Chapter 38
Chapter 38
yake yiwa Asmau. Ya sha nemanta sai dai taki bashi hadin kai kuma kullum haka ta faru sai ta fadawa Zulaiha don gudun matsala. Tayi ta yiwa Zulaiha nasihar rabuwa dashi sai dai tayi murmushi kawai. Wannan ya tabbatar mata da cewa har yanzu Zulaiha na son mijinta. Sai ta kyaleta suka cigaba da zamansu. ***** Annur yana kwance a daki bayan ya dawo daga makaranta yana dan danna wayarsa aka turo masa wani text da hoto. Da farko baiyi niyar bude hoton ba sai da ya karanta labarin yarinyar a matsayin wadda mijinta ya rasu ranar aure kuma aka gane tana da ciki. Tsaki yayi sannan ya bude hoton don shi da Gaddafi yanzu karatu suka saka a gaba. Matar ya gani kyakkyawa da ita har ya ajiye wayar sai ya sake daukowa ya duba hoton. Hannunsa na rawa ya turawa Gaddafi yace ya duba ko ya gane ta. Ba jimawa Gaddafi ya kira yace sai ya ga kamar matar nan mai ciki da suka taimakawa mai suna Asmau. Matar da suka je nema a asibiti basu sameta ba. Tausayinta suka ji musamman da suka tuna halin da suka tsinceta da irin nasiharta garesu. A cikin sati daya suka yi ta bincike da tambaya ko akwai wanda ya santa har suka dace da samun wani dan makarantarsu da yace a unguwarsu abin ya faru a Kano. Yaron har gidan Umma ya kaisu suka sanar da ita labarin haduwarsu dai Asmau. A wannan ranar an sha kuka sannan Umma tace ita ta hakura zata cigaba da yi mata addua. A duk inda take Allah Ya tsareta kuma Yasa ta dawo gida da kafarta. *BAYAN SHEKARA BIYAR* Idan kaga Asmau bazaka ce itace tazo garin Jos a rame da tsohon ciki ba. Duk da bata da jiki kamar da amma ta dan samu nutsuwa. Ita da Zulaiha kuwa ko 'yan biyu bazasu nuna musu kusanci ba. Tana tuka tuwo Zulaiha na tsinke zogale taji sallamar Amatullah da Aliyu. Da gudu Amatullah tazo ta rungumeta ta baya "Ummina tuwo kike yi?" Asmau ta bata rai "Ama so kike na kone zaki fado min haka. Me ya dawo daku yanzu bayan ba'a tashi ba?" Zulaiha tayi dariya "tunda kika ji ta kiraki da _Ummina_ kema kinsan akwai abinda take so". Amatullah ta kama kasan dan hijab dinta tana wasa dashi, Zulaiha ta dubi Ali "kai da kayi mata rakiya sai ka fadi me ya dawo daku ai" Ya ja baya da sauri "Umma nifa fitsari tace zata yi na rako ta". Asmau ta nuna hanyar bandaki "wuce kiyi kizo ku koma". Sum-sum Amatullah ta wuce bata dade ba ta dawo ta sake tsayawa a bayan Asmau. Zulaiha ta kula akwai abinda take so ta janyota jikinta "Amatullah ta Ummi me kike so ne, fada min naji" Dan turo baki tayi wanda duk lokacin da tayi sai Asmau ta ga kamarta da babanta ta fito sosai Nabila ce take shan kafi kaza kuma Ummi ta hanamu roko shine nazo ta bani biyay na siyo". Zulaiha ta kwashe da dariya "bakinki ne biyay din ai" Amatullah ta dan buga kafa "Umma biyay nace fa ba biyay ba". Wannan karon Asmau ma tayi dariya. Amatullah bata iya fadan duk kalma ma harafin *r*, idan ka fada yadda tayi kuma tace sam ba haka ba. Zulaiha ce ta basu naira biyar biyar ita da Ali suka tafi. Asmau tace " da baki basu ba. Sun baro makaranta takanas saboda kwadayi. Yanzu gobe idan taga wani abin sake dawowa zatayi." "Na sani, rokon ne bana so tayi. Idan suka dawo sai a kwabesu akan hakan. Amma da ban bayar ba karshenta nan gaba bazamu sani ba sai da su roka a makarantar. Asmau ta dage sosai kullum tana yiwa yaran lesson musamman na turanci da larabci. Duk wanda yake da homework zata zauna ta koya masa. A makarantunsu 'ya'yan gidan sun fita daban saboda kokarinsu. Ita kam Zulaiha zuwan Asmau ya janyo mata alkhairi. Manyan yaran Humaira, Muhsin, Amina da Habib duk makarantar gwamnati suke yi. Anisa, Aliyu da Amatullah kuwa a makarantar kudi mara tsada irin ta cikin unguwa suke. Gabaday Asmau ta tattara hankalinta ga 'yarta. Burinta a rayuwa yarinyar ta sami kulawa sosai ta kuma san addininta don gujewa [truncated by WhatsApp] ABINDA AKE GUDU🙆🏽28 Batul Mamman💖 Da yamma Asmau ta dawo daga wurin aiki tun kafin ta bude gate din taji kukan Amatullah. Ji tayi kamar an tsikareta. A duniya babu abinda ta tsana kamar a taba mata 'ya da rashin adalci domin kuwa indai Amatullah tayi kuka a cikin gidannan baya wuce aikin Zinaru. Su Humaira ji suke yi da ita balle tace anci zalinta. Da sauri ta shiga ta sami Zinaru tsaye da bulala ta daga zata sake dukan Amatullah ga Ali da Anisa a tsaye suna nasu kukan. Asmau tayi saurin dauke 'yarta bulalar ta sauka a bayanta. Don ma da mayafi amma ba karamin shigarta tayi ba. Bata damu ba ta duba jikin Amatullah sai ga shati lafcece a bayanta tana ta kuka da sheshsheka. Kawar da kan da take yiwa Zinaru yazo karshe. Bazata zuba ido a kashe mata 'ya ba. Cikin tsananin bacin rai ta dago ido tana kallon Zinarun da ko a jikinta an kamata tana dukan karamar yarinya haka. "Me tayi miki kike mata irin wannan dukan?" "Lallai Asamau wuyanki yayi kauri. Ni kike tsarewa da ido haka kamar wata sa'arki. Ko zaki rama mata ne?" Amatullah sai wani irin kuka take yi, Asmau ta tambayi su Ali me suka yi. Zinaru tace "jikokina babu abinda suka yi. Ba su nake duka ba. Wannan afiruwar yarinyar da har yau ba'a san ubanta ba ita na daka ehe. Na fada na sake nanatawa ta dena kiran Gidadona da Baba taki ta dena. Kun zo kun tare mana a gida kamar tare muka gina shi daku" Rai a bace tace "akan wannan kike neman kashe min ita. A iya zamanmu ban taba tanka miki ba idan kina cin zalinta. Zulaiha ke shiga kullum. To ina so ki sani wallahi kika kara taba min 'ya za'a ji kanmu dake. Na baki girman da zan baki a matsayinki na uwa amma tunda hakan baiyi miki ba zan zauna dake yadda kike so. Kuma da kike cewa ba'a san babanta ba don Allah ki nuna mana naki dangin ko na baban Gidado. Mtsww, gida kuma yanzu na fara zama tunda kema ba naki bane." Zinaru taji zafin maganganun Asmau "ni kike fadawa haka saboda baki da mutumci. Ita Zulaihan ce ta fada miki bamu da 'yan uwa?" Asmau bata tsaya ta karasa sauraron Zinaru ba ta shige daki. Da kyar ta rarrashi Amatullah tayi shiru har bacci ya dauketa tana ta ajiyar zuciya. Kuka ne yazo mata da ta tuna irin rayuwarta. Yau da a gidan aure ta haifi Amatullah babu abinda zai fito da ita daga cikin danginta har wani ya sami damar fada musu magana irin haka. Ta tabbatar har ta mutu duniya bazata taba mantawa da cewa a zina tayi cikin 'yarta ba. Ta cuci karamar yarinya saboda soyayya. Su Humaira sun dawo daga makaranta suma kannensu ke fada musu abinda Zinaru tayiwa Amatullah. Duk sun zo sun dubata har lokacin bacci take yi. Bata farka ba sai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103