Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 14

Chapter 14

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

canje canje haka. Dole 'yan sanda suka tafi domin basu da wata shaida. Yusuf ya nemi ta bishi su koma Zaria daga nan ta koma garinsu da zama. Tana kuka tace "ko zasu kashemu babu inda zamu je. Gidan nan namu ne kuma duk rintse sai ya dawo hannun masu shi." Babu yadda Yusuf ya iya dole ya tafi ya barta. A dakin kwanansu ta sayi risho mai kai biyu da kayan abinci. Kullum suna daki tana saka yadda zata bullo musu. A karshen sati ne abokan marigayi biyu suka zo. Anyi ta kai ruwa rana Hajjo da Rabe da sauran 'ya'yan gidan suka hade musu kai. Magana dai har wurin dan sandan dake bayan layinsu, Adamu Matawalle ashe abokin daya daga cikinsu ne. Shima ya gamsu da bayanansu sai dai ga shaida kurukuru suna gani gida na Rabe da Shu'aibu ne. Shawara suka bata akan ta koma gida kawai tace babu inda zata je. Wani katon fili wanda gida daya ne tsakaninsa da gidan dan sandan ta nuna musu. Rabi nata ne ta siya da kudin kasuwancinta daya rabin kuma Shu'aibu ne ya siya mata. Takardun ta bawa dan sandan ta roke shi ya rike mata amana zata gina kayanta a hankali sannan su tashi daga can gidan. Duk ta basu tausayi. Wani cikinsu ne yayi cuku-cukun nema mata aiki a kamfanin sadarwa na MTN , duk wannan abu batare da sanin su Rabe ba. Tayi musu godiya kamar ta ari baki. Cikin dan lokaci ta saba da iyalin Adamu sai dai kullum a gida take barin 'ya'yanta idan zata je wurinsu. Tana tsoron surutun yara kada su fada a gidan. Makaranta ta samar musu a nan cikin unguwa. Saboda yanayin aikinta ta koyawa Shemau da Jafar girki ko da bata dawo da wuri ba. Zagi da surutu har su Hajjo sun gaji da yi wai tana yawon bariki. Bata kula su ba sai dai bata bari 'ya'yanta sun raina kakarsu ba. Wata rana ta fito suna sauri zata kai yara makaranta ta wuce wurin aiki ta nemi motarta bata gani ba. Rai a bace ta koma ciki ta tambayi Sagira. Sai da ta gama yaukinta sannan tace ban sani ba. Itama Hajjo amsar data bata kenan. Tasan aikin Rabe ne sai tayi kamar ta hakura. Har wani gadara yake yi yana cewa motarsa. Na tsawon sati biyu ta dauke kanta daga kan motar sai dai a bayan idonsa ta sami wani abokin aikinta ya samo mai siya. Ranar Juma'a Rabe na kwance a daki mai siya yazo yaga mota aka gama ciniki ta bashi mota da takardunta. Shi kuma yayi alkawarin kawo kudin ranar litinin. Sam Rabe bai san me ake ciki ba sai washegari ya gama shirin zuwa daurin aure. Ganin babu motar kuma yasan Bara'atu nada mukulli ya tafi kofar dakinta yana ta bugu iya karfinsa. Yaranta duk bacci suke yi ta fito da dogon hijab a jikinta tana murmushi don tasan me ya kawo shi. "kinga ba wasa bane ya kawoni ina kika kai min mota"? "Hmmm, karfin hali barawo da sallama." Ta fada tana tafa hannuwa. Hajjo da Sagira suka fito suka sakata a gaba. Bara'atu ta yatsina fuska "mota dai tawa ce kuma na sayar na cinye kudin. Shikenan ko." Ran Rabe a bace ya zabga mata mari. Hajjo tace kayi min daidai. Bai ankara ba Bara'atu ta kwashe shi da mari shima tana harararsa. "Dani daku a gidan nan daga yau an shata layin rashin mutumci. Na gaji na kai wuya duk abinda zakuyi kuyi. Banda rashin tsoron Allah komai na gado sai mun raba ni daku? To mota dai tawa ce ni kadai" Tsaki taja ta shige dakin ta banko kofa. Hajjo ta kalli Rabe a dan tsorace." Anya yarinyar nan bata shan kwaya kuwa? Kada tasa a koremu fa." Rabe ya dafe kunci "barni da ita Hajjo sai na nuna mata bata da wayo". Sai dai har kasan ransa bazai iya ba saboda son da yake mata. Haka suka cigaba da zaman doya da manja a gidan. Tsakanin Bara'atu da su sai kallo. Yaranta kuwa ta wajabta musu zuwa gaishe da Hajjo safe da dare duk da bata amsawa. A haka har suka shekara daya da rabi tana ta gininta a hankali, sannan duk da tana aiki bata dena kasuwanci ba. Wata ranar lahadi tana daki ta jiyo hayaniya a falo. Yaya Abu ce da Lami suka zo yini da 'ya'yansu. Su Shemau na son zuwa wurin sauran yaran suna tsoron Ummansu. Murmushi tayi tace su je amma banda tsokana. Da gudu suka fice tunda da sauran kuruciya basu gama bambamce masu sonsu ba. Iyayen dai babu wanda ya amsa musu gaisuwa da 'yan uwansu yara suke ta wasa. Kamilu babban dan Yaya Abu ne ya shigo ya soma rungumar kannensa kamar yadda ya saba. Yana rungume da Shema'u yana tsokanarta Bara'atu ta fito idonta ya fada kansu. Mantawa tayi da mutane a wurin tace "Kamilu wane irin wasa ne wannan? Shema'u ban hanaki wannan rungume rungumen ba?" Dena hirar su Hajjo suka yi suka tsaya kallon Bara'atu tana yiwa dansu fada. Lami ta watso mata harara "To kinibabbiya kin fito ne ki fara rashin da'ar taki? Menene aibu don ya taba kanwarsa, yaro da muharramarsa ma sai an nuna musu iyawa" mtws. "Bani da matsala don Kamilu ya taba kanwarsa sai dai Shema'u ba muharramarsa bace shiyasa na hana. Daga shi har ita babu karamin yaron da ba'a budewa littafi ba". "Ya Sayyada manya....indai Yaya Shu'aibu ne uban Shemau to baki isa ki rabata da Kamilu ba domin kuwa iyayensu uwa daya uba daya suke. Kinga sun zama muharraman juna". Kallon Lami kawai Bara'atu tayi ta girgiza kai zata koma ciki Hajjo ta dakatar da ita. "Sai kin fada min dalilin son raba min kan jikoki tunda kin gama fetsare kafafunki". "Hajjo ni ba rashin kunya nazo yi miki ba. Wannan abu ba fadata bace. Da yawa mutane muna jahiltar abinda ake nufi da muharrami. A musulunce duk mutumin da ko ku kadai kuka rage a duniya aure ya haramta tsakaninku shine muharrami." Yaya Abu tace "to ina kuma alakar jini da take tsakaninsu? Ita kuma an datse ta kenan?" Bara'atu ta fahimci neman kureta suke yi sai dai kuma tana da hujja ba da ka tayi magana ba. "Alakar jini bazata hana aure tsakaninsu ba wannan yasa ya zama ba muharraminta ba. Mutanen da suka amsa wannan suna a garemu sune kaka(namiji),'yan uwansa wanda suka hada uwa, uba ko uwa daya uba daya amma banda 'ya'yansu. Haka kuma yake ga bangaren kaka(mace), sai 'yan uwan uwa da na uba suma wanda suka hada uwa, uba ko uwa daya uba daya amma banda 'ya'yansu. Sannan sai 'ya'yan kanne maza da mata. Babban misali shine Sayyadina Ali RA kani ne ga Annabi Muhammad SAW domin iyayensu wa da kani ne. Nana Fadima bazata iya auren Abu Dalib ba saboda kawun babanta ne amma ta auri dansa duk da cewa kani ne ga mahaifinta. Sannan ko a gidan nan Rabe da ya auri Sagira ai kanwarsa ce tunda Hajjo da babar Sagira shakikan juna ne. Muna yawan yin kuskure sai muce 'ya'yanmu 'yan uwa ne mu bari suna taba juna ko suna shiga dakin juna kai tsaye da sunan 'yan uwan

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});