Chapter 54
Chapter 54
zuwa zai tura masu wakiltarsa a nemawa Qasim auren Asmau. Ya gaji da ganin dan nasa gwuaro. Da Qasim yace basu gama shawara sa Asmau ba, Mal Musa yace babu komai sunyi magana da Alh Adamu yace zaije ya sami Umma da Kawu Garzali a tsayar da magana ayi aure kowa ya huta. Murmushi Qasim yayi na jindadi don yasan Asmau bazata bijerewa iyayensu ba. ABINDA AKE GUDU🙆🏽40 Batul Mamman💖 Washegari su Asmau basu sami zaman gida ba. Sun hadu da Shemau, Sabira da su Nasiba an sake gyara gidan Ainau kamar masu shirin kai amarya. Da yamma Umar yaje ya daukota. Kana ganinsa kasan yau yana cikin farinciki. Kusan wata uku bata gida don tun kafin ta haihu aka bata bedrest shine Mama tace ya kaita gida zata fi hutawa. Ranar Jikamshi ya kirata yafi sau shida kuma sai anyi hira akalla ta rabin awa. Yana kira sai ya tambayeta ko Qasim ya kira kuma wayar minti nawa suka yi. Sai da ta gama dariya sannan ta zolaye shi tace "baya ajiye waya sai wata wayar ta shigo min." Shima dariyar yayi mata kawai yace "ba zan damu ba don nasan tawa hirar ce kawai take burgeki koda kuwa ta minti daya ce. Amma zancen gaskiya ki dena kashe masa murya yadda kike yi min. Kara sonki kawai zaiyi ni kuma ba hakura zanyi na bar masa ba" Tayi dariya sosai hakan ya sanya shi nishadi. "Haba Yaya Ishaq, kai fa Yayana ne kuma Yayan Qasim. Kaci girma kawai" Kamar tana gabanshi ya dan daure fuska cikin wasa "ki kiyaye ni fa matar Jikamshi. Ni ba yayanki bane na fada miki. Kina magana da baban Safina mijin Asmau in Sha Allah" Ta danyi shiru tana jin inama hakan ya tabbata. "Baki ce amin ba" "Amin" ta amsa ba don yana tunanin ganin ranar aurensu a gaba ba. Addua zata yi masa Allah Ya bashi mace ta gari. Amma tasan bazata je komai ba a bikin. Daga haka suka yi sallama kowannensu yana kara jin son dan uwansa. ***** Bayan sati daya kullum Col. Ishaq da Qasim sai sun kirata a waya kowanne yana kara jaddada mata irin son da yake mata. A wannan kwanakin da Jikamshi bai zo ba ita kanta abin ba karamin damunta yayi ba. Har mamaki take yi da take masa so irin wannan duk da tana kokarin dannewa. Ranar alhamis ta kira Zubaida ta sanar da ita zata zo yini washegari. Zubaida sai murna don tun dawowarta sau daya ta samu taje gidan, basu zauna sunyi hira yadda suke so ba. Ita kuma Zubaida saboda cikinta ya tsufa babu batun fita. Kafin shabiyun rana washegarin Asmau ta gama girkin rana tayiwa Amatullah wanka sannan itama ta shiga. Tana fitowa taga Umma ta dawo duk da ranar aiki ne. Har daki ta bita tana tambayar ko lafiya. "Babu komai yau dai na gaji ne. Kinsan kwana biyu bamu huta ba. Kema da kin hakura da zuwa gidan Zubaidan sai wani satin. Yarinyar nan kina ta yawo da ita 'yan kwanakin nan" "Umma Yaya Jafar yace zai kaini ba adaidaita zan hau ba." "To kiyi maza ki karasa shiri kinsan baya son jira." Asmau ta tashi ta koma daki ta karasa shiryawa sannan ta zauna jiran Jafar. Ko rabin awa ba ayi ba ya iso. Suna shirin fita taga Kawu Garzali shima ya shigo. Gaisawa suka yi yace mata Zubaida tun asuba take jiranta. Yanzu Kawun nasu kamar wani kaka haka yake musu wasa. Shima dai tayi mamakin ganinsa don ance mata Umma ce ta sama masa aiki a inda take wato MTN office. ***** Suna fita Umma tayi ajiyar zuciya ta tafi dakin Hajjo ta sanar da ita wayar da suka yi da Mama tun tana wurin aiki. Shine ma dalilin dawowarta gida da wuri da zuwan Kawu Garzali. Alh Adamu ne yake son ganinsu don yace gidan zai zo idan ta taso aiki. Kasa hakura tayi saboda Mama tace mata batun auren Asmau da Qasim ne zai kawo shi. Shiyasa ta fada Garzalin suka dawo gida kawai. A cikin satin da tayi magana da Asmau akan manemanta biyun ta nuna mata ita karatu kawai zatayi duk zata sallamesu batare da bacin rai ba. Sai dai kuma tuni Umma ta gano inda zuciyar 'yarta tafi karkata. Matsalar dai bai wuce abinda itama Asmau take jiyewa tsoro ba na dangane da gori ko rashin amincewa daga dangin mazan. Bayan ta gama bayaninta Hajjo tace "yaron nan da gaske yake da rike amanar amininsa. Allah Ya tabbatar da alkhairi." Ta danyi shiru kamar mai tunani sannan tace "Amma idan banyi kuskuren fahimta ba sai naga Ishaq shima kamar fa sonta yake yi. Kinsan mu idonmu idon soyayya. Muna ganinta muke ganewa" Umma tayi dariya sannan ta fada mata wayarsu da Anti Bintu da kuma yadda suka yi da Asmau "Bazamu zuba mata ido ba duk da muna jin tsoron surutun mutane auren shine rufin asirinmu. Duka su biyun ni bana kin kowa amma Hajjo kinga Qasim muka fi sani kuma gashi har maganarsa ta kai kunnen manya. Garzali ma ya shigo ina tsammanin a falo ya tsaya. Shine namiji dole ayi komai dashi " "Kinga wancan mutumin banzan shi ya kamata ace zaiyi komai akan lamarin yaran nan amma kafin a ganshi ma aiki ne" Umma ta fahimci da Kawu Rabe take. Murmushi kawai tayi "kada ki damu Hajjo, Garzalin ma ai babanta ne kuma na fadawa su Yaya Abu don su san me ake ciki. Saura kuma sai yazo munji" Kawu Garzali sallama zai shigo dakin yaji Hajjo tace "Kinsan Allah Bara'atu kada ku yarda kuce kun amince ba tare da munji ta bakin Asmau ba, bazan yarda kuyi mata auren dole ba. Idan bata so ya hakura kawai" Umma tace "Hajjo mu har mun isa muce bama so? Kada ki manta duk abinda ya faru da Asmau. Yanzu duk wanda yazo neman aurenta ai alfarma yayi mana" Hajjo ta danyi shiru tana tausayawa jikarta "kuma fa haka ne. Allah Ya rabamu da mummunar kaddara" Tashi Umma tayi "dama yanzun ma ina jin shawara ce dai yake son bamu a matsayinsa na uba gareta." Kawu Garzali ya gaishe da Hajjo sannan tace su fito falo Alh Adamu yazo. ***** Sun zazzauna an gaisa da Alh Adamu da Mama Yalwa da bata dade da shigowa ba itama. Yayi dan gyaran murya wanda ya janyo suka fuskance shi "Nasan Yalwa ta fara sanar dake dalilin zuwan nan. Mal Musa ya kirani a waya ya sanar dani yadda suka yi da Qasim akan auren Asmau. To shi a son ransa nan da lahadi su zo ayi magana ta iyaye a tsayar da lokaci. Shine ya bukaci lallai in fara sanar daku domin ayi shawara" Hajjo ce ta soma magana "hakika Alhaji kai uba ne ga dukkan 'ya'yan Bara'atu. Ka rikesu tsakani da Allah tun lokacin da mu da suke dolenmu muka wofantar dasu. Duk shawarar da ka yanke akan yarinyar nan muna da tabbacin bazata cutar da ita." "Duk da haka Hajjo me kuka gani? A basu dama su zo ko akwai wani tanadi da kuka yi mata". Kawu Garzali yayi saurin cewa "haba haba Alhaji akwai wani tanadi ne da ya wuce aure. Amma Haj Bara'atu me kika gani?"
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103