Chapter 52
Chapter 52
tayi abinda zai bata masa rai. Amma laifinsa ne don ranar da suka dawo yace zai zo shiyasa yau ta fito wurin Qasim da kwarin gwiwarta. So take yi ta fara sallamarsa sannan shima wanda yayi nasarar samun soyayyar tata ta nemi su rabu. Duk iya tunaninta karatu ne kawai mafita garesu ita da Amatullah. Qasim bawan Allah ya kula da yadda ta canja lokaci guda har ya fara tunanin waye a motar. Motar ya rinka kallo da Asmau. ****** Kamar ya juya haka ya rinka ji sai dai kuma hakan ba girmansa bane tunda har ya shigo gidan. A zuci ya karanta *Hasbunallahu wa ni'imal wakeel*har yaji bacin ran ya ragu sannan ya fito yana zuba _kamshi_. Taku yake daidai har ya iso kusa dasu. Kamshin turarensa da yake sanya Asmau nishadi ne ya fara ziyartar ta. Taji bugun zuciyarta ya tsananta. A iya saninta da Jikamshi baya boye magana ko gaban waye. Bata san me zai ce a gaban Qasim ba, mutumin da bai cancanci wulakanci ko kadan ba daga gareta. Yana karasowa ya saki fuska duk da ta ciki na ciki ya mikawa Qasim hannu yayi masa sallama. Qasim ya karbi hannun shima cikin fara'a ya tashi suka gaisa. Sai kuma suka kalli Asmau suna jira ta gabatar dasu. Tsuru tayi da ido kamar wadda tayiwa sarki karya. Da kyar ta saita kanta tace "Yaya Qasim ga baban Amatullah da nake fada maka. Col. I M Jikamshi." Sake kama hannunsa Qasim yayi yana murmushi "naso ace har gida nazo na sameka domin kara mika godiya bisa taimakon da kayi mana. Allah Ya saka da alkhairi Ya bada lada. Ashe manyanmu ne masu tsaron kasa. Bari na baka girmanka yallabai." Gyara tsayuwa Qasim yayi ya daidaita kafafunsa sannan yayi saluting Jikamshi. Shima murmushi yayi ya tsaya a attention ya mayar masa da salute din duk suka yi dariya banda Asmau. Col. Ishaq yace "ka kirani Ishaq kawai. Asmau bata iya kiran sunana kai tsaye ne shiyasa kaji tana maka kwana kwana ko" ya fada yana mata kallon da ke kara kashe mata zuciya. Ta sunkuyar da kanta kawai. Abinda take gudu kenan ya bata kunya a gaban Qasim. Ta daure tace "ga Yaya Qasim shi dan sanda ne" "Allah Sarki, its a pleasure meeting you. Ai ta bani labarinka. Kune manyan ai muna bayanku. Baka ji ana cewa abokin kowa dan sanda" Col Ishaq ya fada yana kara kallonsa zuciyarsa fal kishi yana ta kokarin dannewa. "Nima ta fada min yadda ta hadu daku. Muna kara godiya." "Kada ka damu ai yiwa kai ne. Amma me kuke yi a waje haka ga kura? Ina tsammanin damuna ta kusa tsayawa dai" yadda yayi maganar Asmau ce ta fahimci da biyu yake yi. Shi kuwa Qasim ya dan sosa kai yana dariya. Ko babu komai Jikamshi ya girme shi "Yallabai kenan. A tayamu addua dai muna nema ne" Wani abu ne ya tokarewa Col Ishaq makoshi yaki sauka kasa. Wai ya taya shi addua. A zuciyarsa yace (Allah Yasa kada ta taba yi maka soyayya irin ta mace da namiji.). Abu daya ke yi masa yawo a ka shine kada Asmau ta juya masa baya. Wannan Qasim din wani sanyi ne gareshi mai sa mutum yaji dadin mu'amala dashi. A fili kuwa murmushin yake yayi "ah to bari naje naga Amatullah sai na tafi. Dama ita nazo gani kewarta ta isheni" daga nan gefe ya matsa ya kira Yassar. Bai dade ba ya fito ya shigar dashi ciki. Ransa a bace da ya hango Asmau da Qasim yana taya Jikamshi kishi. Bayan sun shiga ciki Qasim yayi ta yabon saukin kai irin na Col. Ishaq "kamar ba babban soja ba, ji yadda yake jana kamar ya dade da sanina" "Uhmm" kawai Asmau tace a sanyaye. "Asmau wace shawara kika yanke mana?" Ta dago kai a hankali "Yaya Qasim ni dai da mun bar maganar nan" "Kinga Asmau duk abinda kike gudu baki da tabbas a kansa. Yana iya faruwa ko kuma kiga bai faru ba. Haka nan ma masu aure na fuskantar matsaloli musamman mata daga dangin miji. Bance komai zai tafi mana daidai ba amma nayi alkawarin tsaya miki har karshen rayuwata" Tausayinsa ta kara ji. Banda tsoronta na aure ko kadan bata jin son Qasim sai tausayinsa saboda yadda yake mata. "Ka dan kara min lokaci, ban samu nayi maganar da Umma ba" "To babu komai, shi garaje ai bashi da alkhairi. Duk yadda kuka yi ki sanar dani. Sannan zan kiraki idan na koma gida in sha Allah. Akwai keke da na siyowa Amatullah bari na dauko yana bayan mota" "Nagode" "Wai kin gode, mutum da 'yarsa? Shiga ciki bari na dauko" Da sauri sauri tayi shige. ***** Daga kallon kofa sai agogo Col. Ishaq yake yi tunda ya zauna hankalinsa baya tare dashi. Ji yake kamar ya koma wajen ya hana zancen. Hajjo ce take kokarin janshi da hira sai Amatullah tana bashi labarin Wushishi. Yassar kuwa kamar yaje ya dauko Asmau yake ji. Da ta shigo Jikamshi ya kafe ta yayi da ido ta kasa kallon inda yake kawai sai ta shige dakin Umma inda suke ta hada kaya ita da Ainau zata koma gidanta washegari. Qasim ya shigo da keke mai kyau na yara. Amatullah sai tsalle da murna. Tana ta cewa ta gode kamar yadda Umminta ta koya mata. Hajjo ta dubi Col Ishaq "da kai da Qasim kuna shagwaba yarinyar nan da yawa. To ni ina nawa keken?" Suna dariya Yassar yace "kada ki damu ni zan siyo miki irin mai katuwar tayar gaban nan na zamaninku" Umma ta fito tayi godiya sannan Qasim yayi musu sallama ya fita. Sai da suka ji tashin motarsa Col Ishaq shima ya tashi yace da Amatullah ta kira Umminta su gaisa. Umma ta jinjina kai tunda ya shigo dazu ta kula ransa a bace yake yana dannewa. Gaskiya akwai matsala nan gaba sai dai fatan Allah Ya zabawa Asmau mafi alkhairi cikinsu. ***** Tana kwance akan gado har wani zazzabi ke neman kamata saboda tunani Amatullah ta fada mata sakon babanta. Ta dan zaro ido "Baba Qasim ya tafi?" "Eh ya tafi kuma ya kawo min keke mai kyau" "Kinyi masa godiya ko" "Nayi masa Ummi" "Muje kiyi wasa kafin lokacin bacci yayi" ****** Baya falo da ta fito sai ta saka takalmi ta fita waje. Tsaye yake a jingine da motarsa yana danna waya ta hasko fuskarsa. Kamar mai taka kwai haka Asmau ta karasa gabansa. "Ina wuni" Muryarta tana masa dadi, wani irin sonta yake kara ji yana shigarsa. Sai dai kishi yasa ya kasa amsa gaisuwar. "Asmau wallahi ina da kishi sosai. Kada ki bari na kara ganinki a yanayi irin na yau. I can't take it" Ta kara sunkuyar da kai da jin furucinsa. "Kinga ki dago kanki ki kalleni magana zamuyi" Mayafinta tasa ta rufe fuskarta gabadaya. kunyarsa take ji. "Kina so na bude fuskar ne da kaina?" Ta girgiza kai da sauri "To ki bude da kanki kafin hakurina ya kare" Hannu tasa ta bude fuskar tare da dagowa a hankali. Fuskarshi ta bata tsoro saboda babu digon wasa "Jiranki da nayi a falo dazu yana cikin lokutan da bazan manta ba a rayuwata. Zuciyata bazata juri ki hadani
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103