Chapter 10
Chapter 10
kayan maye jibi dik yanda kayi duhu ka lalace..” Mommy ta k’walolo idanu waje jin Inne tace zata tafi da Musaddiq Fufore yaje yayi noma da kiwo, ta dubi Daddy tana jiran taji mai zaice amma shiru baice komai ba... Musaddiq ma ganin iyayensa ba suce komai ba ya sanyasa soma girgiza kai yana fad’in “No.. No way.. Gaskiya bazan koma Gidan Gona ba..Ai dai kinsan ina makaranta Inne..” Ta kuma Kai masa bugu a kafad’arsa yana karewa, lokaci guda take furta “Rufe mun baki shashasha.. Yo makarantarka har wani makaranta ne, inji kaje can k’asar wajen ka gama yawon shashashancin Naka babu abinda ka tsinana, na tabbata nan d’inma ba abun arziki kake ba.. Idan ba an rabaka da shashashan abokan naka dake nan ba bazakayi hankali ba.. Ni tuntuni nasan cewa shashashancinka yakai har ruwan kwalba kake sha da ban Barka ka girma a bariki ba..” Ta dubi Daddy da kansa Ke kife k’asa tace “Kana jina Marwan, yaron nan zamu tafi tare.. Kayi magana da D’anuwaka Salmanu tinda shike kula da Gidan Gonar, ya samar wa Gidado aiki a nan Gidan Gonar.. Ya dinga kula da shanun dake gidan gonar..” Musaddiq baki sake yake dubanta shaye da tsananin mamaki.. Katseta yayi da fad’in “Amma Inne kinsan ni ba karatun kula da Dabbobi nayi ba koh..I’m not a Vet Dr..” Carbinta da ko yaushe yake nad’e hannunta wannan karon ta warb’a masa tana fad’in “Rufe mun baki idan bakayi karatun kula da dabbobi ba ai ka gada kiwo... Ubanka ma ya gada.. Gidan Gonan da Kakanka ya mutu ya bari arzikinsa kake ci..” Ta d’ago tana kuma duban Daddy “Kana jina ka kira Salmanu ka sanar dashi tun kafin mu koma Adamawa..” Jinjina mata Kai Daddy yai yace “Za’ayi yanda kikace Insha Allah Inne..” Mik’ewa ta soma k’ok’arin yi ta dubi Mu’azzam tace “Kai kuma shige muje..” Cikin rashin yarda da batun Musaddiq Ke fad’in “Haba Daddy.. You can’t be serious.. Daddy this is unfair.. Dan Allah kar ka bari hakan ta kasance..” Ya d’ago ya dubi Mu’azzam dake k’ok’arin bin bayanta yace “Officer dan Allah ka mata magana, you’re her favorite zata saurareka..” Ya k’arashe yana bin bayan Mu’azzam d’in cikin gudu gudu... Saitin kunnensa Mu’azzam Ke fad’i a hankali “Hakan yafi idan dai halinda zakaci gaba dayi kenan a nan..” Musaddiq ya girgiza masa kai yace “Wllhi na daina..” “Proof it then..” Mu’azzam ya fad’I yana mai bin bayan Inne.. Cikin sauri Musaddiq ya take masu baya.. Suna ficewa Mommy Ta dubi Daddy tace “Yanzu bazakace komai ba.. Haka zaka zuba ido Ta tafi dashi..” “Mai kike so nace Hajara.? Nace mata ba haka ba.. Ko kin mance cewa matar nan mahaifiyata ce.. Sannan idan hakan shi zaisa d’anki ya dawo cikin hayyacinsa I’d welcome the idea d’ari bisa d’ari.. If he stays here babu wani abinda zai tab’uka ma rayuwarsa..” Shiru Mommy tai tana mai kwantar da kai, hawaye ya ciko idanunta, k’ok’arin saita kanta tai sanda Daddy yaci gaba da fad’in “He’ll be better off there, tinda a nan dai kina gani yanda muke tare tare dashi, idan aka canza masa environment d’in na d’an wani lokaci k’ila Allah yasa hakan ya zamto sanadin shiriyarsa... Muyi masa addu’a kawai da fatan hakan ya zamto alkhairi..” Mommy dai bata ce komai sai mik’ewa da tai ta haura sama tana tinanin hukuncin cikin ranta.. Ita tanadinta shine Nuratu ta fice mata daga gida tayi nesa da ita da ahalinta ba Wai d’aya daga cikin yaranta yai nesa da Ita ba.. Daddy ya bita da kallo yana mai kwantar da kansa cikin kujera had’ida lumshe idanunsa kad’an.. Inne na gaba Mu’azzam da Musaddiq na biye da ita, Musaddiq naci gaba da magiyan cewa ta janye k’udirin ta.. “Kai Gidado (Kaman yanda take kiran Musaddiq d’in) bari kaji na fad’a maka.. Ko Marwan Ubanka bai isa ya hanaka komawa Gidan Gona ba.. Na riga na gama magana ehe, bazan zauna inaji Ina gani ka zame mun zakka ba.. Banyi shirin sallameka ba.” Musaddiq ya dubi Mu’azzam da yai kaman bashi a wajen a hankali kaman mai rad’a yake furta “Aren’t you gonna say anything.. Talk to her please.. She can’t do this to me... I mean she’s turning my life into a nightmare.” Bai Kai aya ba yaji sauk’ar ‘ya’yan carbi a k’eyarsa, yai saurin sosawa yana d’an sakin k’ara.. Kunnensa ta kamo dikda ratan tsawo dake tsakaninsu.. Nanma k’ara Musaddiq ya saki yana k’ok’arin k’watan kunnensa.. Inne Ta dage k’arfinta ta matse kunnen tana fad’in “Ni na gayyaceka d’akina..? Maza a k’ara gaba.. Fita ka bani waje jarababbe..” Ta k’arashe tana turasa waje.. Dik tsimewan da Mu’azzam yake saida yaji dariyar Inne da Musaddiq ya taso masa.. Ya sunkuyar da kansa gajeriyar murmushi saman fuskarsa.. Inne na hankalce dashi sannan sosai taji dad’in ya d’an saki ransa dan zata iya cewa tinda tazo bataga murmushinsa ba.. Abubuwa da dama Sun faru dashi d’in.. Ga mutuwar k’anwarsa bayan jinyar da mahaifiyarsa Ke ciki... Musaddiq na ficewa Inne ta K’araso ta zauna bakin gado, tai nuniwa Mu’azzam da kujerar dake fuskantar gadon “Modibbo zauna kaji muyi magana.” Ba musu Mu’azzam ya k’arasa ya zauna yana “Inne na zata kin tsufa a Adamawa..” Ta tab’e baki kad’an tace “Ina zanje bayan ban kai maka Matarka d’akinka ba..” Ba zata yaji maganan nata ya d’ago yana dubanta, dan shi harga Allah ya mance da wani maganan tariyar Safeenah.. “Kana jina.. Yau d’in zuwa dare.. Kokuma a barshi gobe yarinyar nan ta tare a d’akinta.. Zaman baida wani amfani..” D’an tura yatsunsa yai kad’an cikin sumarsa kafin yace “Inne Wai dama da dai an barshi sai zuwa gaba kad’an..” Shiru tai tana dubansa cikeda tausyawa, ta jinjina kanta a hankali kafin tace “Idan kace haka zan iya fahimtarka Modibbo.. Nasan har yanzu alhinin rashin ‘yaruwarka na tareda kai.. Amma idan kana tareda Matarka sai ta d’ebe maka wani kewan ka fahimta..” D’an shafe fuskarsa yai kad’an kafin yace “Inne ai akwai abubuwan da nake so su daidaita kafin nan.. Kinga yanzu babu Ikram dama itace take taimaka wa Aunty Hajara da jinyar Mamy na.. Aunty Hajara bazata iya kulada Mamy ita kad’ai ba dukda dai dama akwai ma’aikatan jinya da ake hayansu masu taimakawa.. Inaso idan al’amarin suka daidaita Sai mu tare mu koma cen gidan..” Katsesa tai da fad’in “Ni nan zanyi jinyar Nuratu.. Dama wannan karon nace zan d’auketa mu koma gida a jarabba jinyar gargajiya tinda na asibitin Allah bai nufa za’a dace ba.. Nayi magana da Baban naku dikda shima naga yafi son zamanta a nan amma haka dole zaku hak’ura a jarabba na gargajiyan.. Sannan zatafi samun kulawa a wajena sama da nan d’in..Watak’ila maganinta na gida bamu sani ba..” Shiru yai kaman mai nazari, harga Allah baison mahaifiyarsa tayi nesa dashi musamman duba da yanayin jinyar da take ciki.. Amma baida wani zab’i idan hakan shine Alkhairi.. Zaifi kowa son mahaifiyarsa ta sami lafiya.. Kaman kuma yanda Inne tace zatafi samun kulawa wajen Kakar tasa dukda kuwa cewa bai tab’a ganin gazawar Mommy ba sannan har kullum fatan alkhairi ne tsakaninsa da ita.. Ko dan mutuncin iyayen Safeenah Daddy da Mommy da yanda suka rik’esu amana shida ‘yaruwarsa da kuma mahaifiyarsu dake cikin tsananin jinya baiji
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243