Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 45

Chapter 45

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

har ta bukaci lallai ta dawo gidannan dasu Aina'u idan har ta yafe mata. Shi kuma tace ya soma gyara musu gidan kofar mazugal su koma. A nan aka ji ashe ya dade da siyar da gidan. Ya kuma dage wannan nasa ne. Sai ga ainihin takardun gida Hajjo ta fito dasu, ke magana har za'a shiga kotu don duk su Kawu Garzali sun ce sai ya biyasu kudin gidansu da ya sayar. Wurin aikinsu ma suka kore shi yaci kudin kamfani bai biya ba. Sai da yaga abu ya kure masa ya roki gafarar Umma suka tashi. Yanzu haka yana kauyen Dakasoye can ainihin kauyen babansu Anti Sagira. A nan baban nata ya bashi gona da gida suka zauna tunda bashi da wurin zama. Yanzu da wuya yazo cikin Kano. Zahra dai tayi aure tana Jigawa" Asmau tace "har ya bani tausayi. Da ma Umma ta barshu kawai a nan din" Aina'u tace "tabdi, ko yanzu fa ba wani rissina yayi ba. Tsoron hukuma yaji don da gaske su Yaya Abu sunso a kama shi sai ya biyasu kudin shiyasa ya bada hakuri ya tattara yayi gaba" "To Allah Ya kyauta" duk suka ce Amin. Kan katon gadon Umma suka kwanta su uku sannan aka shimfide yaran akan bargunan banda baby Asmau wadda suke kira Husna. Sai wurin daya da rabi na dare Umma ta baro dakin Hajjo inda su Anti Lami suke. Su ma sum gama tasu hirar. Wani hawaye taji yazo mata da taga 'ya'yanta mata kwance su uku a wuri daya sun takure alamun daya gefen nata ne. Kasa kuma ga yaransu duk sunyi bacci. Maimakon ta kwanta alwala ta dauro tazo tayi sallah tana mai mika godiyarta ga Allah tare da adduar dadin shiriya ga zuri'arta da sauran musulmi. ***** Col. Ishaq yana kwance amma ya kasa bacci. Ya rasa abinda yasa yake ta tunanin Asmau. Can kasan zuciyarsa yace tausayinta ne kawai da kuma son Amatullah. Sai dai kuma ko rufe ido yayi murmushin da tayi bayan komawarta gida yake tunawa sai kawai ya tsinci kansa da yin murmushin shima. ***** Washegari karfe takwas na safe sai ga Jafar da Sabira dauke da kwanunkan abinci. Dankali ta suya da plantain da kwai. Duk da tasan dai a gidan ma za'ayi. Umma ta nuna jindadinta sosai. Shiyasa take son Sabira, barta dai da surutu amma mace ce mai ladabi da sanin ya kamata. Sauran matan masu jini a jika irin su Shemau da Rashida suna kitchen ana ta soye soye. Aina'u ma ta tashi duk da hanata aikin komai ita da Zubaida mai ciki. Asmau kuwa kamar wadda aka saukarwa bacci tana yin sallar asuba ta koma. Ji takeyi rabonta da bacci mai dadi cikim kwanciyar hankali har ta manta. Amatullah ce ta tasheta tana kiran Babanta. Cikin bacci Asmau ta janyota jikinta ta soma rarrashi "Ama nan ne gidanmu fa, na rasa inda kika koyi rigima. Amma idan kika cigaba zan mayar dake wurin Zinaru" Shiru tayi ta kwanta a jikin Asmau daga baya tace "Ummi to zaki kaini naga Babana sai mu dawo?" Asmau ta shafa kanta tana murmushi "in sha Allah zan kaiki kinji. Tashi muje muyi brush a gaishe da su Hajjo" Suna fitowa falo suka tarar da kowa a zaune har su Jafar. Rike take da hannun Amatullah sai suka basu sha'awa. Ita kuwa kallon da suke mata yasa taji kunya ta saki hannunta. Yanzu tunda anzi gida sai ta koyi kara kada ace bata da kunya. Suna zama suka gaishe da kowa Anti Bintu ta cikawa kowannensu plate da abinci. Amatullah ta ware ido sai ta tashi taje tayiwa Asmau rada a kunne. Duk ana kallonta sai suka ga tana share hawaye. Hankalinsu ya tashi Umma tace me ya faru. Kunya tasa Asmau ta kasa fada da wayo Umma tace "Safina zo ki fada min abinda kika fadawa Ummi. Kinga gashi har kin sakata kuka" Duk aka zuba mata ido ita kuwa tace "Ummi in fada?" Murmushi kawai Asmau tayi tace "tambayata tayi taci ko kuwa" Amatullah ta cafe "idan naci Ummi zata ce nayi kwadayi. A gidan Babana ma sai tace naci. Mu a gidan Zinayu koko da kosai muke ci, ko byodi da tea, ko tuwon safe ko Ummi" Kasa cin abincin Asmau tayi ta fashe da kuka. Sunga rayuwa ita da Amatullah. Dan kudin da take samu a kudin makaranta yake tafiya. Abinci kuwa sai dai aci garau garau. Su Umma suma kukan suke tayata. Abinda tafi karfi a da shine yanzu yafi karfinta. Anti Bintu tazo ta rungumeta "komai ya wuce Asmau. Kuka bazai dauke shekarun baya ba sai dai ya tuna miki da bacin rai." Hajjo tace "haka ne ki dena kukan haka. Rayuwace kowa da irin tasa duk da dai komai yana da sanadi. Naji dadi da kika koyawa yarinyar nan tarbiya mai kyau." A haka suka ci abincin ana taba 'yar hira har Asmau ta sake. Kafin su tashi Amatullah ta sake cewa "Ummi daga yau a nan zamu zauna ne?" "Eh mana ai kun dawo gida kenan" inji Shemau Tare duk suka tashi aka kwashe kwanukan suka fara layin wanka. Wurin shadayan safe Asmau na saka kaya don kuwa Mama Yalwa tace yau a gidanta zasu yini taji wayarta na ringing. Ko da ta dauka bakuwar number ta gani har tayi zaton ko Zulaiha ce tace "tuba nake maman 'yan biyu ban samu na kiraki ba" Shiru taji daga daya bangaren tace "Zulaiha ko kinyi fushi ne. Ni da ke fa ba'a ji kanmu ba" "Ashe kin iya hira Idon kuka" ji tayi gabanta ya fadi. Muryar da ko cikin bacci yanzu tasan zata gane taji. Kamar yana gabanta ta dan russuna a kunyace ta gaishe shi. "Har kin gane mai magana, ko kuwa dai wayancewa kika yi?" Tana murmushi tace "Na gane" Col. Ishaq ya gyara kwanciyarsa. Shi bai ma san dalilin da yasa yayi mata waya da safe haka ba. "To waye?" "Baban Amatullah" "Uhmm uhmm, a wurinta kadai nake baba. It seems ko sunana baki sani ba. Shiyasa jiya kika kasa fadawa yayanki" Asmau taji muryarsa kamar baiji dadin hakan ba tace "na sani kuma na fada masa ma" Magana yake kamar maganar aiki ce mai zaman kanta yace "me kika ce masa? I am sure ba Baban Safina kika ce ba". Ita fa kunyarsa take ji. Ganinsa take yi babban mutum mai matukar kwarjini da cika ido shiyasa bata tsawaita hira dashi. Sake maimaita tambayar yayi tace "Col I. M Jikamshi" Wani iri yaji yadda ta fadi sunan a hankali kamar bata so yaji. "I. M Jikamshi yana rokon alfarmar ayi saving din numbarsa saboda kada ki sake kirana Zulaiha. By the way ina princess dina? "Ana yi mata wanka" "To zan sake kira anjima ki hadani da ita. Ina fata kinji request dina. Idan kika sake kirana da sunan mata zamu kulleki ni da Safina. Ki gaida da Umma." Amsa masa tayi da to...tana 'yar dariya ta ajiye wayar. Mimi babbar 'yar Shemau ce ta shigo tana kiranta Umma tace tazo falo. Hijab ta saka ta fito daidai lokacin da Qasim ya dago kansa. Suna hada ido nata ya ciko da hawaye shi kuma nasa suka yi ja sosai. Ya kura mata ido yana kallonta "Asmau

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});