Chapter 28
Chapter 28
nan nan dashi take dan Farin ciki, tuni ta soma masa tayin abinci daban daban harma tambayarsa take ko akwai abinda yake so a girka masa a gurguje. Mu’azzam yace “A’a Inne zanci duk abinda ya samu, amma zanyi wanka na duba Mamy first idan yaso sai muci dinner gaba d’aya..” “Har dare bakaci komai ba, yammacin da saura fah..” “No Inne babu komai ai ba wani yunwa nakeji ba ma.. Zan duba Mamy sai na d’an huta..” Mik’ewa tai tana fad’in “Mutum yayi tafiya bai saka komai cikinsa ba inyi.. Badai a gidan nan ba..” Ta k’arashe tana mai kiran ma’aikatan. Mu’azzam yabita da kallo murmushi saman fuskarsa zuciyarsa Cikeda k’aunar ahalinsa. “You must be jet lagged.” Musaddiq ya fad’i murmushi saman fuskarsa yana mai k’ok’arin k’arasowa cikin parlorn. Juyowa Mu’azzam yai sanda Musaddiq d’in ya k’araso fuska fal fari’a sukai handshake suna d’an hugging juna. “Wai dama kana tafe.. Kuma shine baka fad’a mun ba.. I would’ve arranged something for you. You know this place is boring and annoying..” Da mamaki Mu’azzam ke duban Musaddiq dake sanye da uniform na ma’aikatan gidan gona“I can see you’re better off here.. And to be honest, naji dad’in ganinka haka da uniform kana aiki..” Musaddiq ya fuzar da fuci kad’an yana ‘yan waige waige dan ya tabbatar Inne bata wajen “Ai ni kawai matar nan ta gama dani.. Wllhi wnn jarabbebbiyar tsohuwa Ta gama dani.. Musaddiq Marwan Gamji no longer exists.. I guess fate has decided for me.. Ni kuma kalan nawa K’addaran kenan..” Yai maganar sanda suka jera suna tafe hanyar d’akin Aunty Nuratu.. Mu’azzam yaci gaba da fad’in “Haka shine da kyau Musaddiq, kaga one day you’ll takeover the family business. After all, Wannan shine mafarkin da a Kullum Daddy yake.. Wani daga cikinmu ya kula da kasuwancin Ahalin.. Saidai ni tuni Allah ya k’addari ba d’an kasuwa bane kaman yanda Daddy yaci min buri ni D’ansanda ne.. Naji dadi sosai da naga kai d’in zaka cika burin Daddy.. I’m so proud of you Musaddiq..” “Kawai ka fito fili kaima kace kana Farin ciki da k’untata rayuwata da akai..” Musaddiq yace yana kuma b’ata fuska Murmusawa wann karon Mu’azzam yai ya kaikaito yana duban Musadddiq sosai “Watarana zaka fahimci Inne gata ta maka Musaddiq.. We all love you, and we want what’s best for you..” Yai maganar kyakkyawan murmushi saman fuskarsa. Gajeren murmushi Musaddiq d’in ma yai yace “Sai ka shafe watanni Abuja kaji bana nan sannan ne zakace a dawo maka dani and your Grandma bata kyauta ba data d’auke ni..” Mu’azzam ya d’an daga fuskarsa suna ci gaba da takawa a hankali, ba tareda ya dubi Musaddiq d’in ba yace “At least zan d’an huta da rashin jinka..” “Au haka kace. Zamu gani ai.. I know rashina a gareka tamkar rashin police force ne..” Cewar Musaddiq daidai sanda yake tura k’ofan d’akin Aunty Nuratu sallama saman bakunansu. Aunty Shemau suka tadda ta gama kintsa Mamy ta d’aurata saman wheelchair.. Ta fad’ad’a murmushinta tana duban Mu’azzam d’in “A a Mu’azzam ka shigo, Aiko har na gama shiryata zan kawota wajenka.. Sai gashi ka shigo ma..” Cikeda jin dad’in yanda Aunty Shemau ke kulada mahaifiyarsa yace “A’a dama zan shigo Aunty.. Sannu da d’awainiya fah..” Aunty Shamau tai saurin katsesa da fad’in “A’a Haba dai Mu’azzam wani d’awainiya kuma.. Kawai na d’aura daga yanda ‘yar uwata Aunty Hajara ta tsaya ne. Aunty Nuratu ai ‘yaruwa ce a garemu.. Ka daina mana godiya kaman wani hidiman muke.. Ciwo ai na kan kowa, fatan mu dai Allah ya bata lafiya ya tashi kafad’unta..” Gaba d’aya suka amsa da Ameen daidai sanda Mu’azzam ya k’araso gaban wheelchair d’in ya duk’a Aunty Shemau na kuma gyara mata kanta da ya tank’washe a karkace. Mu’azzam ya zuba mata idanu zuciyarsa fal k’aunarta gauraye da tsananin tausayinta, Allah sarki inama wani na iya yaye ma wani cuta da ya bada duk abinda ya mallaka koda rayuwarsa ce dan mahaifiyarsa Ta sami lafiya.. Saidai ba haka abin yake ba. Allah shine yake jarabtan bayinsa da cuta ba Don ya k’isu ba saidai dan ya jarabci imaninsu da wannan cutan sannan ta kuma zame ma bayinsa na k’warai kankarewar zunubi.. Inne ce ta shigo tana tambayar ko mai maganin ta iso.? K’irjin Musaddiq ya buga dan sai yanzu ya tina da Ajidde da yanda sukai.. Inne taci gaba da fad’in “Shemau ki kirata muji ko lafiya bata iso ba har yanzu.. Ni bana son ana sako shiririta cikin lamarin jinyar nan..” Aunty Shemau ta d’an daburce tana fad’in “Ai Inne tace tana tafe.. Inaga abin hawa ne bata samu ba..” Musaddiq yayi caraf yace “Wait. Wai mai maganin Mamy.. Ai kuwa tazo amma saidai akwai maganin data mance bata taho dashi ba wanda za’a bata yau d’in.. So sai ta koma, and I don’t think zata iya dawowa yau dan wajen da take zuwa akwai nisa daga nan.. And kaman hadari ne a garin..” Duk suka juyo suna dubansa kafin Inne tace “Wannan ai shirita kenan..” Inne ta fad’i tana duban Musaddiq. Taci gaba da fad’in “Kuma sai ta rasa nawa zatai bayani sai kai..” “Toh ai ni ta samu Inne shisa ta fad’a mun..” Baikai aya ba tace “Kai rufe min baki..” Ta dubi Aunty Shamau tace “Shemau ki kira matar nan kiji bayani daga bakinta dan ban yarda da zancen Gidado ba.” Aunty Shemau ta jinijina kai tana fad’in “Toh Inne zan kirata..” Shidai Mu’azzam bai bi tankasu ba hannun mahaifiyarsa rik’e cikin nasa har lokacin.. A haka har d’akin ya rage saura shi da mahaifiyarsa.. Addu’o’i ya dinga mata har Shemau ta shigo ta taddasa. Nan take sanar dashi mai magani tace ko zuwa gobe za’a iya bata idan Allah yakai rai dan lokacin ma ruwa ake tsulawa.. Ta kuma k’arasowa tana fad’in “Kaje ka huta kaci abinci Mu’azzam gani nan ga Hindu zamu kula da ita...” Gajeren murmushi ya d’anyi had’ida mik’ewa yana ma Aunty Shemau godiya.. Yana ficewa Shemau ta Sauk’e ajiyan zuciya had’ida fuzar da fuci a hankali. Ta maidoda dubanta ga Aunty Nuratu tana aika mata mugun kallo “Nakasasshiyar banza.!” Ta fad’i tana mai hankad’a wheelchair d’in da Aunty Nuratu ke kai.. ** A b’angaren Ajidde kuwa koda ta koma gida ma Kyallu ba taro ba Sisi jibaganta tai Ta jefata d’akin Tumakai tace ta Kwana dasu, D’akin da Kyallu ke aje dabobbinta harda turke tayi ma Ajidde Wanda idan tai mata laifi take d’aureta a nan itama Ta Kwana tareda dabbobin.. Haka tayi lamo jikin turken da Kyallu ta d’aure mata k’afafu tana rungume da hular da ma’aikacin Gidan Gonar ya bata wanda bata San koda sunansa ba. Saidai tuni Ta masa lak’abi da Kuran Tashe.. Dikda azaban da take ciki hakan Bai hanata sakin murmushi ba sanda ta tina had’uwarta da mutumin wanda ko sunansa bata sani ba.. Tanaji can k’asar zuciyarta tana son ta sake ganin wannan fuskar tasa mai lullub’e da hazon k’ura wanda ya sanyata dariya da nishad’i har ya mantar da Ita ukuban da Inna Kyallu ke mata.. Washe gari bata aiki Ajidde ba da kanta tai shiri Ta nufi gidan dan bama Majinyaciyar maganinta.. Kyallu tana fita Ajidde ta samu ta k’ok’arta ta tsinke Turken data d’aureta. Gefe da Gidansu akwai wata mata
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243