Chapter 24
Chapter 24
sosai. Allah Ya sauwake. Bari na soya kosan sai kici kiyi wanka." Jikinta a sanyaye ta fita ta koma daki tayi wanka. Zuciyarta ta gama raunana amma cigaba da kukan bazai amfaneta da komai ba sai tonon silili. Umma kuwa sai tattalinta take yi har daki ta kai mata abinci tana ta sannu. Wannan ya kara sawa taji ta tsani kanta. Ji yadda mahaifiyarta ke kula da ita bayan ciwon nata baya bukatar tausayawa daga kowa. Sunje asbiti tasha allurai saboda zazzabi sannan aka bata magunguna. Da suka koma gida Umma ta sanar da ita Abubakar yazo amma ya wuce Kaduna ana nemansa akan wasu takardu da ya kulle a office. Kai kawai Asmau ta gyada ba don ta yarda ba. Daga dawowarsu zuwa wayewar gari tayi masa text yafi goma banda waya da ba'a kirgawa. Gani take yi kawai zai gujeta ne kamar yadda take yawan jin labarai na samari da suke yaudarar 'yan matansu. ***** Kafin azahar Abubakar ya isa Kaduna. Jiya ko kadan bai runtsa ba sau tunani da ya addabi zuciyarsa. Ji yayi Kanon tayi masa zafi shiyasa ya dawo saboda baya son yawan tambaya akan me yake damunsa. Kwanansa biyu da dawowa baya zuwa ko ina daga office sai gida sai ko masallacin unguwar da yake. Rabonsa da abincin kirki ma ya manta. Yana kwance ya kurawa fanka dake juyawa ido wayarsa tayi kara. Sunan Qasim ya gani shiyasa ya dauka. Qasim ya sanar dashi wani aiki zai kawo shi garin yanzu zai kamo hanya. Addua Abubakar yayi masa sannan ya dan gyara dakin da ko shara baya samu. Tun zuwan Qasim ya kula da canjawar da abokinsa yayi. Yayi tambayar har ya gaji babu amsa. To me zai fada masa? A nata bangaren Asmau ji take yi kamar tayi hauka. Tayi wayar har ta gaji. Hawayenta ma ya kafe jira take kawai azo ace Abubakar ya fasa. ***** Ranar juma'a da safe Abubakar ya gama shirin tafiya office Qasim yace "Karfe nawa zamu tafi Kanon?" "Wannan satin bazan je ba ayyuka sunyi min yawa" Abubakar ya bashi amsa. Kayan da yake sawa a 'yar jakarsa ya ture ya koma kallonsa "Abubakar nayi nayi ka fada min abinda ke damunka kaki na rasa dalili. Ni mai sonka ne da alkhairi idan ka fada min ko addua sai na tayaka". Kwalla yaji ta cika masa ido ya dan dake "na fada maka babu komai bari naje na dawo mu tafi. Shikenan ko". Qasim dai bai gamsu ba. Yana nan zaune aka kawo wuta ya saka wani CD na wa'azi da ya gani a kusa da tv din dakin. Ko minti goma ba'ayi da farawa ba Abubakar ya shigo lokacin shabiyu saura. Zamansa ke da wuya aka yiwa malamin dake wa'azin tambaya akan ZINA. Malamin yace "Lallai zina tana daga cikin manyan kaba'ira da Allah SWT Yayi hani dasu. Ban da lalacewar zamani yanzu da muka dauketa ba a bakin komai ba zaka ga yawanci duk addinin duniya yayi hani da zina saboda muninta da kazantar dake cikinta. A cikin suratul Furqan ayoyi na 69 zuwa 71 Allah Yana cewa *WADANDA BASA DAUKAN WANI BAYAN ALLAH A MATSAYIN UBANGIJI KUMA BASA KASHE RAI BA BISA SHARI'AH BA, KUMA BASA ZINA WANDA DUK YA AIKATA HAKA ZAI SAMI ZUNUBI DAIDAI AKIN DA YAYI*. *ZA'A NINKA MASA AZABAR RANAR ALKIYAMA KUMA ZAI KASANCE A CIKINTA HAR ABADA*. *SAI WANDA YA TUBA KUMA YAYI IMANI KUMA YA AIKATA AIKI MAI KYAU, WADANNAN SUNE ALLAH YAKE CANZA MUSU ZUNUBANSU ZUWA GA LADA. ALLAH MAI RAHMA NE MAI JINKAI* Abin duba a nan shine an lissafa zina da ayyuka masu matukar muni wato shirka da kisan rai ba tare da hakki na shariah ba" Haka malamin ya cigaba da janyo ayoyin AlQurani da hadisan Annabi SAW wadanda suka yi hani da zina ko azabar dake jiran masu yinta. Ya kawo aya ta 32 a cikin Sural Isra' wadda Allah Madaukakin Sarki Ya umarce wadanda suka yi imani da kada su kusanci zina. Sai aya ta 2 a cikin suratun Nur wadda Allah SWT Yake cewa: *MAZINACIYA DA MAZINACI IDAN SUKA YI ZINA KU BULALI KOWANE DAYA DAGA CIKINSU BULALA DARI. KADA KUWA WANI TAUSAYI YA KAMAKU GAME DA TABBATAR DA HUKUNCIN ADDININ ALLAH IDAN KUN KASANCE KUN BADA GASKIYA GA ALLAH DA RANAR LAHIRA. KUMA LALLAI NE WATA TAWAGA DAGA MUMINAI SU HALARCI WURIN YI MUSU HADDIN* Abubakar da Qasim duk hankalinsu yana ga bayanin wannan malami. Duk su biyun jikinsu yayi sanyi musamman Abubakar da yasan abinda ya aika. Malam mai wa'azi cikin bayaninsa ya kawo hadisin Bukhari wanda Annabi SAW yake cewa _MAZINACI BA SHI DA IMANI A LOKACIN DA YAKE AIKATA ZINA...._ Da wani hadisin na Abdullahi ibn Mas'ud wanda yake cewa _MUN KASANCE TARE DA ANNABI SAW MATASA MARASA KOMAI NA DUKIYA_. _SAI ANNABI SAW YACE DAMU_: _YA KU SAMARI, WANDA YA SAMI IKO A CIKINKU YAYI AURE DOMIN YAFI AKAN KARE KALLO DA MUTUMCI. WANDA BAZAI IYA BA SAI YAYI AZUMI SABODA ZAI ZAME MASA KARIYA._ Kallon kallo ne ya koma tsakanin Abubukar da Qasim a lokacin da malamin ya soma bayanin lahira da tanadin da Allah SWT Yayiwa bayi masu biyayya da masu sa6o. Ya karanto ayoyin Suratul Haaqqa wurin da Allah SWT Yake fadan irin farincikin da masu aikata aiki nagari zasu shiga idan sun karbi littafinsu da hannun dama da tanadi mafi kyau da Yayi musu a aljannah. Da kuma tashin hankalin ma'abota sabawa Allah a lokacin da suka karbi nasu littafin da hannun hagu(Ya Allah Kasa bama cikinsu. Amin) da azabar da zasu tarar. Duk da Qasim ya shiga tashin hankali da jin wadannan bayanai saboda abinda yake aikatawa na shafa jikin 'yan matansa saboda gusar da sha'awa, yayi matukar mamaki ganin Abubakar ya fashe da kuka. Dafa abokin nasa yayi yana cewa "Ba kaine zaka yi kuka ba Abubakar. Ni ne ya kamata nayi kuka saboda nasan na sabawa Allah sosai. Irin wannan abin da na fada maka akalla nayi da mata wurin biyar." Abubakar ya kalle shi hawaye na kwararo masa." Qasim nawa sabon yafi naka. Na cuci kaina na aikata zunubin da bana hangowa kaina komai sai azaba." A tsorace Qasim ya dago kan Abubakar dake kallon kasa" ban fahimceka ba, kada dai kace maganarmu ta rannan tasa kaima kaje kayi romancing wasu. Na shiga uku, ai ni ne cikin matsala tunda duk wanda yayi umarni da mummunan aiki yana da zunubi kwatankwacin na wanda ya aikata kamar yadda yake ga mai umarni da kyakkyawa". Dafe kansa kawai yayi yana tunanin wannan sabon tashin hankali da ya saka kansa a ciki. Zuciyar Abubakar cike da danasani yace "Qasim zina nayi" "What??? Abubakar garin yaya? Da wa?" Sai da ya hadiyi yawu da kyar ya iya amsawa "Asmau". Qasim yana girgiza kai yana karanto La haula... "Marainiyar yarinya, wayyo Abubakar ni ne sila ko? Tun yaushe ne? Garin yaya ka aikata hakan kai da ka kusa aure? Idan aka gane fa? Ga mahaifiyarta mutuniyar kirki." Tambayoyin da Qasim keyi shima Abubakar din sune suke masa yawo a kansa. Yana hawaye ya sanar da Qasim abinda ya faru da irin kunya da bakincikin da ya sami kansa a ciki. "Yanzu shikenan nima da hannun hagu zan karbi littafi na ranar lahira. Lallai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103