Chapter 27
Chapter 27
na uku ta zauna kusa dashi cikin damuwa. "Baban Abba me ya faru ne? Allah Yasa ba laifi nayi ba." Dan murmushi Sada yayi yana kallon abar kaunarsa. "Ko kadan Maman Abba. Bari nayi wankan dai." Sai da ya gama cin tuwo sannan ya bata labarin Asmau mai zuwa kofar shagonsa. "Ni bansan daga ina take ba sai dai ta bani tausayi. Muna ganin kanmu kamar marasa arziki amma wallahi cikin rufin asiri muke akan wasu. Tsorona daya kada taje wurin wani mara imanin ya bata maganin." Rashida tace "to ai dama kaine kullum kake ganin kamar shagonka kadai baya wadata mu. Amma gashi yara hudu duk suna makaranta kuma bama rasa abinci. Idan bazaka damu ba gobe sai na kawo maka abincin da kaina na ganta. Kila idan na bata shawara ta hakura da zubar da cikin ta koma gida". ***** Asmau ta dauko robar da Uwargida ta bata. Tana son sha kuma har ranta bata son zubar da cikin. Dama gudun zubarwar yasa ta fito daga gida. Dan motsin nan da taji ya sa ta kara son abinta. Robar ta dauka ta zubar da kadan a bakin rariya sannan ta mayarwa Uwargida. Bakin Uwargida a washe tace " nan da wayewar gari ma yana iya zubewa. Kinyi kyan kai 'Yar Da6as." Yau ma ta riga Sada zuwa shagonsa. Ita kanta bata san me ya dawo da ita ba. Da yazo har kasa ta durkusa ta gaida shi. Ya amsa mata fuskarsa babu yabo babu fallasa. Yayi mamaki da ko sau daya bata sake batun maganin ba. Tana dai zaune ne kawai a gefe guda. Wuraren shabiyu wata mace ta sha katon mayafi ta iso kafar shagon da flask din abinci. Matar tayi mata murmushi Asmau ta gaisheta. Sada ya fito daga cikin shagon yace "wannan ce yarinyar". Rashida taji tausayin Asmau ba don komai ba sai don yanayin da ta ganta. Har wani wari take yi saboda rashin wanka. Sada yace su shigo ciki ya dan kara kofar alamun ko anzo kada a shiga. Asmau na zaune a kasa a gabansu Rashida tace ta fada musu daga ina take kuma ina uban dan dake cikinta. "Kada kiyi mana karya domin kuwa Allah Yana kallonmu". Karo na biyu kenan tana bada labarinta. Kafin ta gama Rashida tayi ya6e ya6e da hawaye don tausayi. Mata da yawa idan an tambayesu game da ciki a irin wannan yanayin sai suce fin karfi aka yi musu. Amma wannan yarinyar ta zabi ta fada musu abinda suka fi tunanin gaskiya ne. Wato biyewa rudin shaidan da son farantawa masoyi. Shi kansa Sada yaji tausayinta matuka. Lokaci guda tarbiyarta ta wargaje a dalilin kawa da kafafen sada zumunta. Waje suka ce ta fita ta jira su. Muhawara sukayi inda yace su mayar da ita gida Rashida tace kada ta koma sai ta haihu ta yiwu iyayen su yafe mata idan suka ga dan a hannu. Duk da suna tsoron halin Dan Adam yanzu. Kayi masa rana yayi maka dare amma zukatansu sun amince da taimakonta musamman ma suna jin tsoron kada ta zubar da cikin ta fada sana'ar banza. Sada ya rufe shagon suka ce ta biyosu. Babu musu tabi bayansu tana adduar Allah Yasa alkhairi ne a tattare da mutanen. ABINDA AKE GUDU🙆🏽22 Batul Mamman💖 Zahra 'yar Rabe ta biyu ke zaune tana waya da mahaifiyarta Laraba wadda Raben ya dade da saki. A hirarsu ne take fadawa Laraban zancen haihuwar Shema'u wadda akayi kwanaki goma da suka wuce. Tun ranar da akayi haihuwar Yassar yazo ya sanar sai akayi rashin sa'a Rabe da Zahran ne kadai a falon. A wurin ya ci mutumcin Yassar sannan yace da Zahra kada ta fadawa Hajjo babu mai sake zuwa gidan Bara'atu. Laraba duk ta gama sauraren 'yarta tace mata su kara hakuri da babansu. Dama ita ta bata shawarar dagewa taje bikin Asmau. Tace idan ta shigo Kano zata zo tayiwa Umma jajen abinda ya sami Asmau da barkar Shema'u. Hajjo tana tsaye a bakin kofa ta fahimci duk hirar Zahra da Laraba. Ko kwanaki uku da suka wuce sai da ta cewa Rabe wai har yanzu Shema'u bata haihu bane yace wa ya sani ne. Bara'atu da bakin hali kuma. Ta rasa gane irin wannan tsana da yake nunawa iyalin dan uwansa. Dakinta ta koma jiki a sanyaye ta dauko mayafi ta fito. Karnukan Garzali ne suka yo kanta ba shiri ta koma ciki. Dakinsa ta je yana bacci ta daka masa duka a baya. Shi babu arabi babu boko sannan auren ma ya gagara. Sai dai yaje yawo ya dawo gida ya kwanta bacci. A zabure ya bude ido ganin wace ke kansa ya turo baki "haba Hajjo yau kuma me nayi zaki doke ni? Na rantse jiya ban sha komai ba. Sansana bakina kiji". Ta kau da fuska "Allah Ya tsareni na kai hancina bakinka. Ni tashi ka daure karnukan ka fita zanyi. Ka mayar mana da gida kamar dandalin 'yan daba. Motsi kadan sai haushin karnuka." Dariya yayi tare da zuro kafafunsa zai sauko daga kan gadon. Daga bayanta taji ance "ina zaki je?" Gabanta sai da ya fadi don firgici ta juya tana kallon Rabe wanda bata san ya dawo gida ba. Murmushin da bai kai zuci ba ta kakalo "Yaushe ka dawo Alhaji?" Ya basar da tambayar. "Naji kina cewa zaki fita". Kamar ba mahaifiyarsa ba duk ta kidime tace "uhmm dama gidan waccan mara kunyar zani. Ashe Shema'u ta haihu shine ko ta aiko mana. Ai bata isa ta rabamu da 'ya'yan Shuaibu ba ko?" Rabe ya soma jin tsoron yawan ambaton su Bara'atu da take a kwanakin nan sai ya dan dake. "Yanzu a kanta zaki fita cikin ranar nan? Ki kyaleta kawai da halinta. A ce har 'yar dan uwana ta haihu bamu ji ba kawai don bata daukemu a bakin komai ba. Ni daga yanzu na kafa doka babu mu babu su. Tunda haka ta zaba kowa yayi ta kansa." Hajjo ta jinjina kai tama mamakin yadda yake gilla mata karya haka. Ta tabbatar maganar da Zahra keyi a waya ba karya bane. Ta sake gwada sa'arta ta hanyar cewa "Wai dama nace muje ko tare da kai ne mu dan zagesu mu huce haushi" Juyawarsa yayi don kada ta sake jan zancen. " Koma daki kiyi kwanciyarki ki huta Hajjo". Tana kallo ya tafi itama ta juya zata koma dakinta. Hawaye ne ya sauko mata wanda bata san dalilinsa ba ta goge da habar zaninta sannan ta koma daki. Garzali da bai tanka musu ba yaji tausayin mahaifiyarsa ya ratsa shi. Ya rasa dalilin da yasa dukkansu har Yaya Abu da Yaya Lami basu da katabus sai abinda Rabe yace. Amma zaiyi kokari ko yaya ya kai Hajjo taga jikokinta tunda wulakancin da suke musu yasa suka dena zuwa gidan. A daki Rabe ya kasa sukuni. Sagira na masa magana ya daka mata tsawa. Dama ba wani matsayi gareta a wurinsa ba. A duniya babu matar da yake matukar so kamar Bara'atu duk da girma ya kamasu. Sai kuma batun Malamin tsibbunsa. Dama lokaci lokaci yake sake biya a toshe bakin Hajjo da 'yan uwansa. Yanzu idan asirin ya karya yasan Hajjo cewa zata yi su tashi daga gidan Bara'atu ta dawo. Matsalar idan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103