Chapter 178
Chapter 178
Zo mu sab’a.. Yau da gobe Sai Allah. Dik auren da kikaga yayi k’argo Toh ki sani hak’uri ne ya kaisu ga cin nasara... Kuma Ina so ki sani dan Kin sami d’an little misunderstanding kar kike d’iban jiki ki taho gida.. Ba komai ake d’iban jiki a nufi gida ba, wani abun tsakaninku zakuyi sorting out matsalarku kuyi fixing komai ba Sai kun k’ara da third party ba, just the two of you.. Kuyi abinku a d’aki ku binne babu wanda yaji.. Har kullum idan kikace komai sai kin kai k’ara toh fah ke da kanki kin bud’e ma aurenki gib’i ne.. Matsala tsakanin ma’aurata idan ba yafi k’arfinki bane karki kuskura ki kai gaba kinji koh.. Wani dama ba Farin ciki yake da zaman lafiyar da kuke keda mijinki ba, akwai ‘yan jira auren ya lalace suyi Farin ciki da hakan. Duniya ce mai tarin mutane na kirki da akasin hakan..Wani k’iris yake jira yaji akanki dan dama ba k’aunar ci gabanki yake ba koda a fuska yana nuna maki k’auna..” Ta d’anyi fasali kafin taci gaba da fad’in “Rayuwar aure haka ta gada Sadiya, yau dad’i gobe akasin haka.. Iyayenmu duk haka sukai hak’uri suka jure har ta kaisu ga cin nasara..Sann Kowa fah da irin battle d’in da take fuskanta gidan aurenta, babu auren da za’ace anyisa ya tafi smoothly hundred percent babu matsala babu shi, wata zaki samu matsalarta Uwar mijin ce, wata dangin miji.. Wata abokiyar zamanta, wata da ‘ya’yan cikinta ma za’a jarabceta wata kaw shi kansa mijin shine nata k’alubalen.. Saidai na wani yafi na wani, mai imani shine Allah yake jarabtarsa.. Shiyasa kansa auren kansa ibada ne.. Bautar Allah kike. Kinga kaw dik abinda akace ibadah ne dole sai an jure anyi hak’uri.. Zakiga auren soyayya akai amma abinda za’a fara maku nasiha dashi shine hak’uri.. Ayi hak’uri, zakice yana sona Ina sonsa yo wane hak’uri? Sanin abinda ke cikin zaman auren yasa ake cewa sai anyi hak’uri.. Ayi hak’urin zama da juna. D’an Adam ajizi ne, tara yake bai cika goma ba, idan ya gaza miki Ta wann b’angaren Sai ki duba b’angaren da bai gaza ba, shima haka a b’angaren mijin, idan matarka ta gaza maka ta wani b’angaren sai ka duba b’angaren da bata gaza ba.. Mu ‘yanadam ne kuma masu kuskure, kiyi hak’uri kiyiwa mijinki uzuri kinji koh..” A hankali take jinjina kai tana hawaye. Aunty Larai tace “Yauwa yayi kyau, toh yanzu salin alin ki tashi ki koma d’akinki banso ma Umma tasan anyi wann..” Girgiza kai ta soma tana kuma fashewa da wani kukan “Aunty naji duk abinda kikace kuma zanyi amfani dasu in sha Allah.. Amma Aunty ni banzan iya komawa gidan yanzu ba, banson zuwa gidan.. I just need space.. Dan Allah ki barni a nan..” Aunty Larai ta murmusa kafin tace “Shikenan bazan tak’ura miki ba, barin barki ki d’an huce kad’an maza tashi ki shiga band’aki ki wanke fuskarki.. Ni bani son ganin damuwar nan saman fuskarki ne balle Umma ta d’ago wani abu.. Kinsan idan ta fahimci ba da sanin mijinki kika taho ba tsaf zata koraki ne.. Maza tashi ki wanke kizo kici abinci nasan da wahala idan kin saka abinci a cikinki..” Ta jinjina kai da k’yar dan har lokacin kanta bai daina sara mata ba, Ta mik’e tana jin jiri na k’ok’arin kayarda ita.. Aiko kaman wasa tana ida mik’ewa Ta yanki jiki ta fad’o kan gadon.. Hankali tashe Aunty Larai ke jijjigata tana ambato sunanta. Muryar Aunty Larai d’in da Umma Ta jiyo yasa ta nufo d’akin babu shiri rik’e da cazbahanta dan dama tinda ta ida sallar la’asar bata mik’e saman abin sallar nata ba. “Subhanallahi.. Meke faruwa.. Ke Sadiya..?” Umma ta fad’i a d’an kid’ime tana jijjiga Sadiyar yayinda tuni Aunty Larai Ta fice d’ibo ruwa, Ta k’araso ta shiga shafawa fuskar Sadiyar Umma na mata fifita da bakin hijabinta. Tana numfashi amma still idanunta a lumshe ga jikinta da ya sake gaba d’aya. Umma na mata fifita take ambato sunanta tana fad’in “Ke Sadiya.. Kina jina.. Sadiya bud’e idanunki mana.. Sadiya..!” Hankalin Umma duk a tashe, ba komai take tunawa ba sai rashin mahaifin Sadiyar da sukai.. Gani take kaman zasu kuma rasa ahali ne.. Aunty Larai kam tuni Ta shiga neman layin Mu’azzam amma saidai bata samu, hakan yasa Ta yanke shawarin kiran Assad.. Nan ta sanar dashi maza maza ya taho ya kaisu asibiti. Cikin mintoci da basu gaza talatin ba Assad ya k’araso, Umma da Aunty Larai suka tallafeta suka sakata cikin motar. Aunty Larai tace da Umma ta zauna gida wajensu Habeeb ita zata kula da Sadiya. Yaranma duk hankulansu a tashe. Umma ta jinjina kai tana duban d’iyar tata cikeda tausayawa had’ida k’aunarta. Nan tai masu fatan sauk’a lafiya da addu’an samun sauk’i ga d’iyarta Sadiya. ** Mu’azzam ya tsare Musaddiq d’in sosai da idanu kafin yace “Kana tunanin zamu iya samunta a wann gidan.?” Jinjina kai kad’an Musaddiq yai yace “Gidan Amaryar Senator Abba Mijinyawa, na tabbata zamu iya samun Mommy a wann gidan dan Hajiya Faty aminiyarta ce.” Jinjina kai Mu’azzam yai kafin yace “Muje.” Babu musu Musaddiq ya zaga ya shige mazaunin mai zaman banza. Koda suka iso gidan Musaddiq ne ya shige ciki yayinda Mu’azzam ke jiransa daga haraban gidan. Musaddiq ya dubi Hajiya Faty k’awar Mommy wacce Kwanakin baya Mommy tazo gidanta sanda suka sami sab’ani da Daddy. Musaddiq ya gyara tsayuwarsa yace “Aunty zaifi kyau idan kika sanar dani gaskiya, nasan Mommy batada yanda zataje da ya wuce nan..” Hajiya Faty Ta d’an sauk’ar da farin glasses na k’ara k’arfin gani dake manne saman idonta kafin tace “Musaddiq, kana so na sake maimaita maka ne.. Your Mom isn’t here.. Bata nan, kuma ni bansan yanda take ba..” Musaddiq ya d’an shafi fuskarsa kad’an cikeda k’osawa “Aunty please.. Dan Allah ki fito da Mommy idan har kece kike b’oyeta.. Aunty Mommy fah ba mai laifi bace kawai, Mommy is dangerous.. Please idan tana tare dake ki fito da ita..” Hajiya Faty ta tsare Musaddiq da idanu kafin Ta girgiza kai tace “Musaddiq akan mahaifiyarka ta aikata kuskure guda shine zaka bud’e baki ka kirata mai laifi..” Cikin k’unan zuciya yake furta “I know what I’m talking about Aunt.. Nasan kura kuran da Mommy Ta aikata da dama wanda baki bazai iya fad’i ba, kunnuwa bazasu iya sauraro ba haka nan zuciya bazata iya d’auka ba.. Aunt please, if you’re hiding Mommy ki fitar da Ita yanzu.. Mu’azzam na waje yana jira kuma na tabbata bazai bar gidan nan ba tareda Mommy ba..” Hajiya Faty ta daidaita tsayuwarta tana dubansa kafin Ta girgiza kai, tasa hannu ta ture Musaddiq d’in gefe tana fad’in “How dare he zai shigo mun gida ba tareda izini na ba..” Tasa kai ta Shige fuuu Musaddiq na biye da ita na kiranta. K’arasowa tai yanda Mu’azzam ke tsaye a haraban gidan yana jiran fitowar Musaddiq d’in. “Wace doka ce ta baka dama ka shigo mun gida ba tareda amincewata ba.. Who do you think you are..? Just because you are a Cop doesn’t mean zaka shigo mun gida kai tsaye..” Ta d’ago kai tana duban securities “Kai security kuzo ku fitar mun dashi..” Ta k’arashe tana kiran securities d’in
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243