Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 101

Chapter 101

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

su Umma na koma motarsu" "Wani abin ne ya faru kike son canja wurin zama?" Shiru tayi sai kuma ta soma hawaye. Nan da nan hankalin Asmau yayi mugun tashi. Shi kuwa Yassar hannunsa rawa ya soma yi ya sami gefen hanya yayi parking din motar. Asmau tana ta tambayar me akayi mata sai ji tayi Yassar yace "Bilkisu" Ta dago kai idanunta sun kumbura sunyi jawur. "Idan ba cewa zakayi kana sona ba ka rabu dani. Allah zai bani wani" Asmau ta hangame baki cike da mamaki. Rashin kunya a gaban masoyi ta yarda gadon gidansu Jikamshi ne. Anya Bilkisu bata manta tana bayan motar ba. Allah Yasa ma Amatullah tayi bacci. Yassar yace "kema kinsan ina sonki don Allah ki share hawayen kinga a hanya muke" Ta murguda masa baki "a haka ne kana sona tunda ka tafi ba waya ba text sai na gaji na nemeka. Kuma kaki fadawa kowa balle a fara shirin bikinmu sai iya zuwa bikin wasu" Asmau ta shiga tafa hannu a hankali tace "Bilkisu kwantar da hankalinki naji komai muna dawowa in sha Allah magana zata je gaba kinji ko. Kinsan Yassar din ne akwai tsoron mata" Dora hannu Bilkisu tayi a kanta tare da jan mayafi ta rufe fuska. Wallahi ta manta da Asmau a motar. Haushi Yassar dinta ya bata tun bikin su Asmau da ta samu yace yana sonta bai kara waiwayenta ba. A nasa bangaren shima wata matsananciyar kunya yaji. Ko Bilkisun ba don baya sonta yake kin nemanta ba. Shi bai san me zai rinka fada mata ba a waya ko text. Shiru suka yi su biyun Yassar ya tayar da mota Asmau tana ta dariya. Abu yayi dadi zumunci zai kara kulluwa tsakaninsu. Tsabar murna a lokacin ta turawa Jikamshi text tana fada masa. Shi dinma ya nuna farincikinsa sosai yace sai sun dawo. Bilkisu dai har aka isa Jos bebiyar dole ta zama. Ansha biki Zulaiha ta sake bawa Asmau labarin yadda suka kare dasu Zinaru dama ta sanar da ita a waya. Asmau tace ina ma tana wurin ta ga idanun Zinaru mai son kudin tsiya. Daga nan suka koma hirar cikin Asmau da kuma Alh Najib da yake jiran Zulaiha ta gama iddah. Ita dai tace bata da ra'ayin aure tasha wahala a wancan ga yara har shida waye zai dauketa tare dasu. Shawara Asmau ta bata kada ta bari dama ta kubuce mata wurin yiwa babanta biyayya. Ranar Asabar da sassafe suka dauko amarya suka taho Kano da ita. Washegari akayi dinner sannan aka wuce da ita Shanono inda zatayi sati sannan su tafi Zamfara da angonta. Ranar da suka dawo Col. Ishaq kamar ya cinye Asmau. Kwanaki uku kawai ji yake kamar ya dade sosai basa tare. Itama tayi kewarsa domin kuwa duk kulawar da take samu bata kai tasa ba. ***** Cikinta na da wata shida ya fara siyayyar kayan baby. Wani lokacin yaje da ita wani lokacin kuwa sai dai taga ya shigo da kaya. Tun daga gadon yara (cot), kayan sawa da duk wani abin amfani ya tanada. Ita har gajiya tayi da cewa ya barsu haka. Mutum mai shekarunsa zaiyi haihuwar fari sai dai a zuba ido. Wata rana ya dawo daga aiki a gajiye yake fada mata ta hada kaya jibi zasu tafi Port Harcout an tura shi aiki na wata daya. Amatullah sun fara hutu sai a kaita gidan Umma kafin su dawo. Asmau ta zauna ta hada musu kaya washegari suka kai Amatullah gidan Umma sannan suka je yiwa Hajiya sallama. Tunda ya fara bayanin abinda ya kawo su Hajiya ta dakatar dashi. "Babu inda zaka je min da ita da wannan cikin. Wa kuke dashi a can da zaka kaita cikin arna ka ajiye. Idan haihuwa tazo yaya zaku yi?" Yace "Hajiya akwai musulmai kuma da sauran lokacin haihuwar har maje mu dawo" "Kasan Allah babu inda zata je. Ko dai ka fasa tafiyar ko kuma ita ta zauna a nan ko can hotoro. Wannan karon ba kyaleka zanyi ba irin yadda ka tabayi min har na bari kuka koma gida" Asmau kanta na kasa Col. Ishaq yaki shiru don ba karamar cuta bace gareshi tafiyar wata daya babu matarsa. Hajiya ta dage harda kiran Umma. Itama Umman tace abinda ta gani kenan da suka kai mata Amatullah sai dai batayi magana ba. Hajiya tace ta gama magana shawara na garesu. Jiki babu kwari suka tafi gida. Asmau tayi ta bashi baki akan yayi hakuri ya dena nuna bacin rai amma ya kasa. "Matar Jikamshi wata daya ba sati bane. Ta yaya zanyi kwanakin nan ni kadai bayan na riga na saba da yin komai tare dake" Idonta na shirin zubo da hawaye tace "kayi hakuri kaima kasan abinda ta fada domin amfaninmu ne. Bazaka iya fasa tafiyar ba? Wallahi bana son kayi min nisa" Kuka ta soma yi ya rungumeta "bani da yadda zanyi ne. Umarni ne daga sama" A ranar ko kadan basuyi bacci ba sai aikin rarrashin juna. Tayi ta masa kuka har muryarta ta dashe. Bayan ya dawo daga sallar asuba ya hada mata kaya a wani akwatin. Ko abincin kirki sun kasa ci haka suka fita ya kaita gidan Umma ya wuce office. Daga nan dreba ya kaisu airport su hudu suka tafi. Harda Hussaini wanda idan sun dawo za'ayi bikinsa da Walida. Sai da ya kusa sati sannan ta warware ta dena zaman daki. Umma tayi dariya kawai. Safe, rana da dare aiki yana yi masa sauki sai waya. Kafin su kwanta kullum sai anyi video call yana kallonta da cikinta da kuma princess dinsa. **** Kwanci tashi saura kwana biyu ya dawo gida. Ita da Sabira suka je ta tayata gyaran gidan domin tayi nauyi sosai. Harda kitso da kunshi Jikamshi zai dawo. Ranar da zai dawo kuwa karfe tara na safe ta gama shiri zata tafi gida. Umma ta rinka ja mata rai tana dariya a ranta yadda Asmau take ta kallon agogo. Sai goma da rabi ta fito ta ajiyeta a gida ta wuce office. Amatullah tana gidan Nasiba tana karasa hutunta. Karfe daya taji motarsa ta bude kofa da sauri. Col. Ishaq ya tsaya yana kallonta. Ciki yayi girma sosai. Ita ma shi take kallo har wani jiki ya danyi ta fasa rungumeshi taja da baya. Rufe kofa yayi yana binta "haba Matar Jikamshi kada kiyi min rowar kanki. A tausayawa bawan Allah" "Shine kayi kiba duk da baka gani na ko" Ya janyota yana murmushi "yau 'yan rigimar suna kusa ne? Bayan wata daya not even a kiss sai korafi zan samu. Bari na koma tunda bakiyi murnar dawowata ba" Kin sakinsa tayi ta rungumeshi sosai tana kuka "bazaka kara tafiya irin wannan ka barni ba. Kullum da kyar nake bacci" Yayi kissing dinta yana kallon fuskarta "na sani my sweet Asmau. In sha Allah next time kafata kafarki." Daki suka je zai shiga wanka yaga tana dan runtse ido ya tambayeta ko meye tace kafarta ce ta dan rike. Ranar sallah kawai ke fitar dashi daga gida. Kowa yana kokarin nunawa dayan irin yadda yayi kewarsa. Makale suke da juna kamar ranar aka kawo masa ita. A haka kuma tana ta dan jin ciwo daga mararta zuwa baya amma tana cijewa

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});