Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 28

Chapter 28

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

suka tashi basu da wurin zuwa. Ya riga ya sayar da gidansu na kofar mazugal ya mutstsike kudin batare da sannin kowa ba. ***** Baaba Ta Annabi tana zaune kofar wurin girki tana tsintar wake taji sallamar yayarta Hassana wadda suke kira da Yaya Tagwai. Farantin waken ta ajiye ta tarbo su cikin farinciki. Ta Annabi ta kalli 'yar daya yayan nata Usaini tace "auta ba kya laifi kullum kina kuturin Yaya Tagwai. Naga alama idan anyi bikinki tare za'a kaiku." Yaya Tagwai tayi murmushi tana kallon Harira autar dan uwanta . Ita Allah bai bata haihuwa ba shine ya bata Harira take ruko duk da a gida daya ma suke da zama. Tabarma Ta Annabi ta dauko Harira ta shimfida musu suka zauna aka gaisa. Ta tambayesu ya suka baro mutanen Misau. Sai da suka ci abinci ne Yaya Tagwai tace ina sauran yaran gidan. Ta Annabi ta fada mata sunje biki ne a dangin Babansu. Ita ma girki zata karasa ta tafi. Yaya Tagwai tace " gara da nayi sa'ar ganinki. Ke Harira tashi ki tafi gidan yayarki kafin nazo na sameta ita ma." Fitar Harira ke da wuya Yaya Tagwai ta kalli kanwarta rai a bace "kin kyauta Ta Annabi, wato don ni ban haihu ba shine kika kira Usani kina sanar dashi katobarar da 'ya'yanku suka yi. Allah Yasa ina labe a bakin kofa naji duk abinda kika fadawa Ado ya sanar dashi. Don shashanci sai ji nayi yana sanya musu albarka. Sai da na kare masa tanadi na taho. Duk tsiyarku nice babba dole kuyi yadda nake so daga ku har 'ya'yan naku." Ta Annabi ta dukar da kanta. Yaya Tagwai akwai rikon zumunci sai dai bata da hakuri. Hakuri ta bata sannan tayi mata bayanin yarinyar da Sada da Rashida suke riko. Sada da Rashida auren zumunci suka yi. Shi Sada dan Ta Annabi ne ita kuma Rashida 'yar Kawu Usaini. Tun farkon zuwan Asmau yayiwa mahaifiyarsa bayani a kanta kuma ta nuna amincewarta. Daga baya ne ta yanke shawarar sanar da Usaini don yasan me yake faruwa. Bayan ta gama bayanin Yaya Tagwai taja dogon tsaki. "Ina tsammani yarinyar dai da asirinta tazo gidan. Idan ba haka ba waye zai ajiye mace mai ciki a gidansa ba dangin Iya ba na Baba. Ni zanje gidan na same su. Lallai ne su koreta ko don tsare lafiyarsu da ta yaransu. Wa ya sani ma ko mayya ce ko kuma duk abinda ta fada musu karya ne." ABINDA AKE GUDU🙆🏽23 Batul Mamman💖 Hanjin cikin Rashida sai da ya kada da Harira ta gama fada mata dalilin zuwansu. "Bari na kira Baban Abba na fada masa kafin ta karaso gidan nan." Ta dauko wayarta sai dai tayi ta kira Sada bai dauka ba. Harira tace "kema Yaya me zaisa ki amince ku ajiye matar da baku sani ba. Wallahi yanzu duniya babu gaskiya." "Na sani Harira. Sai dai karki manta mu musulmai ne. Idan har zamu biyewa halin mutane yanzu ko sadaka bazamu bayar ba. Kamar yadda Baban Abba ya fada kayi komai saboda Allah. Idan mutum ya cutar da kai yayiwa kansa kuma dama faruwar hakan rubutaccen al'amari ne. Asmau bata da matsala ko kadan,sai kin zauna da ita zaki gane hakan". Suna hirar Asmau su Abba suka dawo daga makarantar boko. Dama jira tayi su dawo ta basu mukulli ta tafi gidan bikin da su Baaba Ta Annabi zasu je. Yanzu dole ta hakura tunda Yaya Tagwai ta zo gari. Sai biyar da rabi Yaya Tagwai ta iso gidan tun daga bakin kofa take fada. Rashida tayi tsuru tsuru da ita har ta shigo ciki. Gaisuwar ta ma bata amsa ba sai fadan rashin hankalinsu da ta gani sun ajiye matar da basu san asalinta ba. Tana wannan fadan Asmau ta shigo a gajiye tana jan kafa saboda tsufan cikinta. Sallama tayi ta shigo ganin baki ta durkusa da kyar ta gaishe da Yaya Tagwai. Kamar gaske ta saki fuska "maraba da tsintacciyar mage. Babu kunya kike yawo da cikin shege a cikin gari." Asmau tayi shiru tana kallon Rashida wadda kunya duk ta lullubeta. Rasa abin cewa tayi ita kuwa Yaya Tagwai ta cigaba da magana "Rashida yanzu wannan mai kwalakwalan idanun kika ajiye a gidanki da sunan taimako. Kina kallon yadda jikinta ya mulmule babu mai cewa daga gidansu ta gudo." "Yaya Tagwai don Allah kiyi hakuri. Idan kika ji labarin yarinyar nan sai kin tausaya mata. Kaddara ce ta afka mata. Adduarmu Allah Ya kare 'ya'yan musulmi daga fadawa makamancin halin da ta tsinci kanta a dalilin sharrin waya." Hannu Yaya Tagwai ta kai zata doke Rashida "yi min shiru shashasha. Sai iya bayani rai-rai-rai kamar wata zabiya. Zabgegiyar mace kamar wannan kika sani ko barauniya ce, ko kuma rufeki Sada yayi cikin ma nasa ne". Kukan da Asmau take yi ta tsayar ta dago kai da sauri tana kallon Yaya Tagwai. "Wallahi duk abinda na fada ba karya nayi ba. Kuma ban taba ganin Kawu Sada ba sai a garin nan da ya taimake ni. Kiyi hakuri don Allah idan zuwana ya bata miki rai". Rashida ma hawaye take yi tace "na yarda dake Asmau nasan amana ce a tsakaninmu. Yaya Tagwai don Allah kiyi hakuri. Da zarar ta haihu zamu mayar da ita gaban iyayenta". Ta juya wurin Asmau da take ta zubar da hawaye. "Tashi ki koma dakinki. Bani mukullin Kemis din nasan ya kusa dawowa ya karba." Su biyun Yaya Tagwai ta ke bi da kallo cike da mamaki." Mukullin wane kemis din ne?" Rashida tayi shiru ita kuma Asmau ta tashi ta tafi dakinta. "Nace mukullin wane kemis din ne?" Rai a bace Rashida tayi mata bayanin tsarin da suke yi na zaman kemis da Sada. Hannuwa ta shiga tafawa tana salati. "Aahaf, ni nasan ba a banza ta barku ba. Yanzu hanyar samun naku ma tare kuke yin komai da ita. To na rantse sai ta bar gidan nan ko kunki ko kunso. Bazan koma Misau ba sai naga abinda ya turewa buzu nadi." Asmau tana daki tana jin fadan Yaya Tagwai da muryar Rashida da Harira suna bata hakuri. Kuka take yi sosai tana cike da fargabar abinda zai faru a gaba. Har kusan magariba Sada bai dawo ba. Dole Yaya Tagwai ta tashi ta koma gidan kanwarta saboda idan duhu yayi sosai ba gani take da kyau ba. Gidan shiru har Sada ya dawo Rashida ta fada masa abinda ke faruwa. Ko zama baiyi ba ya wuce gidansu sai dai shima babu sa'a. Fada yasha sannan tace ya tashi ya bata wuri. Haka suka kwana gidan kamar babu mutane. Asmau tasha kuka ga wani ciwon kai da ya kama ta. Da safe Sada ya kirata suka kara kwantar mata da hankali yace zasu je gidan su sake bata hakuri. Har Kawu Usaini sun kira yace yana hanya zai zo a taru a bata baki. Batun zuwa kemis kuwa ranar babu ita. Adaidaita sahun ya karbo bayan yaran sun tafi makaranta sannan suka fita shi da Rashida da Harira da ta kwana a gidan. Ba suyi minti biyar da fita ba Yaya Tagwai ta shigo tare da kanin Sada mai suna Habu. Asmau na daki taji sallamarta. A tsorace ta fito ta bude mata

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});