Chapter 89
Chapter 89
hankali da muguwar kyama. Kuma wasu da gaske sun tuba amma hakan bai sa mutane raga musu ba. Ta san dai komai bazai taba gogewa kamar bai faru ba amma duk da haka auren da tayi yafiye mata komai. Ta auri irin mijin da kowace mace zata so kasancewa dashi. A take ta yanke shawarar neman izininsa na yin azumi duk ranakun litinin da alhamis domin neman karin kusanci da Allah da kuma tuba. ***** A nan ya dawo ya sameta tana kuka da addua. Ya zauna a gefenta suka karasa tare sannan ya kuma bata baki akan ta cigaba da hakuri da rayuwa. Daga hira ya dawo da maganar rama cizo. Ta soma bashi hakuri yace bai san zance ba. Daga baya yace "nuna min inda bakya so a jikinki sai na rama a nan" "Gaskiya ina son ko'ina" Dariyar mugunta yake mata don yaga tsoro take ji. "To bari na saukaka miki. Rinka nuna min inda kika fi so, duk inda kika bari karshe shine ba kya so din. Sai ki bar min nayi yadda na ga dama". Asmau ta hau tunani gashi ya kureta akan gado. Duk inda tasan ana jin zafin cizo ta fara lissafawa a cikin zuciyarta. Yace ita yake jira tace "to bakina nafi so" Col. Ishaq ya dan bata rai "ni kuma nan ne bana so sosai a jikinki. Kinga sai na rama a nan ba sai munyi nisa ba" Daga nan bai bari ta motsa ba bare ta gudu.... ***** Shi ya fara tashi wurin goma ya kalleta. Bacci take sosai kamar wata 'yar yarinya. Allah Sarki Asmau, duk wata matsalarta ta wuce a wurinsa. Yadda ta iya jajircewa akan aurensa duk da matsalarsa yasa yake jin sonta sosai a ransa. Zaiyi nasa kokarin sosai wurin kyautata mata. Duk wani gata da miji zaiyiwa mace shima zai kokarta. Baya son ko kadan suyi nadamar auren juna. Yadda take tunanin yayi mata alfarma shima hakan yake ji. A hankali ya fita daga dakin don kada motsinsa ya tasheta. Yasan ba karamar gajiya ta tara ba tun kafin a fara bikin. Ga ta biki ga rashin bacin kirki a nasa gidan. Kitchen ya shiga wanda ya cika store din da kayan abinci tun kafin a kawo gara. Sauran kananan abubuwa da mace ke bukata na kitchen ya bawa Safiyya kanwarsa kudi yace ta tabbatar idan an gama jere ta sayo su ta ajiye. Ai kuwa ta siyo su kwai, kayan miya da 'yan tarkacen da ba'a rasa ba duk ta ajiye a inda ya kamata tun jiya. Su Shemau ta tarar suna karasa aiki lokacin da ta kawo kayan. Ya duba ya sami abubuwan da yake bukata ya fito dasu. Addua yake kada Asmau ta tashi sai ya gama komai. Ya dade da koyon girki a wajen Hajiyarsu. Ko ta koreshi daga kitchen sai ya dawo yace tayata zaiyi. Ita tana haka saboda namiji ne kuma dan fari shi kuwa ko a jikinsa. Har babansu yace ta rabu dashi. Ga amfanin koyon girkin yazo. Da Asmau idonta biyu kila tayi masa dariya ko kuma ta hana shi. Wata hira da suka taba yi ta fada masa abinda tafi son ci da safe ya tuna. A lokacin dama tunaninsa yayi mata shi ranar farkon aurensu. Tana can tana baccin gajiya ya da fa masu indomie da attaruhu, albasa da caras yadda tace tana so. Ya dafa kwai ya yanka a gefe da cucumber sannan ya hada musu tea a cups ya zuba a tray. Shi kadai yake murmushi har yaje dakin. Tana nan inda ya barta. Ajiye tray din yayi ya zauna kusa da ita ya janyota jikinsa. Ta bude ido kenan zata yi magana ta kula da agogo. Shadaya harda rabi. Ta zaro ido tana kokarin tashi."Subhanallah haka nayi ta bacci, ka dade da tashi ko? Ko breakfast ban hada maka ba. Bansan wane irin bacci nayi ba yau" Duk ta damu ko kadan ba haka taso ba. Amare da take jin labari sun riga mazansu tashi sun hada musu abinci ita gashi rana ta fito tana bacci. Zaunar da ita ya sake yi "duk kin wani tada hankali kamar wadda tayi laifi. Bacci kuma ai dole kiyi, ko kin manta baki sami damar yi ba jiya" Asmau ta ji kunya, duk inda zai dauko maganar da zata kunyatata ya iya. Ta sake yunkurin tashi sai ta ga tray din abincin har tiriri yake, sai lokacin ta farga da kamshin dake tashi taji cikinta na kukan yunwa. Idonta ne ya ciko da kwalla da ta ga yadda ya tsara komai kamar ba hirarsu ne sati daya kafin biki. Fadawa tayi jikinsa "Jikamshina nagode" tana jin wani sabon sonsa a ranta. Wannan farincikin yake son gani daga gareta kuma ya samu. "Kije kiyi brush kada yayi sanyi. Idan kuma godiyar zaki yi zan baki goyon baya. Kinsan ana son yawan godiya" yana magana yana daga mata gira ta tashi da sauri tana dariya ta shige toilet. Kafin ta fito wayarsa ta soma kara ya dauka ganin maigadinsa ne. "Sir baki ne suka zo har mota biyu. Na bude musu?" Col. Ishaq yaji kamar ya fita ya kori ko su waye. Shi fa yana mamakin wannan dabiar ta hausanmu. Ayi komai na hidimar biki da mace wai amma gari na wayewa sai su zo ganin amarya. Ko ganin gulma kamar yadda yake kiran ziyarar. Ai dai a bari ko azahar ayi. Amma yanzu ko shabiyu batayi ba ace an zo gidan sababbin aure ai ba'a so zaman lafiya ba. Bare a lokaci irin wannan da ya gama tsara yadda zai kasance idan sunci abinci da amaryarsa. "Ina fata ba a gabansu ka kirani ba" "Eh Sir, ina daga ciki ne" Rai a bace yace "to ka fita kace wayata a kashe take kuma nayi umarni kada ka bude sai da izinina" Ya ajiye wayar da yaji Asmau zata fito. Akan gadon suka ci duk kunyarta ta ajiye a gefe suna bawa juna a baki. Yadda ya kyautata mata itama haka take kokarin yi masa. Shaf ya manta da batun baki sai da Asmau ta fita kitchen zata mayar da kwanukan Hajiya ta kira shi. Ko gaisuwarsa bata amsa ba ta fara fada akan lallai yasa a bude gate ga baki nan 'yan uwansu ne da wasu daga gidansu Asmau duk sun hadu a bakin gate maigadi yaki budewa. Ba'a son ransa ba yace to tare da bata hakuri. Da Asmau ta dawo tace masa zata je tayi wanka. "Nazo muyi tare?" Ta fito da manyan idanunta "rufa min asiri" "Nine sirrin naki Matar Jikamshi. Bakya bukatar rufe min komai. Kije kiyi amma idan kika dade zaki ganni" Ta fita shi kuma yayi waje daga shi sai dogon wando da jallabiya. Bazai fada mata da baki ba yasan rudewa zatayi ta fara komaina gurguje. Abinda baya so kenan shiyasa ya kyaleta ma tayi wankan. Bayan ya bawa maigadi umarnin ya bude musu ya bude kofar falon ya koma ciki. 'Yan uwansu ne na Jikamshi masu komawa a ranar sai na Asmau 'yan Wushishi. Sake fitowa yayi da bayan sun shigo an fara hayaniya ana ta gaisawa. Wasu suna ina amarya take. Ai suna ganinsa har 'yan uwan nasa kunya sosai ta kamasu domin kana ganinsa zaka san
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103