Chapter 47
Chapter 47
gaba. Hasashensu ita da Yassar ya tabbata. Wannan kallo da yake yiwa Asmau indai ba na soyayya bane to bata san dame zata kwatanta shi ba. A iya saninta dai yasan komai game da Asmau shiyasa ta fada masa magana ce surikarta ta fada da batayi mata dadi ba shine dalilin kukan. Bata so aka fada masa ba tana tsaye a inda take tun dazu ta soma hawayen da ta rasa dalilinsu. Karshe ciki ta shige kawai ta koma daki. Sai da yaga shigewarta yace "ita Asmau haka take ne da saurin kuka? Na zata a yadda taga rayuwa by now ta zama jaruma wadda zata iya daukar duk abinda yazo mata" Yassar ya bi bayanta zai lallabata ta dawo wurin bakonsu don maganar komawarsa Kano yanzu kuma tabi iska. Anti Bintu tace "tun da can Asmau mace ce mai raunin zuciya. Faruwar wadannan al'amuran sun sa ta kara samun rauni dole ne sai muna binta a hankali har Allah Yasa ta iya sakin jikinta kamar da. Dazu munyi mata nasiha sosai akan toshe kunnuwanta game da irin wadannan maganganun da zasuyi ta tasowa" "Allah Ya kara rufa asiri. Kiyi hakuri I just can't help myself when it comes to Asmau" Tayi dariya "babu komai, mu hakan muke so ma. Allah Ya tabbatar mana da alkhairi" Da yake yasan bazata girmeshi sosai ba sai yayi murmushi "ko Yayata? Kada kice kin gano ni " "Na nawa kuma" tayi dariya. Sai ya rufe fuskarsa da hularsa "amma kuwa har naji kunya." Anti Bintu me zatayi banda dariya ta tashi "haka kake da abin dariya" Dan dakewa yayi shi a dole babu wasa "don dai kawai a gaban in-law nake. Amma ni serious mutum ne. Soja ai baya abin dariya" "Uhmmm naga alama, sai dai ban rike sunan wannan sojan ba" "Call me Ishaq" "To Ishaq kanina Allah Ya bada sa'a. Bari na turo maka ita. Ga abinci nan don Allah ka ci" Daga shi har ita dariya suke yiwa juna sannan yayi mata godiya ta tafi. Da taje dakin Yassar ta gani yana faman bawa Asmau dake kuka hakuri tana yi masa fadan me yasa ya kawo shi gidan. Ta shiga dakin ta zauna a gefen gado "bana son shirme Asmau, meye abin kukan ma. Idan mutum ya nuna kina da mahimmanci a rayuwarsa bai cancanci wulakanci daga gareki ba. Dan gyara fuskarki kije ku gaisa." Ta tashi zata shiga bandaki ta wanke fuskar Yassar yace "Antinmu kema kinyi mubaya'a ne. Naga kin shigo kina dariya" Ta kalli Asmau da ta juyo tana kallonsu " ina wasa da kai ne. Tashi ka bani wuri kazo ka zauna a cikin mata" fita yayi yana dariya kawai. Asmau ta wanko fuskarta ta fito "mubaya'ar me Yassar yake tambayarki?" Ainau da tun dazu bata saka musu baki ba tace "nima abinda zan tambaya kenan" "Ku kyale shi shashancia ne kawai" ta bagarar da zancen ta fita. Ainau tace "ko dai baban Amatullah yana ciki ne" "Kinga ki kiyayeni. Ya isheku daga ke har Yassar" Tana jiyo dariyar Ainau har ta kai karshen korido din da zai kaita falon. A zaune ta same shi yana waya ta zauna a wata kujerar daga can gefe. Yassar yana daga kusa dashi. Sai da ya gama yace "Yassar dan bamu wuri ina son siye zuciyar yayarka" Ya tashi yana dariyar da ta soma bawa Asmau haushi ita kuwa ta bata rai. Ya dan mike kafafunsa "yunwa nake ji" Fuskarta babu wata fara'ar kirki tace "ba ga abinci nan a gabanka ba" "Kince naci ne?" "Au sai nace?" Ya gyada kai yana murmushi wanda yasa ta dan saki fuska. "To ga abinci nan kaci" "Nagode" ruwa ya fara sha sannan ya bude plate din da aka hada masa abincin zai ci. Asmau ta tashi "bari na baka wuri kaci abincin" "No yi zamanki please" Kasa kallonsa tayi yana cin abincin. Shima kadan yaci ya rufe plate din. Haka yake abinci bai dame shi ba. "Asmau kalleni nan" Dan kadan ta iya daga kanta ta dube shi "Ina so ki zama jaruma mai hakuri da dukkan abinda zata ji ko ta gani a wurin mutane. Babu wani abu da bazai wuce ba a duniya saboda haka yawan zubar da hawaye akan magana ba naki bane. Ke uwa ce dole ki jajirce wurin zama macen da ba raguwa ba ko don kada 'yarki tayi koyi da hakan" Yana magana ta soma hawaye har ya kai karshe. Girgiza kansa kawai yayi "Don nace ki rinka barin kukanki kiyi a gabana shine zaki yi kuma. To share hawayen ko na share miki da kaina" Habar mayafinta tasa ta goge hawayen da sauri "Ko ke fa...yanzu ace nazo tun daga Kano amma fuskarki duk a kode" Ta dan turo baki "don zaka zo sai nayi kwalliya?" "Sosai ma kuwa, ko ba kya so ki kara samun karbuwa ne. Yanzu haka zan kama hanya har na koma gida kodaddiyar fuskar nan zanyi ta gani. Da na sani driver nasa ya kawoni" Asmau tace "nifa..." "Ke fa me? Kinga mu bar wannan zancen sai kin koma gida. Wai ina princess dina ne banganta ba" "Sai yanzu ka tuna da ita? Tayi bacci" Ya kwantar da kansa a saman kujera "duk laifinki ne. Kin wani kasheni da ido kinsa bana tunanin komai sai naki. Kije ki tasheta magriba ta kusa kada ki koya mata baccin yamman nan" Asmau ta tashi tana tafiya tana waigensa. Duk juyawa sai yayi mata murmushi sai ta kawai da kai. A na ukun ta kusa karo da bango ya soma dariya "yi a hankali ba yanzu zan tafi ba sai kin koreni da kanki" A kunyace ta shige tana mamakin yadda ya gama da zuciyarta cikin dan kankanin lokaci. ****** Bayan tahowarsu Mama Yalwa taje gidan Umma. Suna zaune harda Hajjo take fada musu yadda suka yi da Qasim a daren jiya kafin ya tafi da kuma amsar da Asmau ta bashi. Hajjo tace "ki ji min yarinyar nan fa. Ita banda abinta ai ba saka mata ido zamuyi ba. Kuma yaron nan Qasimu ya cancanci yabo wallahi. Bari ta dawo muyi magana amma aure ai shine rufin asirinta." Umma tace "nima na yaba da halayensa sosai. Nasan duk abubuwan da take tunani har yasa take tsoron yin aure. Amma ko kadan ba hujja bace. In sha Allah zamuyi mata magana. Ni kaina ban hango mata rufin asiri ba kamar a gidan Qasim. Allah Yayi masa albarka". "Amin" Mama ta amsa. "Kar kiso kiga yadda naji dadin labarim nan. Yarinya ce mai biyayya nasan bazata watsa mana kasa a ido ba. ***** Da yamma ne bayan tafiyar Mama Anti Bintu ta kira Umma tana bata labarin zuwan Col. Ishaq da hirar da suka yi. Cike da murna tace "Yaya Bara wallahi na yaba da yadda ya damu da Asmau. In Allah Yaso shine zai share mata hawayen dukkan damuwarta." Umma bata iya bata amsar kirki ba saboda tunani da ta shiga yi akan maneman 'yarta. ABINDA AKE GUDU🙆🏽36 Batul Mamman💖 Ba karamin damunsa rashin daukar wayarsa da Asmau take yi yayi ba. Sai dai kuma ya kuduri niyyar bazai barta ba. Murmushi yayi....yana son mace mai jan aji, amma bazai bari ta ja masa aji da yawa ba saboda yadda yake ji
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103