Chapter 26
Chapter 26
tuba ba shikenan haka mutuwa zata riske shi yana halin sabawa Mahalicci. Taci kuka har ta godewa Allah a wurin. Har rana ta take naira hamsin da biyar ta hada. Ga jiri na dibanta saboda tsabar yunwa. Tashi tayi ta kama hanyar gidan da yanzu shine matsuguninta. A hanya ta sayi fanke na naira hamsin din da pure water guda daya. Dakinta ta wuce wanda ko jawo kafar batayi ba. To me zata rufe bayan bata da komai. Fanken nan ta janyo tana ci hannu baka hannu kwarya. Ko uku bata ci ba sai amai ya taso mata. Dole ta hakura ta dan jingina da bango tana adduar kada ya fito don ta dan ji kwarin jikinta. Ba don tana gudun mutuwar kafirci ba gani take yi a wannan lokacin gara ta mutu ta huta. Tana jin shigowar Uwargida ta tashi ta bita daki. Bazata iya cigaba da bara ba gara kawai tayi abinda zai fishshe ta a nata ganin. " 'Yar Da6as yau tun safe kina ina?" Asmau ta dan waiga bayanta tana dube dube. Uwargida tace "indai Zubaida kike nema na kaita wurin uwargijiyata a wannan sana'a. Girma ya fara kamani dolenta ta nema mana kudi. Yaya Babba zata koyar da ita ta karfin tsiya sannan ta dawo gidan nan ta taimaka wurin dago darajarsa kamar da." Tausayin Zubaida ya kama Asmau. Yarinyar da bata kaunar zaman gidan ma bare sana'arsu ace wai mahaifiyarta da kanta take son lalata mata rayuwa. Sai dai babu taimakon da zata iya yi mata yanzu. Kanta a kasa tace "idan kina da maganin zubar da cikin ki bani". Wata shewa da tafi Uwargida tayi cike da murna. Tasan za'a rina. Wannan yanzu idan ta fara bawa Asmau abinci na sati tuni zata murmure ta fara caskar kudi da ita. " kin taimaki kanki kuma na tabbatar bazaki yi dana sani ba muddin kika fara jin jakarki da nauyi. Bari na dauko miki wani jiko da na bawa Darling kwanaki." Uwar dakinta ta shige ba jimawa ta fito da wata robar swan da ta dafe da datti. Ruwan ciki kore ne fatau ga wasu 'ya'yan ball suna ta shawagi a ciki. Asmau na ganin robar taji amai na yunkurin fitowa. Toshe bakinta tayi ta karbi robar ta fita bayan Uwargida tayu mata bayanin yadda zata sha. Tun da ta ajiye robar ko kallon wurin bata sake yi ba. A matsayinta na wadda take da ilimi daidai misali tasan shan wannan kazantar babbar illah ne gareta. Washegari wurin karfe goma ta tashi ta shiga cikin kasuwa. Tasha yawo sannan Allah Ya sa taga abinda take nema wato chemist(kemis). Daga saman an rubuta *SADA AND SONS CHEMIST*. Mutane ne suke ta shige da fice a wurin ta rakube daga can gefe tana jira suyi sauki ta je ta roki mai kemis din ko zai taimaka mata da maganin zubar da ciki. Sama da awa daya bata ga alamun mutanen zasu yi sauki ba har ta gaji ta soma gyangyadi a gefen wani benci da aka ajiye a wurin shagon. Cikin bacci taji an soma kiraye kirayen sallar azahar ta bude ido tana hamma sannan ta dan kalli kofar shagon ta ga akwai mutum daya a ciki har yanzu. Daga can nesa ta hango wani yaro da kayan makaranta da flask din abinci ya nufo wurin shagon. Ta tashi ta kade jikinta da niyyar idan ya iso zata roke shi ko ya rage abinci ya bata. Yana zuwa kuwa ta dan sauke murya. "Don Allah in ka rage abincin makarantar ka bani in ci". Yaron da zai kai shekara goma yana da dan jiki ya kalleta yayi murmushi "Kwanon abincin makarantana na mayar gida. Wannan na babanmu ne na kawo masa". Daga haka ya shige cikin shagon. Ba dadewa suka fito wurin 'yar rumfar kofar shagon inda bencin yake. Yaron ya ce "Baba kaga almajirar da tace na bata abincin naka". Mal Sada mai kemis ya dan kalli Asmau. Tabbas babu wanda zai mata wani kallo daban da na almajira. Dogon mutum ne mai dan haske da kiba. Fuskarsa kadai zata nuna wa mutum yana da kirki. Da hannu ya yafito wata mai awara yarinyar ta karaso da gudunta don kada 'yan talla 'yan uwanta su riga ta zuwa. Ya zira hannu a aljihu ya dauko naira dari ya mika mata. "Zuba wa matar nan ta sittin sai ki bata canjin. Abba miko mata ruwa a cikin fridge dinnan guda biyu." Mai awara da Abba suka yi yadda Mal Sada ya saka su. Asmau na karba ta rinka yi masa godiya da fatan alkhairi sai ka zata ta dade tana sana'ar bara. Mal Sada ya dan daure fuska "nan ba wurin zaman almajirai bane kinji ko. Idan kin gama ci ki tafi." Ta gyada kai ta koma gefe ta zauna. Da ledar ruwa daya ta wanke hannunta ta fara cin awarar cikin jindadi. Rabonta da abincin kirki ta kwana biyu. Tana gamawa tasha ruwa sannan ta dauki daya ledar ruwan tayi alwala ta shimfida dankwalinta tayi sallah. Lokacin tuni Abba ya tafi. Sada yana kallonta sai ta burge shi da bara bata hanata ibada ba. Bayan ya dawo daga masallaci yana bude shagon kafin kowa ya shiga ta bi bayansa. Sai kuma kunya ta hanata fadin abinda ya kawota. "Kina bukatar wani abu ne?" Kamar mai rada tace "nawa ne maganin zubar da ciki?" Cak ya tsaya yana kallonta. Wato ban da bara har jikinta take sayarwa. Ransa a bace yace "idan baki fice min daga nan ba ranki zai baci. Ku baro gidajenku kuna bara saboda mutuwar zuciya karshe almajirai da marasa zuciya irinku su rinka yi muku ciki. Ko ina dashi bazan bayarba." Asmau ta soma kuka tana rokonsa ya taimaka mata. Daga hannu Sada yayi kamar zai maketa shiyasa ta fita. Amma a kofar shagon nan ta zauna har taran dare lokacin da yake rufewa. Ko kallonta baiyi ba da zai wuce tana ta masa magiya. Washegari tun kafin yazo shagon ta iso. Yinin ranar da ta ga babu mutane sosai sai ta shiga ta roke shi. Tun yana mata fada ta fita har ya dena kulata sai ta ga wani zai shigo ta fice a sanyaye. Dansa Abba ya sake kawo masa abinci amma yau bai bi ta kanta ba. Yana ciki yana cin abincin ne ya jiyo kakarin amanta. Tun awarar jiya bata sake samun wani abincin ba. Kamar ya share sai ta bashi tausayi ya dauko flask din ya mika mata. Idanunta sun kara fitowa waje sai hakora gayau kamar ta shekara tana jinya. Kusan fizgar flask din tayi ko wanke hannu bata yi ba ta soma cin abincin. Abinda bata taba ji bane ya faru a wannan lokacin. Motsi taji a cikinta wanda ya kara tabbatar mata lallai ba ita kadai take rayuwa ba. Yanayin da ta shiga da jin motsin yasa ta farinciki ta dafe cikin. Tunowa da Abubakar da halin rayuwarta kuma yasa ta koma yin kuka. Abincin da bata iya cinyewa ba kenan. Da Sada zai tafi ta mika masa flask din yace ta rike ya bar mata. Yana kallonta ta tafi har ta bace masa. ***** Sau biyu kenan Rashida tana fadawa maigidanta ta kai masa ruwan wanka sai yace to ina zuwa. A karo
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103