na ganta ba.” A haka Daddy ya janye hannunsa jikin Mu’azzam d’in na kuma mutuwa lak’was. Dr yai gyaran murya yace “The situation is very delicate.. I’m afraid we couldn’t remove the bullet from her body..” Ya d’an daidaita tsayuwarsa kafin yaci gaba da fad’in “But Fortunately, harsashin bai tab’a Jaririn dake cikinta ba. Amma We are not sure waye zamu fara cirewa cikin biyun. jaririn dake cikinta ne Ko harsashin da ya hudata.. Zamu iya rasa d’aya cikin biyun koma mu rasasu gaba d’aya.!” Abinda Likitan ya fad’i kenan cikin tsananin sanyin jiki. Girgiza kai Mu’azzam yake yana jin duniyar na juya masa “No.. No please.. Dan Allah kuyi duk abinda zaku yi.. Just save my wife please.. Dan Allah ku ceci matata.. I can’t lose her.. I can’t lose her right Mamy..” Yai maganar yana duban mahaifiyarsa cikin wane irin yanayi mai ban tausayi. Daddy ya shafe fuskarsa da tafukan hannayensa yana karanto innalillahi wa inna’ilaihi raji’un cikin zuciyarsa. Duban Dr yai kafin yace “Likita kuyi duk abinda zakuyi ku ceci Mahaifiyar da Jaririn.. Please Dr.. Just do whatever you can..” Dr ya jinjina kansa a hankali kafin yace “Ban San mai zan sanar dakai ba Alhaji.. But all I can is.. Mu shirya ma aukuwan koma menene.. Let’s prepare for the worse.” Ai bai kai aya ba Mu’azzam ya cakumosa “Incompetent! Are you telling us to prepare for the worse.? What kind of a Dr are you..?” Yaci gaba da jijjiga Dr yana fad’in “Zata sami lafiya.. Matata zata sami lafiya Kaji koh.. She’s going to get better.. And you will see.!” Daddy yai saurin janyesa yana dannarsa. Silalewa Mu’azzam yai wajen saman gwiwoyinsa yana jin wani abu mai zafi ya tsaya masa a k’irji.. Wayansu yake tunowa na k’arshe da yanda taita kallon fuskarsa har kaman bataso Ta janye idanunta. A hankali ya dafe fuskarsa da garu yana girgiza kai bai iya komai sai lumshe idanunsa da yai, yanajin hannun Mahaifiyarsa saman kafad’arsa tanata k’ok’arin kwantar masa da hankali had’ida karanto masa addu’an da zai dinga fad’i. Ya d’ago gajiyayyun idanunsa yana duban mahaifiyarsa “Mamy sun hani ganin Sadiya tinda nazo nan.. I can’t lose her.. Right Mamy.?” Yanda yake maganar dole ya baka tausai. Cikin sauri mahaifiyarsa ta rungumosa jikinta tana jin kuka na zuwa mata itama “Bazamu rasasu ba duka kaji.. Sadiya da abinda Ke cikinta harmada Safeenah.. Allah zai tashesu kaji koh.. Kaita karanto Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.” Daddy ya tare Likitan da fad’in “And Safeenah..? How’s my Daughter doing..?” Duban Daddy Likitan yai Sai kuma ya sadda kai kad’an. Daddy ya girgiza kai yace “Babu wani rufa rufa Dr, ka sanar dani situation d’in ‘yata please..” “Ka kwantar da hankalinka Alhaji. We are currently operating on her..kuma..” Bai k’arasa fad’in abinda yake cewa ba suka soma jiyo sautin alarm daga cikin ER d’in ga wasu nurses sun fito gudu gudu.. Babu shiri Likitan ya nufi Emergency Room d’in Bakin Daddy na karanto Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un. SameenaAleeyou📚 *GIDAN ARO* _(2022)_ *85* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Tashin hankali wanda ba’a saka masa rana, gidan duniya ake ma taken GIDAN ARO wanda duk ya shigo cikinta toh kuwa ko shakka babu akwai ranan da zai barta da shiri ne kokuwa babu shiri. Hankula sun kuma tashi musamman da ya kasance likitocin sun d’auki tsawon lokaci a d’akin operation d’in, babu wanda ya fito babu wanda gifta balle suyi tunanin jin ba’asi.. Sallah ne kawai yake fitar dasu amma haka suka yini zubur suna jira suji daga likitocin. Zaune yai cikin masallaci bayan sun ida sallah yana tunanin rayuwar da sukai da Sadiya da kuma Safeenah. Yaita kwararo masu addu’an samun sauk’i domin kaw baya fata ya rasa guda daga cikin su Fatansa shine su sami lafiya gaba d’ayansu. Saman wasu kujeru suka zauna shida Assad bayan sun fito daga masallacin Assad na kuma tausansa da basa baki kan cewa shi musulmi ne kuma ansan musulmi da d’aukan k’addara a duk yanda tazo masa. Fuskarsa na duban wani b’angaren yake tuna victims d’in Mommy da Danger. A hankali yake furta “First it was my Dad.. Then Ikram, sann mahaifin Sadiya.. Sann D’an cikin Safeenah.. Yanzu kuma.. Yanzu kuma Sadiya da abin cikinta harma da Safeenah.. Kana tunanin zuciyata zata iya d’aukan duka wad’ann abubuwan kuwa Assad.. Assad banida wann jarumtar.. I’m not that strong..!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya mai cikeda rauni. Assad ya Dafasa kad’an yace “Kai hak’uri Mu’azzam.. Sann Ka tuna Allah baya d’aurawa rai abinda bazata iya ba. Sann ita duniyar nan ba’a barin wani dan wani yaji dad’i.. Kowa lokacinsa k’ayaddade yake jira.. Dukanninmu kuwa.” Ya k’ura ma Assad Idanu kafin ya jinina kai a hankali. Da kalaman Assad masu kwantar da hankali ya d’an samu nastuwa kafin suka mik’e
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243