Chapter 50
Chapter 50
Allah Kadai muke yiwa laifi yafe mana baki daya amma indai dan adam ne to a kowane lokaci ya sami dama sai ya tuna mana da laifinmu ko da bisa kuskure ne. Hakika shaidan dole yayi murna idan yaci galaba ya sanya mutane suka aikata zina domin tabonta baya taba kankaruwa a duniyar mutane dai. Yassar na zaune ransa sai suya yake. Ko kadan abinda aka fadawa yayarsa baiyi masa dadi ba. Mutane basu san laifi indai Allah akayiwa kuma aka tuba Shi mai yawan gafara ne da jinkai. Yamadidi da mai laifi bashi daga cikin kyawawan halayen musulmi. Tsaki yayi ya dauki wayarsa ya kira Col. Ishaq dama ya karbi numbar a wurin Asmau. Ya sanar dashi sun iso lafiya sai dai tuni ya gano akwai abinda yake damun Yassar din. Yayi ta tambayarsa me ya faru ya dage babu komai. Hankalinsa ne ya tashi ya kira Asmau. A lokacin Anti Bintu har da mijinta sun gama bata baki sun fita akan sai tayi hakuri domin zata yi ta cin karo da irin haka. Tana ganin wayar batayi tunani komai ba ta dauka. Wannan muryar mai dadi taji yace "Ummin Safina" Fashewa tayi da kuka mai tsuma zuciya wanda ya sashi saurin tashi daga zaman da yayi. "Asmau me ya ya sameki?" Shasshekar kukanta ya cigaba da ji ya sake kiran sunanta har lokacin bata amsa ba. Hankalinsa a tashe yace "Asmau please ki amsa mana" "Naam" ta fada cikin muryar kuka. To me aka yi mata haka?duk yadda akayi abin ya shafi 'yan uwanta tunda yaji Yassar ma ransa a bace. "Kina son ganin Jikamshin ki?" Ya fada cikin wata irin murya. "Naam" ta sake fada da alamar tambaya duk da kukan da take yi. "Kinji me nace fa ni bana son gulma. In zo ki ganni ki fada min damuwarki?" Sake kankame wayar tayi tana jindadin maganarsa harda dan murmushi. "Kinyi shiru ko ba kya son gani na?" "Eh" sai tayi saurin cewa "a'a" tun kafin ya sake magana. "Ban san abinda ya saka min ke kuka ba amma ki rinka jira sai ina wuri kiyi kuka don na rarrasheki. I will see you soon in sha Allah" Bai jira tayi magana ba ya katse wayar ya tashi ya tafi office din abokinsa. SADAUKARWA GAREKU *MATAN KWARAI NA SAMI SAKON GAISUWA *UMMUL DIHYAH, HASSANA, USAINA, AMINA DA RUQAYYA. SAURA MASU GAISUWA DUK BAN MANTA DAKU BA. NAGODE ABINDA AKE GUDU🙆🏽38 Batul Mamman💖 Har karfe tara na dare ta wuce Col. Ishaq bashi da niyar tafiya. Hira suke yi da Anti Bintu da Kawu Yusuf kamar sun dade da sani juna. Sai ko Amatullah da ta tare a falon tana jikinsa tun bayan tashinta daga bacci. Hatta masallaci da ita suka je da Yassar. Maman Kawu Yusuf kuwa tana daga daki tuni tayi bacci bata san wainar da ake toyawa ba. Asmau tana tare da 'yan uwanta suna tasu hirar amma tana tunanin yaushe Jikamshi zai tafi ne. Gashi a dalilin zuwansa Yassar yayi biris da zancen komawa Kano. Ainau ta dauki waya zata kira babbar Yaya wato Shemau ta tsegumta mata abinda ke faruwa a Zaria Asmau ta hanata. "Naga alama sai da ya tofeku tas ya shigo gidan nan. Kowa sai wani kokarin kyautata masa yakeyi" Ainau tayi dariya "ki ce hakan baya miki dadi duk sai mu daure fuska" "Yaya Asmau mu dai kada ki cucemu ki hanamu zuwa bikin sojoji. Kinsan babu abinda ke bani sha'awa kamar su hada takubba amarya da ango su wuce ta tsakiya." Dijah ta fada tana hango ranar bikin. Daga nan suka shiga tsara biki harda irin kayan da zasu saka. Tun Asmau na hanasu har ta koma sakin baki tana jin yadda suke bayani kamar gobe ne daurin aure. Da ta gaji tace "to amarori sai kuyi hakuri zan bata muku show amma ni bani da niyar aure, dadin abin ma ba cewa yayi yana sona ba kuke ta rawar kai" Ainau tace "jiran *I love you*kike sai kace wata matar da. Yanzu ai alama kawai ta isheki. Dazu fa da na fito falo ba karamar kunya naji ba yadda yake yi miki ga Anti Bintu a wurin." Bata da abin cewa da zai hanasu abinda suke yi sai kawai ta kyalesu. ***** A falon Col. Ishaq yace zai nemi wurin kwana gobe da sassafe ya kama hanyar Kano don ba da niyar kwana yazo ba. Yassar yaso binsa masaukin da zai nema sai dai yadda Anti Bintu ke kallonsa ya gane rashin dacewar hakan ko don kada ya dora masa nauyi. Tace ya daure ya biyo ta gidan yayi breakfast sannan ya wuce. Ya tashi yana yi musu godiyar irin karramawar da suka yi masa, suma suna masa godiyar ziyarar da ya kawo musu. A waje ya tsaya da Amatullah wurin motarsa ya tura Yassar ya kirawo masa Asmau. Daga shiga sallar magriba bata sake fitowa ba. Gabadaya kewarta ta dameshi. Don kada aga rashin kunyarsa tayi yawa ne da tuni ya nemeta saboda ziyarar ma don ita yayi. Tasha tsokana a dakin kafin ta fito. Yassar ne mai yi musu jan ido su dena damun matar ubangidansa. Yana fadin haka ta dage ta kai masa dundu a baya tana cewa duk sun raina ta amma zatayi maganinsu. Tana sakkowa daga matattakalar kofar wajen yana ta kallonta har sai da ta kusa faduwa saboda yadda kafarta ke hardewa. Yayi saurin zuwa inda take yana mata sannu ta dan daure fuska. Yayi murmushi "ashe dai kema kina jin yadda nake ji Asmau." "Nake jin me?" "Dazu garin kallona kika kusa bugewa da bango, yanzu kuma gashi kina neman faduwa" yayi mata murmushi "idan muka yi aure anya zaki bari na rinka zuwa aiki?" Tafa hannu tayi tana girgiza kai sannan tace "ni bansan me zan ce maka ba ma." "Babu abin fada ne tunda kinsan gaskiya" Ya bawa Amatullah ledar alawa yace ta shiga ciki yana zuwa. Sai da ta nunawa Asmau tayi masa godiya sannan ta shiga ciki. Yace "gara ta koma cikin gida kada ki koya mata soyayya tun yanzu" Dan cije lebenta tayi tana murmushi. Har kasan zuciyarta ta amince tana son Col. Ishaq. Bata san lokacin da ta kira sunansa ba a can ciki tana mai jan sunan. _Jikamshi_" Wani irin sonta yaji yana kara shigarsa. Bai taba damuwa da sunan garinsu ba amma saboda dashi Asmau take kiransa har wani dadi yake ji na daban. "Yes dear" Ta sunkuyar da kanta kasa "wai so...so" "Ki fadi abinda zaki fada bana son jan rai. Ko don kinga ina son muryarki. Hmmm? Sai ki rinka kara hargitsani da ita." Murmushi ta sake yi shima yayi. Yana jindadi idan yaga ta saki jikinta tana fara'a kamar kowa. Tace "Wai soyayya muke yi"? "A'a a filin yakin duniya na uku muke" ya bata amsa yana daga gira. "Kina so nayi miki gwari gwari ne sai ki fi fahimta?" Ta kawar da kanta gefe cike da kunya da fargaba. Muryarsa taji yace "Ina sonki Asmau Ummin Safina. Babban burina yanzu bai wuce na aurenki ba da kasancewa tare daku har karshen rayuwata. Kuma zuciyata tana bani kema abinda ke taki zuciyar kenan. Right?" Hawaye taji sun taho mata. Wannan mutumi da ya santa cikin kankanin lokaci kuma yasan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103