Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 82

Chapter 82

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

daurin nata da pin. Takalminta mai tsini da jaka duk kalar mayafin ne. Ango ma shaddarsa irin mayafin nata ce amma fa ba mai kyalli ba. Ga hula har wani dan karkacewa tayi. Asmau tana gama fitowa aka fara daukar hotuna kamar me. Safiyya da Shemau ne masu tsari suka jera su MC din taro S.Kilishi ita ce ta sanar da shigowar ango da amarya. Suka taho suna taku daidai. Wuri ya kaure da sowa. _Qamshi qamshi yana tashi, 'yan mata zamu kamun amarya_ _Yaune muke shirin kamu...amarya_ _Asmau amarya zo gamu...amarya_ _Ki hakuri da zancenmu, kinsan aure yana kanmu_ Kafin mai wakar ta karaso gaban ango da amarya tuni 'yan mata sun fito ana ta rausayawa. Jajimaji kenan, idan ta bude baki ko Sangandali sai dai taja baya. Haka ta cigaba da waka har amarya da ango suka zauna. Bayan Hajiya YBK ta bude taro da addua aka shiga biki da gaske. Su Bilkisu da tawagar gidan Hajiya Lubabatu da 'yan Jikamshi ankonsu iri daya ne da nasu Ainau. Ga su Amatullah yau anyi kwalliya itama ta fito sosai. Yaran su Shemau da nasu Sadiya 'yan uwan Abubakar kowa fa yayi kyau. An bukaci dangin ango su fito fesawa amarya turare sai gasu mata biyar ne harda Mami kowacce da tsadadden turare a hannunta suka zo a rinka fesawa. Biki yayi biki mata sun sha rawa. A cikin taron mata 'yan taya ango da amarya murna sun gwangwaje. Saboda yawansu ba sunan kowa zaka iya kamawa ba. Akwai su Maman Afrah, Tash, Jatma, Zahida, Mrs G, Sadiya Jegal, Ibtihal, Shukriya, Ummu Rauda, Maman Sadiq, Ummu Aslam, Mrs Ambursa, Hauwa Ag, Mum Little, Farha, Jammu, Mardiya, Shafa, Ruqayya, Tafeesu, Ummi BK, Didi, Mjay, Zahra BB, Biebie Isah, Temseey, Khadija Candy.....(wai abin da yawa ni mai rubutu naji hannuna zai tsinke nace wallahi sauran ma duk ina sonku har raina). Taro kam ya kayatar. Anci an sha an kuma rausaya. Ana cikin daukar hotuna ne Mama Yalwa tazo zasu dauka ita da Asmau da ango. Suna hada ido da Asmau suka tuna abu daya suka fara kuka lokaci guda. Duk wanda yasan wadannan matan yasan kukan me suke yi. Allah Ya jikan Abubakar, mutuwarsa ce tasa har aka zo rana irin wannan. Suna yi ana tayasu har su Umma. Suwaiba karamar kanwarsa ce ta iya daurewa tana basu baki. Col. Ishaq duk kishi irin nasa ya dauke kai a yau. Abubakar wani bangare ne na rayuwar Asmau da bazai gogu ba. Haka aka kare taron kowa ya tafi gida cikin farinciki da annashuwa. 'Yan gulma basu sami abin fada ba sai san barka domin taro ya burge kowa. ***** Washegari sai shabiyun rana zaa daura aure. Asmau tun dare ta kasa baccin kirki. Yaushe zata manta ranar aurenta na farko da ango ya rasu. Ji tayi gabadaya bata da kuzari har gari ya waye. Col. Ishaq kuwa jin kansa yake kamar anyi masa wani albishir mai kyau. Farar shadda ya saka harda babbar riga. Anyi mata aiki da zare ruwan goro saboda haka hularsa da takalmi harda agogon hannunsa ruwan goron ne. Masallacin Hotoro ya dauki jama'a wadanda suke son shaida wannan babbar rana. Su Jafar da Yassar suna kan gaba, ga Kawu Garzali da wani abin mamaki Kawu Rabe yazo yana ta ra6e ra6e. Bisa amincewar Hajjo da sauran 'yan uwansu Alh Adamu Matawalle shine waliyin amarya. ASP Qasim ma gayya guda yazo da ita daga abokan aiki zuwa makusantansa a Shanono. Ga su Sada suma ba'a barsu a baya ba. Ango sai faraa yake yana gaisawa da jama'a. Har hoto suka yi da Qasim suka gaisa a mutunce. Shabiyu nayi Liman ya bukaci wakilin angon da waliyin amarya. An daura auren Col. Ishaq Muhammad Jikamshi da Asmau Shu'aib Yahya akan sadaki dubu sittin. ***** Asmau na zaune kowa yayi wanka ana ta shirin tafiya gidan Umma inda zasu zauna saboda baki masu son ganin amarya. Tamkar wadda aka zarewa laka haka take jin jikinta. Ga faduwar gaba da ta kwana dashi. Tana kwance text ya shigo wayarta ta dauka a firgice. Kalma daya ta gani daga Jikamshi wadda ta saka ta kuka sosai. *Alhamdulillah.* Su Sabira suka zuba mata ido har dakin ya fara cika da su Ainau da Zulaiha suna ta tambayarta me aka yi mata. Shemau rai a bace tace "ku kyaleta tayi kukan nan. Tun daren jiya take neman yinsa. Ni nayi mamaki ma da kika jira sai yanzu. Ace mutum bashi da sana'a sai ta zubar da hawaye." Tana kukan tace "Anti Shemau an daura fa" La'ila ha ilallah....shine abinda Shemau ke fada tana tafa hannuwa. "Amaryar zamani da kanta take sanar da aurenta" Wani hawayen ne ya zubowa Asmau bata ji haushin yayarta ba tace "na zata shima mutuwa zaiyi, tun jiya gabana ke faduwa" Jikin Shemau yayi sanyi bata san abinda ke ran kanwarta ta ba kenan taje ta rungumeta. Ainau ma ta matso ta rungumeta suka soma kuka. Sabira da Zulaiha aka bari da rarrashinsu. Sai da suka saka Asmau yin nafila godewa Allah sannan tayi wanka ta shirya suka tafi. Shigarsu gidan ke da wuya Yassar ya shigo yace ga ango a waje zasu dauki hoto da amarya. Umma tana cikin mutane ta girgiza kai tana murmushi. Wannan ango bashi da dama. Bare an daura aure ai shikenan kuma. Dakin da suke zaune da su Rashida Mimi taje ta kirawota. Yawanci sallah masu rakata sukeyi sai ta nemi takwararta Ma'u ta rakata. Mayafi tasa ta rufe fuska haka suka fito. Ashe tawaga guda ce domin harda su Jafar da Qasim. Ita dai duk kunya ta isheta haka akayi hotunan ta kasa sakewa. Shima bai matsa mata ba. Ko don idon mutane ya raga mata. Qasim tun fitowarsu idanunsa suka fada kan Ma'u. Yarinya ce kyakkyawa suna kama da Zulaiha sosai. Itama ta kula da kallon da yake mata sai ta sunkuyar da kanta cike da kunya. A take yaji wani abu a ransa game da ita. Sun gaisa da Asmau zata shiga ciki ya kalli Col. Ishaq. "Ango don Allah a bani dama zan roki amarya alfarma. Ta dan daga kai suka hada ido da Jikamshi yace "bari na matsa ga mutane can zamu gaisa. Idan kun gama sai kuyi mana jagora mu dauka dasu Hajjo" "Godiya nake yallabai, idan tarkona ya kama zan fada maka don kune masu nema" Col. Ishaq na matsawa Qasim ya tambayi Asmau game da Ma'u. Tayi murna sosai ta masa bayani game da ita harda bashi numbar waya. Tana tafiya wurinta ta fada mata. Ma'u tayi murmushi kawai. Asmau tace alamun nasara kenan. Har cikin falo aka shigo da angwaye aka dauki hotuna da iyaye da kakanni sannan suka tafi. ***** Bayan magariba aka shirya tafiya Meena event centre inda za'ayi Sword Crossing. Wasu sun saba yi ido na ganin ido amma wannan karon tsarin na dare ne. Fili suka kama ba hall ba saboda shi zai dace da irin abinda suka shirya. Kayan Asmau na yau har sunfi na jiya. Wannan ango da kansa ya aiko mata dashi dinki kawai ta kai. Material ne light green sosai. Riga da siket aka yi mata. A bisa umarnin ango ita da Amatullah suka dinka kayan. Wani irin dauri Najah mai kwalliya tayi mata da sauran material

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});