Chapter 13
Chapter 13
amma ana dawowa kan Asmau sai kuka. Jafar yace Ummansu tace a zaneta idan bata yi karatu ba. Tunda ta fara kukan farko Abubakar yake kallonta. Dariya abin ya bashi sai da yaga taki denawa ta soma bashi tausayi. Malam Hadi yayi har ya gaji taki karatu sai kuka da rawar murya. Yace kowa ya fita banda manyan yayye. Suna tafiya ya nuna mata Abdulhalim da Abubakar "Waye a cikinsu kika yarda zakiyi karatun a gabansa tunda kin kasa a wurina." Tana daga kai suka hada ido da Abdulhalim ya hade rai. Da shine malamin zaneta zaiyi fes baya daukar rainin hankali. Da sauri ta nuna Abubakar. Malam Hadi yace "to Sadiq ka kwatanta gaskiya ka ji karatun. Ke kuma gobe ki tabbatar zakiyi a gabana ko na samo bulala". Da haka suka fita saura ita da Abubakar. Fuskarsa a sake ya fara tambayarta "shekarunki nawa Asmau?" "Shahudu" "Ashe ma kin girmeni da shekara takwas" Ta dan saki fuska amma muryarta bata dena rawa ba "so kake kace ka girmeni da shekara takwas dai" Yayi murmushi dama so yake ta saki jikinta "Haka ne, ni yanzu ina level two a BUK ina karanta computer science. Ke fa?" "SS1 nake a science class. Likita nake son zama" yadda take maganar yasan ba karamin son hakan take ba. "Very good, sai dai bakiyi kama da likita ba saboda tsoro yayi miki yawa. Likitoci kuma basu da tsoro". Yana kallon bata ji dadin maganarsa ba ya sake yin murmushi. "Kada ki damu akwai maganin tsoro. Shine ki daure ki rinka magana a cikin mutane. Babu mai yanka ki. Iyaka idan kinyi kuskure a gyara miki. Karatun Qur'ani karfin zuciya yake sawa ba ragwanta ba." Shiru tayi tana sauraronsa yana ta janta da zance. Sai karshe yace ta biya masa yaji. Da kyar ta daure hawaye wani na bin wani ta karanta. Kafin tayi rabi kukan ya dauke sai karatun ake ji. Tana kaiwa karshen surar yayi kabbara sannan ya sake karfafa mata gwiwa wurin bude baki a gaban jamaa. Da murmushi ta fito suka tafi gida ran Shema'u a bace saboda tasa sun dade. Tun daga wannan lokacin ko ta fara kukan idan Abubakar yana masallacin sai ta daure. Karshe dai sunanta ya koma Idon kuka saboda kullum sai tayi. Gashi ta tsani sunan. Haka rayuwa ta cigabar musu har lokacin bikin Nasiba. Gidajen biyu suna ta shiri duk da su Umma basu fi shekara daya a unguwar ba. Haka suka yi bikinsu lafiya kalau kamar dangin juna. Su Asmau an kara zama 'yan mata. Yanzu tana dan sakewa har ayi hira da ita. Wani lokaci da Umma zata Wushishi gashi basu yi hutu ba a nan gidan Mama Yalwa ta barsu. Abdulhalim ya tafi bautar kasa Jos yanzu Abubakar ne babba a gidan. Duk da yanayin karatunsa bai hana shi cigaba da zama daukar karatu a wurin malam Hadi ba. Duk cikinsu yafi kowa mayar da hankali akan karatun addini shiyasa Baba yake matukar ji dashi. Watarana an gama karatu kowa ya fita daga masallacin sai Asmau dake zaune tana kokarin kammala aikin da malam ya bata na fitar da hukuncin (NUUN saakina) a thumunin da ya biya mata ranar saboda washegari test gareta a makaranta karatu take son yi. Abubakar yana can wurin zaman liman yana tilawa aka soma iska mai karfi alamun ruwa zai iya sakkowa a kowane lokaci. Da dan gudunta ta tashi zata rufe tagogi kafin ta fita saboda kurar dake shigowa. Har ta gama rufewa Abubakar baiyi yunkurin tashi ba. A take kuma aka dauke wuta saboda wata tsawa da akayi mai karfi. A dan tsorace tace "Yaya Abubakar kazo mu fita kafin ruwan nan ya sauko" Shiru taji sai numfashinsa da ya kara karfi. Gabansa ta karasa sai dai duhu yasa bata ganinsa sosai. Wayarsa da ta taka ta dauka ta haska shi. Kwance yake numfashinsa yana sama-sama da kyar yake fita. Hannunsa daya kuma yana nuna mata aljihun wandonsa. Asmau duk ta rikice ta kuma fahimci abu yake so ta miko masa daga aljihunsa. To kuma Umma tayi musu gargadi sosai akan taba maza wannan yasa ta kasa tabashi ta fita da gudu a cikin ruwan ta shiga gidansu ta fadawa Mama Yalwa. Tare suka dawo har da Suwaiba dauke da irin filtilar nan mai batir. A kwancen dai suka same shi ya hada gumi idanunsa harda hawaye. Mama ta daga kansa ta dora a cinyarta a rude tace "ina inhaler dinka?" Aljihunsa yayi kokarin nuna mata. Tasa hannu ta dauko ta shaka masa. Asmau da Suwaiba suna tsaye suna yi masa sannu. Duk da haka numfashin bai dawo daidai ba. Mama tace a fadawa dreba yazo su tafi asibiti. Bayan fitarsu Asmau ta tafi gida ta sanar da Umma abinda ya faru. ABINDA AKE GUDU🙆🏽11 Batul Mamman💖 Rabe ne ya fito yasha sabuwar shadda sai kyalli take yi. Idonsa a kan Bara'atu da yanayin da ta shiga yayi dariyar mugunta. Don tsabar wulakanci yace "A'a bazawara kune a garin? Ya hanya?" Hawaye take yi wani na bin wani ta durkusa a gaban Hajjo "Nasan har mijina ya rasu baku taba kaunata ba amma Hajjo wallahi cin dukiyar marayu haramun ne. Gidan nan baku da hakki a kansa to a wane dalili zaku zo ku tare batare da izini ba". "Eh, lallai wuyanki ya isa yanka Bara'atu. Ni da gidan dana kike gaya min maganar banza." Hajjo ta amsa itama rai a bace. "Ko kinki ko kinso zama dole muyi a gidan nan. Idan bazaki iya zama damu ba sai ki bar min yaran ki kama gabanki." Yusuf mijin Anti Bintu yace "Anti kada ki sake cewa komai. Ai basu fi karfin hukuma ba. Kuma rabon gado ba hauka bane. Ki bari mu kwana yau gobe sai mu san abinyi." Mikewa tayi cikin zafin nama tana kallonsu daidai. Garzali banda taba babu abinda yake busawa. Rabe da amaryarsa suna tsaye suna mata kallon banza. Hannu tasa ta share hawayenta "Dama can saboda marigayi nake raga muku to amma wallahi yanzu an wuce wurin. Mu zuba ni daku shege ka fasa." Yaranta ta dakawa tsawa duk suka tashi daga gaban Hajjo suka bita cikin gidan. Hajjo da su Rabe kowa yayi tsit suna mamakin wai yau Bara'atu ke mayar musu da martani haka. ***** A cikin gidan dakuna biyu ta samu a bude ita da Yusuf da su Shemau suka rinka shiga da kayansu. Sai cikin dare tana zaune tana kallon 'ya'yanta na bacci ta rinka kuka. Washegari ko karyawa batayi ba suka fito ita da yaran suka hadu da Yusuf zasu tafi ofishin 'yan sanda. Rabe yana tsaye a waje yace " kinga basai kun wahala ba a bayan layin nan akwai gidan wani babban dan sanda. Maza ku tafi ku kai kara kada kuda ya rigaku." Basu kula shi ba suka wuce. Duk wani bayani sun gabatarwa 'yan sandan. Mutum hudu aka hado su dasu suka zo aka bukaci su Rabe su fita. Wannan muguwar dariyar yake yi ya dauko takardun gida sai gashi sunansa ne dana Shu'aibu a jiki a matsayin tare suka gina. Kuka sosai Bara'atu take yi tana karyata shi. Sai dai kuma bata da shaida. Bata san yadda akayi ya sami takardun gidan ba wanda a hannunta suke har akayi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103