Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 100

Chapter 100

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ne ya kura mata ido har Col. Ishaq ya lura zaiyi masa magana Asmau ta kallesu. Baki ta bude cike da tsantsar mamaki. "Annur, Gaddafi?" ABINDA AKE GUDU🙆🏽60 Batul Mamman💖 Annur ya soma murmushi haka ma Gaddafi sannan yace "Antinmu wallahi da farko ban tabbatar kece ba. Alhamdulillah, Allah Ya kaddara zamu sake haduwa" Gaddafi yace "an kusa shekara bakwai fa idan ma ba'ayi ba" Asmau sai murmushi take da ta sake haduwa da 'yan samarin da suka taimaka mata lokacin da take nakudar Amatullah. Bata jin zata taba manta kammaninsu duk da a wancan lokacin suna tare da kuruciya sosai bata tunanin zasu kai shekara sha takwas ma. Jikamshinta ta kalla zata yi masa bayaninsu yace "kina fadan sunansu na gane ko su waye" shima fuskarsa da fara'a. Duk wanda ya taba taimakon Matarsa yana ganinsa da kima da daraja. Sannan bashi da mantuwar sunaye indai a tarihin rayuwarta ne. Hannu ya mika musu suka gaisa yace shine mijinta. Fuskokinsu sun nuna jindadin wannan labari sosai. Col. Ishaq yace "ku shiga kuyi siyayyarku sai muje ku ga gidanmu saboda a cigaba da zumunci." "Ai kuma mun fasa zamu dawo wani lokacin." Annur ne yayi maganar yana kallon Amatullah da alamar tambaya amma dai yayi shiru. Tasu motar suka shiga suka bi bayansu Asmau. Col. Ishaq na tuki ta riko hannunsa daya tana murmushi. "Nagode da ka gayyato su gida. Bani da abinda zan saka musu dashi da irin taimakon da suka yi min amma yadda ka karrama su kadai yasa naji dadi sosai." Yayi mata murmushi "Matar Jikamshi, kin hadu da mutane da dama a rayuwarki wanda banda tsohuwar nan ta Azare kowanne cikinsu ya taka wata muhimmiyar rawa wurin nesanta rayuwarki daga lalacewa. Duk wanda ya taimakeki ni ya taimakawa dole na kyautata musu nima" Tsohuwar da ya fada ta gane da Uwargida yake tayi 'yar dariya "Uwargida fa ta shiryu Jikamshina" "Wani suna naji ta kiraki dashi shine raina ya baci." Bata rai yayi sosai Asmau ta rinka dariya. Itama ta tsani wannan sunan wai 'Yar Dabas. Tuna mata yake da zamanta a gidan da irin bakar wuyar da ta sha. Tana dariya yana kallon bakinta ya dan sassauta murya "I miss you" "Gani a kusa da kai fa" "Ba ke ba wadannan lips din nake nufi" Ta danyi fari da ido yace "nagode Allah da Ya bani ke Matar Jikamshi. Komai naki ina so, har da wannan fari da idon" Kamar wadda aka jeho sai jin muryar Amatullah sukayi a tsakaninsu tana daga bayan mota tace "Babana inyi maka fayi da ido nima na iya" Shiru suka yi duk su biyun. Saboda tana ta aikin gwada sabon takalminta sun manta tana motar ma. Ta sake maimaita tambayar yace "Princess ba kyau ayi fari da ido" Ta turo baki "Amma kacewa Ummi kana so tayi" Tohhh yarinya zata kure babanta. Asmau kyalesu tayi don tasan halin Amatullah yanzu ta rinka jan zancen da wata sabuwar tambayar kenan. Sake tunani yayi sannan yace mata "baki ji abinda na fada bane sosai, cewa nayi akwai abu a saman idonta ina so tayi fari da idon sai ya fadi" Amatullah ta koma ta zauna tana cewa "auuu ashe banji ba. Amma dai na iya fayin inyi maka?" Rike dariyarsa yayi yace mata ta bari su je gida yanzu tuki yake yi. Shi da Asmau suka hada ido suka yi murmushi. Dole ne su rinka kiyaye abinda suke yi a gaban Amatullah don wayo ne da ita. Sai kaga kamar bata kula da abu ba sai zance ya tashi ta maido dashi. Kyakkyawar tarba suka yiwa su Gaddafi. A nan suke bata labarin yadda rayuwarsu ta canja bayan haduwa da ita da suka yi harda komawarsu asibiti nemanta. A yanzu basu dade da dawowa daga Jami'ar Madinah ba inda sukayi degree. Asmau taji dadi da ta kasance silar shiriya garesu. Sunyi hira sosai da Col. Ishaq aka nuna musu Amatullah a matsayin yarinyar da ta haifa. Da zasu tafi duk su biyun sunyi mata alkhairi na kudi wanda su Asmau suka nuna rashin amincewarsu. Gaddafi yace sun dauketa kamar 'yarsu ne don Allah kada a mayar da hannun kyauta baya. Haka su rabu cikin mutunta juna har nambobinsu na waya Col. Ishaq ya karba. A hanyarsu ta komawa shagon ne Annur ya cewa Gaddafi "gaskiya mijin Antinmu yana da kirki sosai. Kuma ko ba'a fada ba ba karamin so yake mata ba. Yarinyar nan Amatullah nake tausayi. Nan gaba zata ji babu dadi idan ta gane yadda aka haifeta. Aure wannan sai kaga yazo da matsala saboda bata da uba" Gaddafi yana tuki yace "haka ne amma komai na Allah ne. Gashi cikin ikonsa mamanta ma tayi aure. Nifa saboda labarinta kasan na gama tsorata da harkar mata. Haka kawai shaidan ya gifta tsakaninmu na nazo na mutu na bar 'yar mutane da ciki. Idan ban tuba ba me zan fadawa Allah" "Shiyasa hakan da muke zaune yafiye min komai, idan mun tashi aure sai mu nema ya zamana babu wannan doguwar soyayyar ayi komai idan anyi auren" Dariya Gaddafi yayi "nifa na sami wata sai munje gida zan baka labari. Ban riga na fada mata ba sai munyi shawara da kai" Annur yayi dariya "na dade da gano ku ai, jira nake naji yadda za'ayi abin ban sani ba. Ba Noor kake so ba?" Mamaki ne ya bayyana a kan fuskar Gaddafi. Tabbas kanwar abokinsa yake so amma ko ita bata sani ba. Annur ya bashi goyon baya sosai yace ai yana kula da yadda baya iya boye son nata idan ya ganta. "Kai kuma wa ka samo mana?" "Kaji lokacin da Amatullah tace min Uncle Annuy? Daga lokacin na kudurtawa zuciyata ita zan jira. Yadda Col. Ishaq ya wankewa Antinmu bacin rai na rayuwa haka nake fatan nayi mata nan gaba" Gaddafi yana tuki yana dariya "haba dai Annur kayi mata tsufa wallahi. Shekararka kusan ashirin da biyar fa. Ka bari ta sami yaro daidai ita" Annur ya shafa kansa yana murmushi "idan na sami mata yanzu zanyi aure ko don kare mutuncina amma zancen yarinyar nan ka bari kawai, lokaci ne kawai zai nuna mana" ***** Bikin Qasim ya matso sai da Hajiya ta shiga zancen Col. Ishaq ya yarda Asmau taje. Dama makaranta ma ya roketa alfarmar ta bari sai wata shekarar bayan ta haihu. A gidan Mami zasu sauka harda Bilkisu da Amatullah zasu tafi. Su Umma suma zasu je da Mama. Sunyi mota biyu lokacin Yassar yazo hutu daga NDA inda Col. Ishaq ya sama masa yana yin short service. Shine zai tuka motarsu Asmau shi kuma dreban gidan Mama Yalwa ya tuka su ita da Umma da Shemau. Ranar da zasu tafi Asmau kamar bazata fito daga gida ba. Jikamshi ya makale mata sai mita yake zata tafi ta barshi. Ga dokoki ya kafa na kula da ciki. Ba don sai an kawo amarya Qasim ya shirya dinner a cikin Kano ba ai da binsu zaiyi ma. Sun rabu ana kewar juna suka je suka shiga mota. Yassar ta kula baya magana sosai a motar har tana tsokanarsa ko sababbin sojoji basa magana ne. Bai ce komai ba sai Bilkisu da ta sha kunu a gaban mota tace "Anti Asmau ko zaki tambayar min

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});