Chapter 191
Chapter 191
ya dinga tuna yanda tin tasowarsa basa jituwa da Uncle Salman, kaman dama tun can Uncle Salman baya wani k’aunarsa, shi zai iya cewa bayan gaisuwa babu abinda yake kuma had’asu sai lokacin da yaje masa da buk’atan karb’ar masa auren Sadiya da yai. A hankali yake jinjina kai cikin zuciyarsa yana fad’in sannu da zuwa Uncle. Zaka amsa min duka tambayoyi na kafin gari ya waye.. Yana tsaka da duban motar suka ida parking saidai hango mutum da yai zaune gidan baya ya sanyasa gyara tsayuwarsa sosai yana kuma duban bayan motar wanda ba kowa ya hango ciki ba face Inne. A fili ya furta “Inne.?” Cikin zuciyarsa yaci gaba da fad’in toh mai ya kawo Inne.. Maiyasa ta taho.? Daidai lokaci suka soma fitowa daga motar securities d’in gidan dake zaune gefe dan an hutasarsu ‘Yansanda ke tsaron gidan, suka soma nufosu suna kwasan gaisuwa had’ida masu sannu da zuwa. Har lokacin Mu’azzam na tsaye daga yanda yake yana dubansu. Abin ya bawa Inne mamaki ganin Mu’azzam bai K’araso ba. A hankali take sauk’owa daga motar tana fad’in “Ikon Allah.. Shi kuma wancan mai D’amaran yana kallon mutane yana tsaye wajen kaman an dasa Sa..? Koda yake dama D’ansanda ne..” Uncle Salman ya taho da niyyan taimaka mata saidai hakan yai dai dai da k’arasowar Mu’azzam murmushi saman fusakrsa. Inne ta d’ago tana duban Mu’azzam d’in da tuni ya tallafo hannunta guda yana mai taimaka mata “Ai cewa nake daga can zaka tsaya kaita kallonmu kaman mai d’aukan hoto ba camera bazaka Zo ka tarbeni ba.” Ya kuma murmusawa kad’an yana fad’in “Ni na isa ban taho na tarbeki ba Inne.. Sannu da zuwa Inne na.” Ya k’arashe hannunsa cikin nata. Ta amsa masa tana karantarsa lokaci guda suna ci gaba da gaisawa, Mu’azzam yakai dubansa ga Uncle Salman wanda shima Mu’azzam d’in yake duba cikeda kulawa, saidai fuskarsa babu yabo babu fallasa. “Sannu da zuwa, Uncle.” Mu’azzam ya fad’i a tak’aice gudun kar Inne ta d’ago wani abu. Uncle Salman ya amsa masa kaman ko yaushe fuska ba yabo. Mu’azzam na rik’e da hannun Inne guda suka nufi cikin gidan tana fad’in “Yo mi wad’annan masu zanzaron suke k’ofar gidan.. Gida ya koma saikace Barikin ‘Yansanda “Inji komai lafiya a gidan.. Ina Baban naku Marwan yake..?” A jere take kan jefowa Mu’azzam tanbayoyi kafin ya amsa guda Ta jefo masa wani. Nan suka had’u da Musaddiq a hanyar shiga cikin gidan. Shi kaw Uncle Salman yana biye dasu ne kawai amma jikinsa ya basa wani babban Al’amari na faruwa tinda yaga irin duban da Mu’azzam yai masa. Mommy kaw daga window take lek’ensu, zuciyarta ya tsananta tsinkewa Ganin harda Inne Uncle Salman ya taho.. Wato dai Mu’azzam ya shirya ma wann ranan. Ya rantse Sai ya tsige gaskiya.. Aiko wann gaskiya da yake k’ok’arin tsagewa ba komai zai haifar masa ba face tarwatsewarsa da rushewar ahalinsa. Ta murmusa kad’an tana jinjina kai kafin Ta furta a fili “Yayi kyau.. Da kyau Mu’azzam Gamji, da alama dai abinda zaka tono shi zai ajalin wann jarabebbiyar tsohuwar Wato Kakarka Inne..” Ta kuma murmusawa kafin Ta isa jikin wardrobe d’inta sai waige waige take. A hankali ta bud’e ta tura hannunta ta ciro wani k’aramin akwati ta, ta k’arasa ta danna ma d’akin nata makulli kafin ta dawo saman gado ta zauna, bud’e akwatin tai wani hoto ya bayyana, hoton wani mutumi ne matashi. Ta ciro hoton tana murmushi “Bansan meye alak’arka da ahalin Gamji ba, amma saidai na tsinci wann hoto naka ne a cikin Takardan yarjejeniyar BAT.. Yarjejeniyar da Abubakar Gamji ya rubuta.. Na shafe tsawon shekaru Ina ajiye da hotonka, nayi k’udirin sai na nemo ko Wanene kai.. Na kuma cika k’udirana na samoka, sann na kawar da kai dan mai yuwa kaima kanada alak’a da Ahalin Gamji ne.. Kaine mahaifin Yarinyar da Mu’azzam ya aura wacce na tura Sagir domin ya nemi aurenta, aka samu akasi Mu’azzam ya zamto mijin yarinyar.. Ban tsara haka ba, watak’ila da Mu’azzam bai auri yarinyar ba da yanzu baka mutu ba.. Ka mutu bansan mecece alak’arka da Abubakar Gamji ba da har ya saka hotonka cikin takardan Yarjejeniyar.. A ina ya sanka..? A ina ya samo hotonka..? Toh kodai kaima kanada Gadon mahaifinsu ne.? Kodai kaima D’an ahalinsu ne..? Ya akai Abubakar Gamji ya samu hotonka..? Toh amma kai d’in ba daga yankinsu ka fito ba.. Bakada wata alak’a na jini tsakaninka da Gamji family a iyaka binciken da nayi..!” Ta d’anyi fasali kafin ta mik’e tsaye still tana rik’e da hoton, lokaci guda taci gaba da furta “Menene alak’arka da ahalin Gamji..?” Take zuciyarta ta bata amsa da fad’in ‘Sanin alak’arsa da ahalin baida wani amfani a halin yanzu tinda ya riga ya mutu an kawar da nasa babin idan ma nada alak’a da dukiyar ne bazai tab’a cimmata ba tinda ya mutu kuma ga dukkan alamun bayan mahaifin Mu’azzam ke kad’ai ce kika San mutumin nada alak’a da ahalin..’ Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali kafin ta juya bayan hoton Wanda aka rubuta haruffan BAT a bayan hoton.. “Shin Yarjejeniyar nada alak’a da kai ne..?!” Ta tambayi kanta a fili kafin ta sauk’e ajiyan zuciya ta maida hoton cikin akwatin ta rufe. Knocking da taji a k’ofarta ne ya sanyata saurin saita kanta, Ta marairaice fuska tai kalan tausayi kafin Ta k’arasa tabud’e k’ofar. Kiki ce mai knocking d’in, Mommy Ta dubeta kad’an kafin ta sakar mata murmushi. Kiki ta isa ta rungume mahaifiyar tata cikeda tausayawa. “Mommy haka zakiyita zama a d’aki ke kad’ai, Mommy abinda ya faru ya riga ya faru, dama tun can Allah ya k’addara cikin Addah Safeenah ba mai zama bane.. Mommy ki daina kulle kanki a d’aki Kina kuka musamman yanzu da Inne tazo zata fahimci wani abu.” Mommy Ta murmusa kad’an kafin ta shafi kan Kiki tace “Karima kunyarku nakeji gaba d’aya, abinda nai ma Safeenah ban kyauta ba yanzu gashi Safeenah tana asibitin mahaukata dik ta dalilin abinda nai mata..” Wani kukan ya kuma kufce mata. Kiki ta fad’a jikin Mommy suna kukan tare. Da k’yar kukan Mommy ya tsagaita har saida Kiki taita lallashinta tana bata baki. Kiki ta goge fuskarta tace “Inne tazo tana sashenta, idan bazaki iya zuwa gaisheta ke kad’anki ba muje ni zan rakaki Mommy.” Mommy ta dubi Kiki ta murmusa tana mai kuma goge hawayenta kafin tace “Ba komai Kiki, zan iya zuwa.. Amma saidai bansan da wane ido zan dubi Kakarku ba, gani nake kaman zata fahimci na cire cikin Safeenah.. Kuma idan ta tambayi Ina Safeenah take mai zance mata..?” Kiki tai sauri tace “Ce mata zakiyi tana gidanta da Ya Mu’azzam..” Mommy ta murmusa kad’an kafin tace “Idan Mu’azzam yace bai maidata ba fah..?” Kiki ta d’anyi shiru sai kuma ta girgiza kai tace “Mommy nasan Ya Mu’azzam idan har yaji kince Safeenah na can gidansa bazai musa ba, bazai ce komai ma Inne ba.. Mommy ba kece kika haifi Ya Mu’azzam ba amma na tabbata shid’in uwa ya d’aukeki ke kisan da haka..” Mommy ta jinjina kai a hanakali kafin tace “Shiyasa nake jin ciwon abinda nai masa, sharrin zuciya batada kyau.. Wllhi ina nadaman cire cikin Safeenah da nai akan idanun Mu’azzam dik sabida burin fansar abinda ya aikata
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243