Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 22

Chapter 22

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kazanta saboda karatun labari wanda a ciki tsafta da kula da miji ake koyarwa? Wata ma bata girkin akan lokaci sai taji mijinta ya kama kofar gida zai shigo ta ruga kicin. Wata ta bar yaro da kazanta har sai ta gama karatu. Wata kuwa da wayar zata shigo bandaki tana biyan bukatarta tana karanta labari. Idan hakane karatun labaran masu dauke da darussa bai amfanemu da komai ba sai kasala, ganda da kazanta. Ki zama mace mai tsari a rayuwa komai kiyi shi a lokacin da ya dace. Babu abin takaici sai kinga mace da tsakar dare ko asubar fari tana cigiyar novel ga mijinta a gefe bawan Allah kila yaso ta bashi hakkinsa na aure ma amma ya hakura don kada ya takurata. Idan mara hakuri ne ayi ta samun sabani. Asmau nasan Yaya Bara tana kokarinta a kanku. Gashi aiki yayi mata yawa duk don biya muku bukatu. Kada ki watsa mata kasa a ido da dabi'u marasa kyau kinji ko". An tuno da Idon kuka ana mata fada tana sana'arta. A take tayi nadamar daukar shawarar Walida wanda yasa take yin abubuwan da a da can tasan basu dace ba. Kukanta ya tsananta da ta tuna tabbas irin yadda suke gudanar da soyayyarsu yanzu yana da alaka da canjin da ya fara tasowa daga gareta. Wai ita ce suke rungumar juna da Abubakar. Abubakar dinta mai riko da addini ta zama sanadiyar da suke munafuntar kawunansu da iyayensu. Anti Bintu ta cigaba da yi mata nasiha mai ratsa zuciya sannan ta tashi. A ranar ta ga canji sosai a wurin 'yar tata. Asmaunta ta da ta dawo. ***** Abubakar na kwance a daki yana kallon wasu hotunan Asmau. Tun daren jiya da ta turo ko baccin kirki ya kasa yi. Yau da ciwon mara ya tashi irin wanda ake samu idan sha'awa tayiwa mutum yawa. Ya rasa abinda yake masa dadi ko office ya kasa zuwa. Shawara ya yanke zaije Zariya a ranar ko dan yaya yayi dan abinda zai kwantar da kwadayinsa. A yadda yake sonta bazai iya neman wata matar a waje ba. Ita dinma bashi da niyar ayi mai gabadaya ta bakin Qasim. Dan dai abinda ba'a rasa ba yadda sai samu yaji dadi. Da wannan shawarar ya tashi yayi wanka ya hau shirin zuwa Zariya. ABINDA AKE GUDU🙆🏽17 Batul Mamman💖 Kafin ya fito ya kira Asmau a waya ya sanar da ita zai zo. Jikinta a sanyaye ta amsa masa don ita yanzu kunyar ganinsa take yi. Ko ba'a fada ba daga nasihar Anti Bintu tasan cewa duk abinda ya faru laifinta ne. Har daki taje ta sanar da Anti Bintun zai zo kamar yadda ta saba. "Ki dora abinci dashi amma ki bar dan waken sai gobe don bazan bawa suriki dan wake ba" Ita da Asmau duk dariya sukayi sannan ta wuce ta dora shinkafa da miya. Wuraren karfe uku ya iso Anti Bintu tazo suka gaisa sannan ta basu wuri. Yau Asmau hijab ta saka dogo har kasa fuskarta babu kwalliya sai hoda da kwalli. Jikinta duk babu kwari tayi nadama sosai. Abubakar kuwa tamkar ya hadiyeta da kallo. Anyi sa'a yaran gidan suna ta gilmawa a falon. Da laasar suka tafi islamiyya shi kuma yaje yayi sallah. Ana idarwa ya dawo ya kalli Asmau dake zaune a can gefe. "Asmy dawo nan kusa dani nafi jindadi". Ya nuna kujerar gefensa. Tashi tayi kamar wadda kwai ya fashewa a ciki. Tana zama ya kama hannunta ya rike yana lumshe idanu. Can kasa take jin muryarsa "I love you so much Asmy. Ina ma anyi aurenmu kiga irin abinda nake nufi." A kwanakin baya har so take ya rike mata hannu amma yau sai taji ta tsani hakan. Tana son nuna masa kuskuren abinda tasan ya fita sani amma dole tabi lamarin a hankali kada yayi mata mummunar fahimta ko yace ta mayar dashi dan iska. Har lokacin tafiyarsa yayi bata iya sakin jiki dashi ba. Shi kuwa gabadaya ya kasa samun nutsuwa. Bakin motarsa da ya ajiye a wajen gate ta raka shi ai kuwa yana bude motar ya rungumota jikinsa. Dama layin ba mutane sosai saboda unguwar bata gama cika ba ga duhun dare. Wasu hawaye masu zafi Asmau taji sun taho mata ta hadiye. Dole ta sami lokaci suyi magana da Abubakar akan wannan abin. Rungumar da take jindadi daga gareshi yau bata so. Tana wannan tunanin taji yayi mata abinda bai taba yi ba. Abinda take ta mararin faruwarsa. Bakinsa ya hada da nata yayi mata rikon da bazata iya kwatar kanta ba koda tayi niyya. Hawayen da take boyewa ne suka sakko ganin Abubakar tamkar baya cikin hayyacinsa. Abubuwan da yake mata sun fara wuce gona da iri. Ba shi ya saketa ba sai da don kansa yaji hankalinsa ya fara dawowa gareshi. Ganin tana kuka ya soma bata hakuri. "Asmy kiyi hakuri please. Na rasa dalilin da yasa nayi miki hakan. Ki sani ina sonki tsakani da Allah kuma in sha Allah bazan sake kwatanta miki haka ba sai munyi aure". Yadda yake maganar sai ya bawa mutum tausayi. Tabbas baya son abinda yake yi sai dai karfin sha'awarsa da tsananin rudin shaidan yasa ya kasa hakuri. A hankali ta share idonta "Yaya Abubakar don Allah mu dena irin wannan abin kaga babu kyau." "Na sami Asmy, ni kaina na rasa gane yadda akayi muka fada ga wannan masifar. Ki share idonki kinji matar Abubakar". Kafin ya tafi sai gashi ta sake sosai hankalinta ya kwanta. Suka rabu zuciyar kowa tana nata sake saken. ***** Abubuwan da suka gudana tsakanin Abubakar da Asmau su suka rinka yi masa yawo a kwakwalwa. Yayi tunanin zaiji saukin sha'awar dake damunsa sai abin yayi tsanani sosai. Kullum cikin mafarkinta yake yi. Baccin kirki ya gagare shi sai tunanin yadda zaiyi ko dai a matso da aurensu ko ya kashe yunwarsa ko sau daya ne. A nata bangaren hatta hirar da suke yi a waya yanzu tana kame bakinta daga hirar da bata dace ba. Ta tarkarta tunaninta kaf zuwa lokacin aurensu ko sa sami nutsuwa da kwanciyar hankali saboda tasan duk su biyun yanzu a matse suke da ganin wannan lokacin. Bayan kwana biyu ya sake zuwa wannan karon ko waya baiyi mata ba. A hirarsu da Anti Bintu ya nemi izinin ranar asabar da Asmau zata tafi zai zo ya kaita da kansa a cewarsa baya so ta shiga motar haya. Anti Bintu tayi shiru na dan lokaci saboda ba haka sukayi da yayarta ba. Dama tasha za'a kaita ta tafi saboda motar Kawu Yusuf tana gareji wurin makanike. A duk dan tunaninta bata hango wata matsala ba duba da irin siffa ta kamala da suke dashi su biyun. Asmau kanta bata ji komai ba saboda yau hirarsu duk irin ta da ce. Cikin nutsuwa da kiyayewa. Soyayya mai tsafta irin wadda masu yinta basa son rabuwa da juna. Kwanaki ukun da suka zo kafin tafiyarsu Abubakar yaji babu dadi. Har wani zazzabi ne ya kamashi saboda ji yake tamkar ana hura masa wutar sha'awar kasancewa da mace. A yadda yake ji ko ba Asmau bace wannan karon zai iya nema. Ranar da zasu tafi wurin karfe goma ya iso. Asmau da yaran harda dan kukansu

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});