Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 85

Chapter 85

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

a goshinta yayi mata wani kiss din ya tafi ya barta a tsaye tana numfashi da kyar. ABINDA AKE GUDU🙆🏽54 Batul Mamman💖 _Gaisuwa da fatan alkhairi gareki Maman Iman da Asim. Nagode Allah Ya saka da alkhairi._ Har motarsa ta fita daga gidan Asmau ta kasa motsi kamar an kafeta a wurin. Daga ciki taji kamar ana taba kofa tayi saurin bude kofar ta shiga da sanda ga takalma a hannu. Tayi sa'a masu kwanan falo wasu sunyi bacci. Na ido biyun kuma ba 'yan tsirku bane. Dakin Sabira ta lallaba ta shiga suma suna kwance. A ranta tace wai sun dade ne da Jikamshi a waje? Ita fa gani tayi kamar bai jima ba. Tana dukawa ta ajiye takalmanta taji ance "Sai yanzu" Ba karamin tsorata tayi ba harda dan tsalle. Ta juya suka hada ido da Zulaiha tana murmushi. "Meye haka kika firgice kamar an kama barawo. Kinga bakinki kuwa?" Asmau tayi saurin dora hannu akan lebenta tana rufewa don a tunaninta ana ganin abinda Jikamshi yayi mata a bakin. Ko kafin ta shigo ji take kamar a lokacin yayi. Ido a waje tace "me...me kika gani a bakin nawa?" Zulaiha sai dariya tace "amma dai kina da matsala. Kowa ya ganki sai yasan baki da gaskiya. Yanzu yanzu kin tonawa bawan Allah asiri har na gano abinda baki son na gane" "Da gaske ana gani? Na shiga uku. Shiyasa a falo suka bini da kallo ashe." sai kuma ta sake rufe baki da ta gane sake tonawa kanta asiri take ta shige toilet da gudu tana jin dariyar Zulaiha. Ita Zulaiha kwanciya ta gyara tana dariya tace "dama wannan angon naki ai banga alamar wasa ba tare dashi. Goben ma gara a kaiki da wuri kada muji dirar sojoji a gidan nan". ***** Wanka Asmau tayi ta dauro alwala ta fito. Dakin dai shiru Zulaiha ma ta gyangyada. Ta dafe kirjinta oh Allah Yasa sauran basu gane ba. Amma Jikamshi ya janyo mata jin kunya sosai. Ko mai bata shafa ba ta saka kayan bacci ta kwanta saboda gajiya. Ji tayi tana son kiransa taji ko yaje gida lafiya. Gashi har daya ta wuce idonta ya soye kamar ba wadda ta gaji ba. Tana ta tantamar kiran nasa taji wayarsa ta shigo. Saurin dauka tayi saboda kada ringing din ya tashi masu bacci. Zaune yake akan gado ya jingina da pillow. Shima tunda yayi wanka bacci ya kaurace masa. Matarsa yake tunani da yadda yaji dadin hirarsu ta dazu. Tana dauka yace "me ya hanaki bacci" Wannan murya ta Jikamshinta ita kadai tasan dadin da take mata. Sai taji kamar kada ya dena magana. Rufe ido tayi taki magana "Ni ne ko? Na biya miki sabon karatu na tafi na barki da bugun zuciya" Sake runtse ido tayi kamar yana gabanta tana jin kunyar kalamansa "ban ce ba fa" "Ai ni nace. Kada ki manta ban dade da jin bugun zuciyarki ba a kirjina, kinsan shi baya karya. Nasan dai nawa yafi naki. Tsoronki yasa baki nutsu ba kinji zuciyar da take bugu da kaunarki. Burina na farko ya cika. Na aureki, na biyun ma in sha Allah zai cika. Shine mu sami zaman lafiya da fahimtar juna" Tayi dan murmushi tace "Amin Jikamshina" Kwanciya ya gyara yace "Kinsan tun yaushe nake son daukar ki? Tun ranar da kare ya biyoki. Daga ranar kika tashi daga matsayin Ummin Safina a wurina kika koma Matar Jikamshi." "Wannan karen naka bai kyauta min ba" "Ni kuwa yayi min komai. Ya bude kofar zuciyar Asmaun Ishaq. Ya kamata ki kwanta haka kafin gobe" Hamma take yi amma kuma bata so ya ajiye wayar. "Bana jin bacci. Gobe nayi idan an gama hidimar nan" Tashi yayi zaune yana kallon wayar da mamaki kamar ita ce Asmau sannan ya mayar kunnensa "ba dai a gidana ba ko?" Asmau tace "to a ina zanyi. Kasan nan yini za'ayi babu lokacin bacci" "Kinga Allah Ya bamu alkhairi, ki kwanta kawai ko babu baccin ki rufe idonki ki huta. Wai bacci! Matar Jikamshi anya kina sona kuwa, a ina kika taba jin anyi bacci ranar da aka kai amarya idan ba auren dole ba?" magana yake da gasken sa ya ma za'ayi ta fadi magana irin wannan. Sai da tayi dariya tace "To bazan tambayeka me ya kamata ayi ba nasan halinka. Yanzu sai kasa na gwammace banyi magana ba, ka fi karfina" "Muka fi karfin juna dai. Dama yaushe zaki tambaya bayan kin san abinda nake nufi." Dariyarta yaji sannan tace "uhmm bari naje falo neman pillow din kujera na dakin sun kare ni kuma bana jin dadin bacci haka." "Kice dai kawai kina so kiyi pillow da kirjin mijinki. Daga gobe ne fa Matar Jikamshi. Har kin fini....." Ya Salaam, bata kara magana ba ta kashe wayar ta fita neman pillow tana dariya. Haka ta dawo ta kwanta don bata samu ba. Shima dariyar kunyar da yasan taji ya gama ya gyara kwanciya yana tuno dan lokacinsu na dazu zuciyarsa na kara nutsuwa da zabin da Allah Yayi masa. ***** Da safe sai da suka yi breakfast kowa ya shirya aka fara komawa gidan Umma wurin yini. Yau atampa ta saka anyi mata dinkin half-gown da plain zani. Ta kashe dauri ta yafa mayafi irin na kayan. Da ta fito falo guda aka saka amarya da farinjini. Kujeru aka jera a waje da tabarmi da kafet. Sai ga Ado Gwanja ya iso da tawagarsa. Wannan aikin Sally ne 'yar Yaya Abu da Ab Kura kamar yadda suka saba kiran babbar 'yar Anti Lami. Sun dage sai sun gwangwaje suma a bikin nan. Tun kafin dawowar Asmau zumuncin 'yan uwan ya karu bayan tafiyar Kawu Rabe. 'Yan mata kuwa da su Shemau aka shiga filin rawa. Amarya dai sai janta akeyi amma ko da can bata iya sakin jiki tayi rawa balle yanzu da tun jiya Jikamshinta ya rada mata baya son rawar nan. Idan zatayi ta jira sai su kadai. Ana ciye ciye biki na ta tafiya aka kira Sabira a waya sai ta fita da gudu tana murna. Anti Bintu tace "ke lafiyarki kuwa" Sauri take ta karasa waje ta taro bakin tace "Anti Bintu 'ya'yan yayyen Mama ne daga Maiduguri. Mota ce tayi musu tsiya tun shekaranjiya suka so zuwa." Ta fita ta taro 'yan uwanta tazo ta gabatar dasu wurin amarya Asmau. "Wannan sunanta Fatima Goni ga kuma Amalus sai Halima Wasagu da Feey. Cousins dina da nace miki suna son zuwa biki" Asmau fuska a sake ta gaisa dasu tana godiya da suka sami damar zuwa. Daga nan aka cigaba da taro har yamma. Sai da magariba ta gabato aka sallami mai waka iyaye suka kira Asmau cikin dakin Hajjo. Jikinta ya gama sanyi ta shiga dakin suna zazzaune. Hajjo ce a tsakiya ga Mama Yalwa, Umma, Anti Bintu, Yaya Abu da Anti Lami don kara irin tasu harda Yaya Tagwai da Uwargida basu nuna mata kyama ba. Nasiha ce suke mata wadda tasa ta kuka kamar an bude famfo. Hakuri ne kowacce take mata nuni dashi domin shine jigo a zaman aure duk son da kuke yiwa juna da miji to sai an kai zuciya nesa. Zama ne ake fatan yi har karshen rayuwa. Suka dora mata da

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});