Chapter 223
Chapter 223
Lallai ya yarda wann azzalumar mata babu abinda bazata aikata ba domin cikar burinta.. Baijin akwai kotun da zai iya yanke hukuncin Hajara a duniyar nan. A shekarun aikinsa na D’ansanda yasha cin karo da criminal cases amma bai tab’a cin karo da ‘Yartadda irin Mommy ba. Harta ‘ya’yan cikinta ma bata barsu ba saida tai amfani dasu ta k’ulla masu sharri. Safeenah da Musaddiq. Ashe cire cikin Safeenah da tai ba komai bane cikin jerin abubuwan da Ta aikata. Ji yai ko kallon yanda take baya son yi, bai tab’a kyamatan wani halitta irin Mommy ba. Ko shak’eta yai a wajen nan har Ta mutu bata biya abubuwan da ta aikata ba.. Ana a haka suka soma sinkayo murya daga k’ofa Sadiya tana k’ok’arin rik’o Umma take fad’in “Umma family meeting suke bai kamata mu shiga ba.. Ki bari har Mu’azzam d’in ya fito Sai ki tambayesa.” Umma taci gaba da janye hannunta tana fad’in “A’a Sadiya.. Ki k’yaleni na tambayesa.. Bazan iya jira ba sai na tambayesa.” Ta k’arashe tana mai sako kai cikin parlorn Sadiya na biye da ita tanata k’ok’arin dakatar da Ita. Gaba d’aya mutanen dake parlorn kallonsu ya dawo kansu. Cak suka tsaya suma suna duban mutanen dake Parlorn yayinda idanun Umma suka sauk’a kan matar dake duk’e tsakiyar parlorn sanye da farar lafaya. SameenaAleeyou📚 *GIDAN ARO* *80* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* A hankali ta soma k’ok’arin mik’ewa tana duban matar wacce ke nufota hawaye na fitowa daga idanun matar. Wani haske mai kaman walk’iya taga ya gifta cikin k’wayar idanunta. Abubuwan da suka faru a wancan shekarun, rasa iyayensu.. Jinyar ‘Yaruwarta kwanciyarsu a asibiti har izuwa saidasu da mutumin da ya taimaka masu yai.. K’aran jiragen ruwa dake shawagi saman manya manyan tekuna take sinkayo cikin kunnuwarta.. Mutumin da ta mik’a masa ‘Yaruwarta tace ya kular mata da ita, bata hotonsa da kuma kamata da yantaddan suka kuma yi har izuwa jefata cikin jirgin ruwa da kuma tashin bomb da jirgin ruwan yai. Take take jin wasu memories d’in abinda suka faru a rayuwarta na baya suna Yawo a kwanyarta da k’wayar idanunta. A haka Umman Sadiya ke K’arasowa itama hotunan abubuwan da suka faru sai gifta k’wayar idanunta suke.. Ta yaya zata mance wann fuskar.. Fuskar ‘Yaruwarta kuma Yayarta Halimatu wacce tai sadaukarwa da dama a sabida ita.. Hawaye sukaci gaba da gangaro mata yayinda su duka biyun suke duban juna, haka nan d’aukacin jama’an dake cikin parlorn idanunsu akansu ne harda Sadiya dake tsaye daga bayan parlorn. Fuskokin juna suke duba hawaye naci gaba da gangaro masu, yayinda Aunty Nuratu takai hannunta dake rawa tana shafa fuskar Umman Sadiya a hankali tana kallon fuskar ya koma mata tamkar dai na k’aramar k’anwarta Aisha a lokacin da suke shekarun k’uruciya.. Kuka taci gaba da yi bata daina shafa fuskar nata ba yayinda Umma ma ke kuka tana duban ‘Yaruwar nata. A hankali Umma ke d’ago hannunta, ta Ware tafin hannunta da coins d’in ke ciki.. Aunty Nuratu ta sauk’e idanunta tana duban coins d’in, kukanta ya k’aru itama.. Coins d’in da akai masu alama a sumarsa lokacinda Yantadda suka sacesu. Cikin rawar murya Aunty Nuratu ke furta “Eassh...Easshaa...!” (Ita kad’ai ke ambatonta da wann sunan duk duniya). Ai take Umma ta kuma bursting cikin kuka tana mai rungume ‘Yaruwarta “Didi.. Didi.. Deedeee..!” (Itama ta ambaceta da sunan da take kiranta) Kuka yaci k’arfinsu su duka biyun suna masu kuma k’ank’ame juna. Gaba d’aya illahirin jama’a dake parlorn mamaki ne ya cikasu da ganin irin wann kayan al’ajabi da mamaki.. Babu kaman Sadiya da Mu’azzam wanda suke duban iyayen nasu cikin tsananin shock.. Mai hakan yake nufi.? Wann dai Umman Sadiya yake gani rungume da mahaifiyarsa suna shek’an kuka.. Did they know each other from the past.? What exactly is happening.? Tambayar da zuciyarsa ke bijiromasa kenan. Saurin juyowa yai yana duban bayan parlorn yanda Sadiya ke tsaye tana duban iyayen nasu cikin tsananin kad’uwa da mamaki. Ya kuma maidoda dubansa ga Mamynsa da Umman Sadiya wanda har lokacin rungume suke da juna tsakiyar parlorn suna kuka mai ban tausayi. Kowa ya zuba ma Sarautar Allah idanu suna duban wann kayan al’ajabi, ciki harda Hajara dake duk’e wajen kaman mabaraciya. Saida sukai kuka mai isarsu kafin Aunty Nuratu ta kuma kamo fuskar ‘Yaruwarta. Ta tallafo fuskar nata sosai da hannayenta duka biyu magana sukai cikin harshen yaren ‘Yan k’asarsu dan su kuma tabbatar ma juna sud’in ne. Murmushi mai gauraye da hawaye saman fuskokinsu suka kuma rungumar juna kaman zasu shige cikin jikin juna. Suka d’ago suna duban mutanen parlorn da sukai masu k’ur yayinda Aunty Nuratu taci gaba da jinjina kai, hannunta rik’e cikin na Umman Sadiya take fad’in “‘Yaruwata ce.. ‘Yaruwata da muka rabu a lokacin da muka shigo k’asar nan.. ‘Yaruwata da na mik’ata amana hannun Ibrahim.. Ibrahim mutumin da ya mun alk’awarin rik’eta da amana.. Sann shine mutumin da Hajara Tasa aka kashe a sakamakon samun hotonsa da tai cikin takardan yarjejeniya.. Abubakar ya saka hotonsa ne cikin takardan domin dani da Abubakar duk bamusan mutumin ba, kawai munga hoton ne a tare dani sabida tunanina da ya shafe.. Abubakar Allah ya gafarta masu baki d’aya ya d’au alwashin nemo Ibrahim sabida tinanin da mukai na cewa Ibrahim zai iya zama D’anuwa a gareni.. Wann haruffa da ya rubuta jikin Yarjejeniyar ya rubutasu ne sabida kalaman dake jikin sisin kobon da muka kuma tsinta tattare dani..” Ta amshi coin d’in hannun Umman Sadiya tana nuna masu “Black African Team.. sune K’ungiya masu safaran mutane da suka sato mu daga k’asarmu wanda aka tarwatsa su tun a wancan zamanin.. Abinda yasa Abubakar ya rubuta BAT jikin takardan ba komai bane Sai dan Black African Team Wato sunan K’ungiyar shine zai zamto mabud’in sirrin sanin ko ni wacece da kuma yanda na fito..” Sai ta dasa aya ta juyo tana duban Umma dake ci gaba da hawaye “Hajara ta kashe Ibrahim..!” Ta furta cikin rawar murya. Umma na hawaye take jinjina kai “Ibrahim ya rik’e amanarki Didi.. Ya kula dani da yaran da muka haifa tare dashi har izuwa lokacin da zai amsa kiran mahaliccinsa..” A tak’aice ta fad’i duk abinda ya faru aurensu da kuma yanda Sagir ya shigo rayuwarsu da yanda suka rasa mahaifin Sadiyar. Aunty Nuratu na hawaye take duban Mommy dake duk’e wajen Al’ajabi bai saketa ba jin Wai ashe mutumin mijin k’anwar Nuratu ne.. Sann matar Mu’azzam da Ta tura Sagir ya aura bai aureta d’in ba Mu’azzam ya aureta ashe d’iyar k’anwar Nuratu ne.. Itakam bata K’ara ma Nuratu da ahalinta komai ba face kusanci.. Ashe Mu’azzam d’iyar ’yar uwar mahaifiyarsa kenan ya aura.. Wato dik yanda kaso ka rufe abu idan Allah yaso abun ya bayyana Sai ya bayyana.. Da ace tasan wann yarinya tanada jinin Nuratu tattare da Ita da ta umarci Danger ya kasheta a lokacin da ya saceta. Tinaninta ne ya Katse sanda Umman Sadiya ta duk’a gabanta tana tambayarta “Baiwar Allah Maiyasa kika kashe mun miji.. Maiyasa kika rabani da Ibrahim.. Maiyasa kika zab’i ki turo Sagir cikin rayuwarmu..? Maiyasa kika zab’i ki jefamu cikin tashin hankali wanda bamu santa a baya ba tun bayan aurena da Ibrahim..!” Kuka yaci k’arfinta ta shiga jijjiga Mommy dake duk’e wajen kanta a k’asa. “kin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243