Chapter 51
Chapter 51
sirri mafi muni a rayuwarta shine yake fada mata kalaman so har yake batun aure. Dole taji sonsa yana kara shigarta sai dai kuma bata manta alkawarin da tayiwa kanta ba. Duk irin son da take yiwa Jikamshi bazata iya aurensa ko waninsa ba. Tana kuka tace "Nagode Jikamshi, kaine mutum na farko da ya fara sona da gaskiya tun bayan kaddarar da ta sameni. Ka kyautata min kuma ka kyautatawa Amatullah. Allah Ya saka maka da alkhairi. Amma kayi hakuri da maganar aure. Kasan komai game da rayuwata me zai sa ka...." Bai nuna damuwa ba ba fuskarsa sai ma murmushi da yake yi mata a yayin da take zubar da hawaye. "Asmau, Asma'u na. Kina ganin idan nace na janye zaki ji dadi?" Sai da taji faduwar gaba sannan ta gyada masa kai. "Hmmm kamar gaske. Ina so kisan cewa bazan taba janyewa ba. Ni ba karamin yaro bane. At the age of 42 nasan meye so ko kishiyarsa. Kuma a naki idon so nake gani....infact kamar ki hadiye ni" "Lahhhhh" ta iya fada hawaye na sintiri a idonta. Wallahi tana son Col I.M Jikamshi amma dole ta hakura indai ba so take ta daukarwa kanta dala ba gammo ba. Tana da yakinin ko Hajiyarsa bazata lamunce danta ya aureta ba. "Rufe bakin mana" Ta kuwa hade bakinta kamar yadda yace. Dan kara matsowa yayi amma da sauran tazara a tsakaninsu. "Kafin haduwarmu na ajiye batun aure a gefe tun bayan rabuwarmu da matata ta shekara kusan shadaya. Yanzu da na hadu dake sai nake jin rayuwata bazata kara min dadi ba idan babu ku. Ki manta da komai na bacin rai ki rungumi mai sonki. Ni fa nake nufi" Murmushi ne yazo mata babu shiri. Sannan tace "Kasan dalilina na gudun aure. Gori nake gudu ko a ni ko Amatullah. Sannan kaima duk inda kaje za'a nuna ka" Hamma yayi alamun baya son maganar "duk kin tsareni da zance kin hanani na tafi na kwanta." "Maganar fa tana da mahimmanci" "Bacci na ma yana da mahimmanci. Ina fatan haduwa da Asmau ne muyi hirar arziki batare da tayi min kuka ba." Jikinta ya kula yayi sanyi. Duk abinda take gudu ya riga ya hangosu amma ko da aure ko babu abinda ya faru ya riga ya faru a baya. Wucewarsa sai a hankali idan Allah Yaso. Indai ya sami amincewar Hajiya wanda baya tunanin zata ki to duk abinda mutane zasu fada sun dade basu fada ba. "Zan baki lokaci daga nan har ki gama zamanki. Yassar ya fada min zaku je Niger so duk zan baki damar yin tunani kiji ko zaki iya zama batare da kina ganina ba. Ranar da kika dawo a ranar zanzo naji amsarki. Kada kiyi tunanin gujemin Asmau." Kanta a kasa har ya shiga mota yana tausaya mata. Ba don kaddara ba ace tana son abu amma wani kuskure da ya riga ya wuce yasa tana gudunsa. Bata dago kanta ba har ya saita motar zai tafi sannan suka hada ido. A hankali ta karanta lebensa ta gane abinda ya fada wanda ba'a ji sai motsin bakinsa kawai. _Love you_ ****** Bayan tafiyarsa gida ta shiga tana ta juyayin zancensa. Dakin Anti Bintu ta nufa tayi sa'a bata dade da fitowa daga wanka ba. Cike da damuwa ta zayyana mata yadda suka yi da Jikamshi. "Ko baki fada ba Asmau idanuwanmu sun gane mana. Ki godewa Allah da Ya dubeki da rahma Ya kawo miki mai share miki hawaye" "Anti ba kya ganin rashin dacewarmu. Karshenta danginsa bazasu amince ba. Kuma ina tsoron wulakanci da gori nan gaba duk da ni na janyowa kaina." Ta fashe da kuka "Haba Asmau. Har yaushe za'ayi ta maimaita abu daya. To bari kiji in fada miki. Indai bakiyi aure ba wallahi sa ido sai yafi a kanki. Ko takalmi kika canza sai an sami masu yi miki muguwar fassara. Gara kiyi aure ki samu garkuwa da rufin asirin da kowace mace take nema." Tasan gaskiya ake fada mata amma gaba take ji. Ranar da miji zai goranta mata. Ranar da zai nuna mata alfarma yayi mata da ya aureta. Anti Bintu tana ta nuna mata ta karbi kyautar Allah hannu bibbiyu ta fada mata yadda suka yi da Qasim. "Ikon Allah, wannan yanke shawara ba zai yiwu da gaggawa ba. Duk mun shaida irin neman da Qasim ya rinka yi miki. Amma banyi zaton abin zai kare a soyayya ba. Ga kuma Ishaq da kuka hadu lokaci guda ya kamu da sonki da na Amatulllah. Kuma kema nasan shi din kike so. Ki bari ku koma Kano nima sai nazo ayi magana da su Hajjo da Yaya Abu. A yanzu dai ki dage da neman zabin Allah. Amma ki sani aure shine gatanki. Kada na kara jin kince bazaki yi ba" ***** Sati dayan da suka yi sunji dadin zaman garin idan ka cire maman kawu Yusuf. Soyayyar Jikamshi kuwa kullum karuwa takeyi a ranta. Duk da basa waya don yace zai bata lokaci tayi tunani batare da ya dagula mata lissafi ba. Ga Qasim kullum yana waya amma baya mata zancen soyayya. Shima yace sai ta dawo zasuyi shawara. Al'amura duk sun cakude mata. Ranar da suka cika sati Umma, Yassar da Jafar suka iso harda Sabira. Mota biyu suka yi. A ranar suka wuce Wushishi. 'Yan uwa da abokan arziki sunyi musu tarba mai kyau. A gidan Kawun su Umma aka yi musu masauki. Mutane suna ta zuwa ganin Asmau da 'yarta. Kowa da abinda zai fada. Wasu su fadi mai dadi wasu kuma sai dai a kawar da kai idan sunyi magana. A nan ma sati guda sukayi suna zaga dangi sannan suka kamo hanyar Kano. Tun a hanya Qasim ya sanar da ita zai zo washegari da daddare idan sun huta saboda jin amsarta. To kawai tace tana tunanin abinda zata fada masa. Gashi Umma tace sai sun dawo Kano zasuyi maganar sosai don duk su biyun babu na yarwa amma dai zukatansu sunfi karkata ga Qasim da suka sani tuntuni. ***** Kamar yadda yayi alkawari a gidan Isha tayi masa ma. Bayan sun gaisa da Umma suka fito waje da Asmau suka zauna kan wasu kujeru daga gefe. Bayan fitarsu Col. Ishaq ya rinka kiran wayarta. Yasan jiya tace zasu dawo saboda haka lokacin jin amsarta yayi. Da yaji shiru saboda tun kafin magariba ta jona chaji ta barta a daki sai kawai ya shirya ya taho. ****** Suna zama Qasim yace "Ya naga kamar kin rame ne? Ko duk rashin hutu ne kuna ta ziyara." "Kai kuma kayi kiba Yaya Qasim kamar ba dansanda ba. Anya zaka iya bin barawo da gudu kuwa yanzu?" Tare suka soma dariya yana kallonta yana jindadi. A daidai wannan lokacin Col. Ishaq ya shigo gidan da motarsa. Bisa rashin sani ya haskosu suna dariya ransa yayi matukar baci saboda kishi. ABINDA AKE GUDU🙆🏽39 Batul Mamman💖 Tsabar bacin rai yasa yayi wani irin cin taya sannan yayi parking din motar. Duk jikinsa tsuma yake yi, zai iya rantsewa bai taba jin kishi makamancin wannan ba duk tsahon rayuwarsa. Asmau ma tuni ta hadiye dariyarta gabanta na faduwa. Duk da bata ganshi ba amma ta gane motar. Sai taji ta tsani kanta da har
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103