Chapter 99
Chapter 99
kwara a dakin" Babanta ya dafe kirji "ince ko ba ke kike gyara wurin ba idan yayi amai" Tayi kwalkwal da idanu "waye zai gyara idan banyi ba. Yanzu ma itace nake so ya siyo min wani saboda wannan yayi danshi yau da marmarin kunu na tashi. Amma yaki fitowa" Zinaru sai bude baki take amma ta ma kasa magana don mamakin karyar da Amarya ke gillawa. Ran Garbebe ya baci sosai. Yadda yake son yarsa shiyasa tana cewa Gidado take so ya amince. Yanzu ga ciki burinsa ta haihu ya sami jika. Ya dallawa Zinaru harara sannan ya fara kwalawa Gidado kira. Mutumin banza haka ya fito daga shi sai wani kodadden wando duk jirwaye. Garbebe yace "na gaji da wannan rashin kirkin naku. Kaje ka kwashe gwanjonka daga shagona. Ke kuma Zinaru idan jikan ne baki so ki fada ba sai kunyi mata horon yunwa ba. Daga yau bazata kara aikin amai ba don ba baiwarku bace" Gidado yace "uwar tawa kake fadawa magana haka?" Zinaru ta kwabe shi cikin harshen fulatanci "kyaleni dasu ka koma daki. Takarda aka kawo daga wurin uwar yaranka nasan bazasu yarda ta kuma zama da kai ba. Amma na sami dillali zan biya shi ya taimaka mu sayar da gidannan ko babu takardu. Ita kuma wannan kazar matsiyatan ka bari mu karbi kudin gidan sai ka saketa itama su karata ita da uban nata. Har yanzu da kyaunka Gidado baza mu rasa 'yar masu kudin da zaka iya aura ba" Shiru Gidado yayi da yaji zancen saki tsakaninsa da Zulaiha. Yara har shida tsakaninsu dole yaji yana sonta duk irin halinsa kuwa. Garbebe ya ja hannun Amarya suka yi wajen kofar gidan yace "shegun nan basu san mu fulani bane hala" Amarya tace "basa yin yaren a gidan shiyasa bana yi musu. Basu san na iya ba" Garbebe ya tafa hannuwa "karen bana ke maganin zomon bana. Kyaleni dasu ki koma amma ki fara shiri gaskiya aurenku ya kare. Ya ma kika ce sunan baban matarsa ta fari?" Amarya ta fada masa ya kwashi kafa sai gidan su Zulaiha. ***** Qasim da Ma'u ke hira a bangaren da ake ajiye motoci tana cewa ya shigo ciki yaci abinci saboda ya kwaso hanya. Innarsu ce tace ta kirashi ma amma yaki amincewa wai gara ta kawo masa nan. "Kai har ka fini kunya ma" Qasim yace "haka kike gani ko, nan da wata uku ne zaki gane waye Qasim" Ma'u tayi dariya "har kasa mana ranar ne?" "Nan da sati biyu za'a kawo kudi da sa rana. ni dai nace wata biyu za'a saka daga nan sai ki fara shirin komawa Zamfara" Tayi murmushi "Allah Ya tabbatar mana da alkhairi" Hayaniya suka ji daga bakin gate karshe dai maigadi yazo ya fada mata wani ke neman Alhaji tace baya nan bari taje ta gani. Qasim ya daure fuska "ina zaune zaki je bakin gate ganin wanda ba'a sani ba. Muje tare dai just incase na gida ne." Ma'u ta mike suka tafi. Mutumin dai basu sanshi ba amma sun fahimci labarin da ya kawo musu na cewa Zinaru zata sayar da gidan Zulaiha. Ma'u tace bari ta fada a cikin gida. Tare da Zulaihan suka fito. Tana ganinsa ta gane shi, lokacin da take tare da Gidado har dashi ake mata wulakanci kala kala wai shi mai 'ya. Yanzu kuwa russunawa yayi yana diban gaisuwa kafin ya sake mata bayanin abinda ya kawo shi. Zulaiha tayi masa godiya tace babu komai hukuma zata shiga zancen tana nuna Qasim. Garbebe ya dan tsaya yana jiran ihsani ladan kawo gulma yaga babu wanda yayi motsi cikinsu sai ya tafi kawai. Ko ba komai ya tarewa Zinaru hanyar samu. Yana fita wata mota hadaddiya ta shigo gidan. Wani mutum ne a bayan motar dreba na jansa. Maigadi yana ta daga hannu saboda Alh Najib akwai kyauta. Kusa da inda Qasim, Ma'u da Zulaiha ke tsaye suna zancen hali irin na Gidado da Zinaru akayi parking motar ya fito. Da fara'asa ya mikawa Qasim hannu suka gaisa sannan ya gaisa da Ma'u da Zulaiha wadda ta kasa kallonsa ma. Ciki ya shiga yace Alhaji na hanya zai jira shi ne. Bayan ya wuce Zulaiha ta tafi jikinta babu kwari. Ma'u tace "wannan Alhaji yaso aura mata fa taki yarda tun farko. Anti Zulaiha tayi masa wulakanci sosai gashi yanzu tana kunyarsa." Qasim yace "rabon haihuwa yasa ta auri wancan. Kuma gara haka akan ta haifesu a titi. Tunda ba yau zan tafi ba sai ki fadawa Alhaji in shiga case din Gidadon nan" "Ai kuwa zaiyi murna. Bari ya dawo anjima sai na fada masa". ***** Cikin kwanaki biyu Zinaru da Gidado sun tattara komai nasu zasu bar gidan sannan yayi mata saki daya. Tayi ta rokon Zulaiha wai ko albarkacin yara ta yafe musu a mayar da auren. Ko kallon kirki basu samu ba daga gareta balle yan uwanta. Da kwanan titi gara na kauye a dole tayi shirin komaa garinsu wane kauye a cikin Taraba state. Bats sani ba mijinta da ta baro yana da rai ko ya mutu. Alhajin su Zulaiha yace lallai wasu daga cikin yayyenta maza su bi bayansu aga tushensu albarkacin yara. Zinaru an sha kuka ga Amarya ma Garbebe ya karbar mata takardar saki. Su Humaira ko a jikinsu saboda irin mugun zaman da suka yi a hannun kakarsu da Babansu wanda bai san kowa ba sai kansa. Ganin idon Qasim ne ma yasa yabi Zinaru a son ransa ko a karkashin gada ya kwana indai zai sami ganyensa ya busa. Alh Najib kuwa tunda yaji anyi saki ya sanar da Alhaji idan Zulaiha ta gama idda a fada mata har yanzu yana sonta. Yana da mata dai da yara hudu. Banda auren wuri shekarunta goma sha shida ta auri Gidado ko secondary bata gama ba. ***** Sati biyu a tsakani aka taho nemawa Qasim auren Ma'u harda Col. Ishaq Jikamshi cikin tawagar su Alh Adamu. Wannan abu yayi dadi domin rashin auren Asmau bai sa sun kullaci juna ba. Daga zuwa kawo kudi Alhaji yace indai sun amince a kawo sadaki kawai a daura aure kada ayi ta wahalar da mutane. Haka kuwa akayi aka saka biki da tariya wata guda. Col. Ishaq ne ya kira Qasim da wannan albishir. Yayi murna sosai shikenan shima ya shiga sahun magidanta. Innarsa kuwa kamar tayi me don dadi. Allah Ya taumaketa danta yayi aure kuma ya auro yar mutumci irin wadda take so. ***** Zuwa yanzu kowa yasan da cikin Asmau a cikin 'yan uwanta da nasa. Kulawa take samu ta kowane bangare kada Mami taji labari. Sosai take kaunarta yanzu. Saura sati biyu bikin Qasim tana ta shirin zuwa Jos yana kallonta kawai. Ciki wata hudu ga laulayin da take fama amma ta dage da roko har da addua akan ya barta taje ko don Zulaiha. Sun gama rigimarsu yana ta shan kunu Amatullah tace masa tayi masa tuni zai kaita siyan takalmin makaranta na gudu. Da kyar ya yarda suka tafi da Asmau. A hanya aka shirya dama basa dogon fushi da juna. Sun gama siyayyarsu suna fitowa daidai inda suka ajiye mota suka hadu da wasu maza su biyu cikin shiga ta kamala kayansu ma iri daya. Daya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103