Chapter 124
Chapter 124
dan basu San wa aka harba cikinsu ba. Su dai kawai sunji sautin fitan harsashi.. Muryar Musaddiq ne ya sanyasu bud’e idanunsu har lokacin suna rik’eda juna. Nan sukaga yanda harsashin ya huda jikin gini. Musaddiq ya nufo Safeenah yana fad’in “Feenah bani bindigar nan..” Nunasa tai da bindigar tana ci gaba da huci take fad’in “Don’t come near me Musaddiq.. Stay back.. Kar ka matso kusana..!” Tai maganar tana nunasa da bindigar. Daidai lokacin Mu’azzam ya nufota yana fad’in “Bai nan.. Bani bindigar nan Safeenah..!” “What if na hanaka..? Mugu kawai.. Macuci.. Maci amana..! Azzalumi.. Mai ha’intar aure... Da kai ya kamata ma na fara kafin na k’araso kan ‘yariskar da kake cin amanata da ita..!” Ta k’arashe tana saita Mu’azzam d’in da bindigar. Da rinannun idanunsa yake dubanta ba tareda yayi ko gizau ba. Shine Safeenah take gaya masa maganganu son ranta irin haka.. Ya jinjina kai still yana dubanta. Ba laifinta bane.. Laifinsa ne da ya bari taga girmansa. Cikin dakewa ya kuma fad’in “Hand me over that gun..!” Ya fad’i yana dubanta. Safeenah ta kuma girgiza kai tana hawaye, lokaci guda take furta “Bazan bada ba.. You choose between ni da wannan ‘Yariskar..” Ta k’arashe tana mai nuna Sadiya da bindigar. Izuwa lokacin zuciyarsa ta gama kai k’ololuwa wajen tafarfasa ya nufota a zafafe yana fad’in Ta basa bindigar. Saitasa tai da bindigar tana huci take fad’in “If you take one more step.. I swear I won’t hesitate to shoot you right in the head..And believe me, I mean it..!” Tai maganar sai sakin huci take tana nunasa da bindigar cikin tsananin zafin kishi wanda ya rufe mata idanu ruf bata ganin komai. Izuwa lokacin kam ya tabbatar ma zuciyarsa k’wak’walwar Safeenah ta samu matsala, ba daidai take aiki ba. Yai mata K’uri yana dubanta da idanunsa da tuni sun kad’a. Cikin huci Safeenah dake pointing nasa da bindiga take fad’in “Ka zaci Allah bazai toni asirinka bane.. Kana can ka ajiye wann karuwar a wani waje without my knowledge.. Toh Allah ya kamaka yanzu sai ka zab’a ko ni ko ita.. Idan ka cika kai Mu’azzam Gamji ne ka zab’a yanzun nan wacece zakai zaman aure da ita.. Ni Safeenah ko wannan ‘Yariskar..!” Ta k’arash still tana nunasa da bindiga. “Haka kika ce..?” Ya fad’i yana dubanta. Safeenah Ta jinjina kai tana fad’in “Eh haka nace.. You choose between us..” Tana maganar zuciyarta na k’arfafa mata gwiwa da fad’in Mu’azzam yana matuk’ar k’aunarki tinda har ya kasa sanar dake yana tare da yarinyar.. Hakan na nufin yana shakkun b’acin ranki ne.. Bazai iya rayuwa babu ke ba. Wannan ya tabbatar miki da irin k’aunar da yake miki.. Bata ida tunanin nata ba ta sinkayo muryarsa yana fad’in “Na sakeki Safeenah..!” K’ara ta saki tana mai d’aura hannayenta biyu aka dai dai lokacin Musaddiq yai azama ya fincike bindigar daga cikin hannunta. Sadiya ta saki Meema ta nufo mijinta Wanda shid’inma tuni ya nufota. Rungumeta yai tana mai fashewa da wani irin kuka jikinta har lokacin bai daina rawa ba. Safeenah Ta kuma fincika daga rik’onda Musaddiq da Mommy sukai mata tana fad’in “Wllhi Mommy sai na kasheta.. Mommy kina gani My Halal ya zab’i wannan ‘Yariskar sama dani.. Wllhi sai na kasheta..” Sai ihu take tana fincika tana fad’in su saketa.. Daidai lokacin Daddy ya shigo ya tadda wann hatsaniyar. Mommy ta fashe da kuka tana salati tana fad’in “Ehh Lallai Mu’azzam ka tabbata.. Ka cika tabbatacce.. Ko mutuwa na kunyan idon uwa.. Ni tinda nake ban tab’a ji anyi saki gaban uwa ba.. Na shiga uku ni Hajara..” Ta dubi Daddy kafin taci gaba da tafe hannaye tana fad’in “Kazo kaga abinda D’an matarka ya aikata ma d’iyarka.. Ya zab’i bare sama da jininsa..” “Enough please Mommy..!” Musaddiq ya dakatar da Ita cikeda takaici. Lokaci guda yake ci gaba da furta “Aiko bai saketa ba Cikin gida biyu ‘yarki zata kasance a guda d’aya.. Kodai Ta tafi gidan Yari ko ta tafi asibitin mahaukata dan babu hankali tattare da Safeenah. Balle ma ita ta buk’aci hakan da kanta.” Safeenah ta kuma kurma ihu ta tsalle tana fad’in atafau bazata yarda ba babu wanda ya isa ya rabata da halal d’inta.. Meema ta k’araso kusanta sanda zata fice, tana duban Safeenar a yatsine. Murya can k’asa tace “Ai saidai kiyi hak’uri Addah Feenah dan Ya Mu’azzam ya zama haram a gareki yanzu kam..” Safeenah ta zabura zata kamo Meema. Tuni Meema ta fice ta basu waje. Musaddiq ya shiga karanto ma Daddy abinda ya faru yana nuna masa jikin garu yanda Safeenah ta huda da harsashi. Ya k’ara da “Daddy what Safeenah needs is a Dr.. A psychiatrist m.. Likitan mahaukata take buk’ata Daddy.. She’s not well..” Haba nan fah Safeenah ta hayayyak’osa tana fad’in lafiyarta lau sune mahaukata da suke tunanin zata rabu da Halal d’inta. Musaddiq ya girgiza kai yana mai jan gajeren tsaki kafin ya dubi Mu’azzam yace zai jirasu a Mota. Jinjina masa kai kurum Mu’azzam yai kafin Musaddiq d’in ya fice. Daddy ya dubi Mu’azzam da Sadiya wacce ke tsaye gefensa kanta a k’asa kana gani zaka fahimci har lokacin a razane take. Daddy yace “D’auki matarka ku tafi Mu’azzam kar ku rasa flight d’inku.” Safeenah Ta kurma wani irin razannan ihu tana fad’in babu yanda zasu tafi wllhi. Ta tafi a guje tana k’ok’arin rik’o Daddy dake haurawa upstairs tana fad’in “Daddy wllhi sakin k’arya ne.. Wllhi My Halal bai sakeni ba.. Mommy ce ta masa dole..” Haba nan fah Mommy ta hayayyak’ota da fad’in “Ni zaki ma sharri Ina mahaifiyarki..! Allah yasa ba ni kad’ai bace wajen.. Daidai kenan yanzu Kinga ranan zab’en namiji akan mahaifiyarki.. Gashi ya zab’i matar da yai auren bariki da Ita ya barki.. Yanzu zaki dawo cikin hayyacinki Safeenah..” Mu’azzam dai bai kuma bi takansu ba ya janyo hannun matarsa suka fice suka bar Mommy da Safeenah sai rantse rantse suke gaban Daddy.. Safeenah tana fad’in Mommy ce ta zugota tazo Mommy tana fad’in hakkin abinda tai mata ne ya kamata. A guje Safeenah tabi bayansu kaman sabuwar kamun hauka.. Mu’azzam zai shige Mota Safeenah ta rik’o rigarsa tana fad’in “My Halal.. Dan Allah kace sakin wasa ne.. My Halal you know I can’t do without you.. Please Mu’azzam kar ka tafi ka barni..!” Ta k’arashe tana mai fashewa da kuka. Kallanta yai ya kalli yanda Ta rik’e masa riga kafin yace “A hukumance abinda kikayi za’a d’aureki akan hakan, Kinyi attempting murder.. Kin sake cin albarkacin Daddy bazan jefaki a cell ba.. Kaman yanda dama zaman auren da kikayi albarkacinsa kika ci.. Sakar min rigata.. You are not my wife..!” Yana ida fad’in haka ya finciki rigarsa yai shigewarsa Mota. Safeenah tabi motar a guje tana fad’in my Halal.. Inaa tuni motar ta fice daga gidan. Ihu ta kuma zundumawa ta nufi cikin gidan tana kuka tana fad’in wllhi sai ta bisu ta dawo da halal d’inta saidai ai duk abinda za’ayi. Zata shige Mota kenan taga Daddy tsaye gabanta ya kai k’ololuwa wajen had’e rai. “Give me the keys..” Ya fad’i yana mik’a mata hannu. Girgiza kai take tana hawaye “Daddy please ka barni na bi mijina.. Daddy wllhi sharrin shaid’an ne.. Daddy zafin kishi ne bansan abinda nake aikatawa ba..
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243