Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 42

Chapter 42

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tayi tana magana a dan tsorace "A wane dalili zaka yi bincike a kaina? Daga taimako, dole ne na bada number?" Yadda ya kalleta yasa tayi shiru. Wayarta ya dauka daga kusa da Amatullah ya kunna sannan ya saka numbarsa ya kira tasa wayar. Mayar da wayar yayi inda take ya kama hanyar fita "saura kuma kiyi tunanin cire sim din. Na bar sojoji biyu zasuyi min gadin 'yata don kada ki gudu cikin dare". Gabanta sai da ya fadi da ya fadi haka. Ji tayi kamar yana karanta abinda ke ranta. Ba'a fi minti biyar da fitarsa ba taji wayarta na kara. Da sauri ta dauko a tunaninta Zulaiha ce sai ta sake jin muryarsa. "Baban Safina ne, Colonel Ishaq Muhammad Jikamshi. Na bugo ne don na tabbatar baki cire sim din ba." Bai jira tayi magana ba ya kashe wayar yaja motarsa yayi gaba. Asmau ta tsaya tana kallon wayar cike da mamaki. Tsoro ne ya kamata don da gaske ta yarda ya bar masu tsaronta kada ta fita su bindigeta a banza. A hankali ta sake maimaita sunan nasa. Dama a jikin rigarsa ta ga inda aka rubuta I.M Jikamshi. ABINDA AKE GUDU🙆🏽30 Batul Mamman💖 Sau biyu Asmau na leka waje amma bata ga soja ko daya ba. Ga tsoro kada sai ta fita su tsareta. Haka nan ta hakura zata zauna don dole. Dadin dadawa tana so Amatullah ta kara samun sauki. Sallah tayi ta ci abinci itama sannan ta saka kati daya a wayar ta kira Zulaiha ta fada mata inda suke. Sauran ukun kamata yayi ta sayar dasu ta fada a ranta. **** Col. Ishaq gidansa ya wuce dake Tudun yola. Gidan da a yanzu baya son zama cikinsa saboda abubuwa da dama da yake tuna masa dasu. Dakinsa ya shiga ya dauko wasu takardu ya jira akayi har sallar isha sannan ya tafi gidan Hajiyarsa. Babu kowa a falon lokacin da ya shiga shiyasa ya wuce dakin kaninsa wanda yayi aure kwanakin baya inda yanzu ya mayar nasa. Yayi wanka ya saka kananan kaya sannan ya hau gado ya kwanta. Tunanin Amatullah yake yi yana dan murmushi. Yarinyar ta tsaya masa a rai. Sai kuma ya koma tunanin mamanta. Ji yayi yana son sanin ko ita wace ce. Tunani kala kala ya rinka yi game da ita. Da ya gaji wayarsa ya dauko yana karanta sakonnin da aka turo masa wasu ya share wasu ya bada amsa. Sunan da baiyi tunanin gani bane ya dauki hankalinsa da sauri ya bude sakon. Sallama tayi masa sai hoton baby da ya biyo baya. A kasan hoton ta rubuta _Alhamdulillah mun sami baby boy_. Da kyar Ishaq ya iya hadiyar yawu don tashin hankalin da ya tsinci kansa a ciki. Har wani guntun zazzabi ne ya nemi rufe shi. Ya tashi ya fita zai je wurin Hajiya a daki sai yaji muryarta a falo. Labarai take kallo ita kuma Bilkisu tana zaune a kasa suna hirar sanyin Jos da mai aikin gidan Hinde. Motsinsa yasa Hajiya kallon kofa tace "yaushe ka shigo gidan ban sani ba?" "Dazu ne bayan Isha" Ya zauna akan kujerar kusa da ita tare da mika mata wayar. "Kin gani Badar ta haihu" Hajiya ta kalli su Bilkisu "ku dan bamu wuri" Tashi suka yi Bilkisu sai da ta waiwayo ta kalli Kawunta tana mai tausaya masa. Bayan sun wuce Hajiya ta karbi wayar ta kalli hoton jaririn tayi guntun murmushi "Allah Ya raya" ta gyara zama sosai tana fuskance shi "Mai sunan Alhaji, nasan irin damuwar da kake ciki amma ina so ka sani ba'a yiwa Allah dole. Duk yadda kaso Allah bai nufa zaku kare rayuwarku da Badariyya ba. Duk kuma yadda kuka nemi haihuwa kasan wani baya haifar dan wani." Kansa a kasa yace "na sani Hajiya. Yanzu na tabbatar mun rabu har abada kuma kamar yadda Mami take yawan fada ya tabbata nine bana haihuwa" a yadda yake ji a wannan lokacin gara yayi kuka ko zaiji sauki a ransa. Tausayi ya bata sosai. "A matsayinka na musulmi ka sani cewa babu abinda bawa zai samu a rayuwarsa sai wanda Allah Ya kaddara masa. A bisa tsari da hikimarSa *Yake azurta wasu da 'ya'ya mata, wasu da 'ya'ya maza, wasu Ya hada musu duka biyun, wasu kuma Ya barsu haka* duk inda Allah Ya jarabceka da fadawa kasan babu wayo ko dabararka. Ka zama mai hakuri wata rana zaka ci ribarsa". Ajiyar zuciya yayi ya gamsu da bayananta wanda ya sani dama. "Nagode Hajiya, bari naje na kwanta" "Abinci fa" "Bana jin yunwa. Sai da safe" Tasan halin da zai shiga kenan shiyasa tun tana Jos shekaranjiya da maman Badariyya tayi mata waya ta sanar da ita haihuwar bata fada masa ba. ***** Sake kwanciya yayi yana tuno rayuwarsa ta baya. Auren soyayya suka yi da Badariyya suna zamansu lafiya. Har suka shekara biyu da aure ko batan wata bata taba yi ba. Gashi Allah Yayi shi da son haihuwa tun bata fara damuwa ba ya matsa su je asibiti. An duba su aka tabbatar musu duk lafiyarsu kalau su jira lokaci. A haka har suka yi shekara shida babu labari. Maman Badariyya duk ta damu. Magunguna har da na gargajiya kawo musu take yi amma shiru. Ishaq ya tayar da hankalinsa sosai gashi ko ina suka je sai ace babu matsala. A wani asibitin Jiddah ne ma aka ce kwan haihuwarsa bashi da karfi. Ya shiga damuwa sosai sai gashi Badariyya ke bashi baki. Sun sami shekara goma da aure Mamanta taje har gidan Hajiya ta roketa arzikin asa Ishaq ya saketa tunda anfi tunanin matsalar daga gareshi. Hajiya Lubabatu tayi ta rokonta akan tayi hakuri sai tace to nan da wata shida idan ba'a saki canji ba dole ya saketa. A wannan wata shidan Ishaq yaje asibitoci sunkai takwas. Magani kuwa duk wanda aka bashi sha yake yi. Lokaci na cika har gida Mami tazo ta bukaci ya saki 'yarta. Badariyya kanta tace ko waye da matsalar a cikinsu zasu hakura tunda suna son juna. Mami ta dage abu har kunnen manya a danginsu duka. Ganin al'amarin yana neman lalacewa dole ya yi mata saki daya suka rabu ba don suna so ba. Tana gama iddah da wata biyu yaji labarin aurenta, gashi yanzu har ta haihu ko shekara bata cika ba. Ya amince bashi da rabon ganin dansa. Kannensa duka sun haihu hatta autansu matarsa ciki gareta. A haka bacci ya dauke shi zuciyarsa cunkushe da tunani. ***** Da safe likita yazo ya duba Amatullah yace jikin da sauki amma zasu barta sai gobe a sallamesu. Asmau masa tayi godiya sannan ta tashi tayi wanka ta gogewa Amatullah jiki ta canja mata kaya. "Ama zan fita na siyo miki abinci kinji. Duk wanda ya shigo ki ce masa ina bandaki" "Ummi kayya ko, ashe kema kina yi kika ce na dena" Kafin ta iya bata amsa taji tace "yeeey Babana ya dawo" Asmau ta dago kai a kunyace. Karshenta yaji abinda Amatullah ta ce. Yau ma kayan sojan ne a jikinsa sai dai babu fara'a kamar jiya. Duk da haka yayi kyau ga cika ido. Gaishe shi tayi ya wuce bai amsa ba. Wani mutum ne ya shigo da kwandon abinci ya gaisheta ya ajiye

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});