Chapter 199
Chapter 199
muma munsan watarana za’a Zo a tafi damu tinda an kwashe da dama an tafi dasu akan idanunmu.. Mukai yunk’urin guduwa nida Yayata amma sai wasu k’artan maza suka kamamu.. Mutumin yace tinda guduwa zamuyi ya kamata a tafi damu kafin mu masa asara.. Washe gari akazo da Mota aka d’aukemu aka kaimu tashan jirgin ruwa.. Haka aka sakamu a wann jirgin ruwan nida Yayata da wasu ‘Yanmatan.. Mun shafe kusan sati muna Yawo saman teku muka yada zango a wasu k’asashe har kusan uku da bamu San ko wasu k’asashe bane dan an b’oye mu ne can wani d’aki a k’ark’ashin jirgin ruwan.. Duk k’asar da muka tsaya sai muga an shigo da wasu ‘Yanmatan ma’ana dai wasu daga cikin k’asashen Africa muke zagayawa ana kwasan ‘Yanmatan. Dik k’asar da muka tsaya idan aka shigo da ‘Yanmatan sai a d’aura mata alama na wani coin a jelar kitsonta kaman yanda muma suka d’aura mana nida Yayata sann sun d’aura ma ko wacce daga cikinmu wann alama na coin a bakin kitsonta wanda nake da tabbacin shaida sukai mana.. Tsoro bai sakemu ba Yayata tana rungume dani.. Dik rana biredi guda ake bawa ko waccenmu a cikin wann jirgin ruwan shine abincin da zamuci.. Wasu lokuta haka Yayata take hana cikinta Ta bani nata kason.. A haka muka tsinci tattaunawan wasu ma’aikatan jirgin ruwan ana cinikinmu kaman wasu bayi.. Nan mukaji cewa K’asar turai zasu fice damu ‘Yanmatan da suka d’an data daga cikinmu zasu yi amfani dasu su dinga kawo masu kud’i dan mazan turawa suna son matayen Africa sann K’anana irina kenan zasu saida wasu b’angare na jikkunansu akan kud’i mai yawa.. Wasu zasu saida k’odansu dama duk wani organ mai amfani na jikin D’anadam.. Hankalin Yayana ya tashi musamman da Ta fahimci cewa nima naji tattaunawan mutanen.. Na soma kuka Ina fad’in zasu kashemu.. Ta rungumeni tana kuka tana fad’in Allah bazai nasu nasara akanmu ba da izinin Allah.. Tace dani nai shiru kar na nuna naji tattaunawar su da sannu Allah zai kub’utar damu.. Aiko bamu ida wann tunanin ba muka soma sinkayo harbin bindiga ashe Jami’an tsaro ne suke bibiyan wann jirgin ruwan.. A haka suka soma bud’emu suna son transferring namu zuwa wani jirgin suna fad’in ga jami’an tsaro.. A haka suna bata kashi tsakaninsu da jami’an tsaron muka samu zamu arce gudu muke suna biye damu.. A haka muna cikin gudu nida Yayata muka had’u da wani mutumi shima gudu yake kowa na Ta kansa.. Yayata Ta a tambayi mutumin ko wata k’asa ce wann sai mutumin yace mata nan k’asar Nigeria ne kuma jihar Lagos.. Muna gudu mutumin yake tambayarmu mu kuma daga Ina muke.. Yayata tace masa sato mu akai daga K’asarmu Eritrea.. Sai ta tambayesa shi kuma mai yake a nan.. Saurayin yace shi daga Arewacin Nigeria yake zuwa jihar Lagos suna kawo fatu na dababbi ana fitar dasu k’asashen waje Ta jirgin ruwa.. Muka ci gaba da gudu na kasa gudu sabida ba wani k’oshin lafiya bane dani.. Sai saurayin ya d’aukeni ya azani a bayansa yana fad’in muci gaba da gudu kar mutanen Su cimmamu.. Muna cikin gudu muka hangi mutanen suna biyomu a guje suna fad’in ko mu tsaya ko su harbemu.. Yayata Ta karaya dan bata fata mutanen su kama ‘Yaruwarta bata fata wad’ann azzaluman su cutar dani ‘Yaruwarta.. Sai Yayata ta dakata da gudun, ta dubi matashin mutumin wanda a lokacin bazai gaza shekaru 24 ba tace dashi Bawan Allah ga amanan ‘Yaruwata ka taimaka ka tseratar mun da ita daga hannun azzaluman nan.. Bansan ko zamu sake had’uwa a gaba ba.. Amma ga amanan ‘Yaruwata na bar maka.. Wann saurayi mai Sana’an Safaran Fatun dabbobi daga arewacin k’asar nan zuwa kudanci mai suna Ibrahim ya amsa amanar da ‘Yaruwata Ta bashi muna kuka daga ni har ‘Yaruwata.. ‘Yaruwata tace mecece alama da zanyi amfani da ita na iya ganeka gaba idan Allah ya nufa zamu sake had’uwa.. Sai Matashin ya ciro hoto cikin aljihunsa ya mik’a mata yace wann hoto na ne bansan wata shaida ko alama da zan baki ba amma ki rik’e wann hoton nawa ki nemeni da ita a gaba.. Yayata Ta amsa hoton tana hawaye tana masa Godiya. Ina gani Ta k’ulle hoton Ibrahim cikin zaninta kafin mukaci gaba da gudu nida Ibrahim.. Juyawan da zamuyi muka hangi ‘Yantaddan nan sun kame Yayata sun jefata cikin jirgin ruwan.. Suna jefata kuwa muka hangi wuta ya tashi a cikin jirgin ruwan dan dama bata kashi suke tsakaninsu da jami’an tsaro...!” Umma taci gaba da hawaye yayinda Aunty Larai ke hawaye.. Umma taci gaba da fad’in “Akan idona jirgin ruwan da Yayata ke ciki ya kama da wuta.. Ibrahim yaci gaba da gudu dani Ina fad’in ya k’yaleni naje na duba Yayata amma bai sakar ni ba, haka ya dinga gudu dani Ina kuka yana lallashina.. A haka Ibrahim ya tseratar dani da taimakon Allah amma alhinin rashin ‘Yaruwata yana nan tare dani.. Ya kawo ni garinsu Birnin Kebbi yanda ‘Yanuwansa sukai masa chaa da fad’in Ina ya samo yarinya.. Ibrahim ya sanar dasu cewa ni d’in amana ce a gareshi.. Babu yanda danginsa basuyi ba cewa ya fitar masu dani a cikin gida dan basu San daga wata duniya nake ba amma fir Ibrahim yak’i aminta yace idan zasu koreni saidai Su had’a dashi.. Ba dan sun so ba suka k’yaleni Sai dan Ibrahim ya dage cewa ni d’in amanarsa ce kuma zai rik’eni amana kaman yanda yaima ‘Yaruwata alk’awari.. A nan gidansu Ibrahim da shike family house ne kuma iyayensa sun rasu dangi ke rik’e dashi a nan suka saka min suna Uwani dan sunana Wato Aisha sunan Kakarsu Ibrahim ne sai suna kirana da Unwani.. Aka Zo za’a saka yara sa’annina a makaranta a nan family house d’in su Ibrahim d’in, kowa ya saka d’ansa a makaranta amma ni babu wanda ya waiwayeni balle ya sakani.. Wariya babu irin wacce ba’a nuna min amma haka Ibrahim yake lallashina yace nai hak’uri wataran komai zai wuce kuma nima zanyi karatu kaman ko wacce yarinya a cikin gidan.. Haka da ‘Yar sana’arsa Ta safaran Fatun dabobbi ya samu ya tara ‘Yan kud’ad’e ya sakani a makaranta.. Harta da tufafi babu mai saya min a dangin komai shi yake mun, wajen kwana da abinci kawai suke bani suma d’in sai nasha gori.. A haka suka soma bijiro ma Ibrahim da maganar aure lokacin ni ina k’arama ban wani girma sosai ba tinda dama ya d’an fini da shekaru masu d’an yawa.. Akwai wata d’iyarsu a cikin gidan da suke son had’asu auren Dangi Amma sam Ibrahim yak’i amincewa yace dasu shi baida lokacin aure kula dani yake ba aure bane a gabansa, kula da amanarsa yake.. Wann soyayya da kula da Ibrahim ke nuna mun yasa suka k’ara tsanata k’arshe suka ce saidai na fice masu a zuriya nasan yanda dare yamun Wai zan raba masu kan ahali sabida Ibrahim yaro ne mai biyayya amma bai tab’a bijire masu ba sai akaina.. Sukace ya zab’a ko su ko ni.. Ibrahim yace ya zab’eni zai aureni kuma zaici gaba da kula dani.. A haka akai aurenmu da k’uruciyata.. Ibrahim ya d’aukeni ya taho dani garin Suleja yanda yake bugabugansa..” Muryar Umma yaci gaba
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243