Chapter 93
Chapter 93
inda alkhairinki yake ba" "In sha Allah zan dage da yin istikhara. Allah Yasa yankewar zaman nawa a gida tazo. Nima nayi auren nan na huta da gorin Anti" "Ke ba'a cewa haka, aure ai saboda Allah ake yinsa ba gorin kowa ba. Da baki samu da wuri ba ai ba laifinki bane. Auren wuri ko rashinsa jarabawace wallahi" Murmushin yake kawai Walida tayi tace "Kada ki manta na girmeki da fin shekara. Ni fa ina jin kamshin shekara talatin. Gorin dangi anyi anyi har na saba dashi" "Masu shekaru arbain suce me Walida? Nayi tunanin yanzu ke mai iya bawa wasu shawara ce idan kika duba rayuwarmu. Kowane bawa mace ko namiji akwai hanyar da Allah ke gwada imaninsa. Fatanmu kada Allah Yasa mu kasa hakuri har mu fadawa shirka." Sun cigaba da hirarsu Asmau ta soma jin zuciyarta na tashi. Da gudu ta tashi ta tafi toilet din cikin falon ta rinka kwara amai kamar kayan cikinta zasu fita. Walida duk ta gama tsorata ta dafe mata baya tana sannu. Hirar da basu karasa ba kenan sai da ta sani nutsuwa Walida tace "ke kuma aka ake yi sai dai idona ya gane min. Meye nufinki da, wato sai ya fito na gani kamar kowa." Ta kalli saitin cikin Asmau "dan albarka ko yar albarka Mama Walida na gaisuwa. Wannan aman nasan so kake nasan da zamanka. Ranka ya dade dan soja" Asmau tayi murmushi mai ciwo. Ina ma dai gaske ne, "Walida ba ciki bane wallahi, kwanakin nan wake baya zama a cikina. Rannan ma daga cin kosai sai amai" "Ban gane ba ciki bane, gashi kince wake na saka ki amai. Kin gwada ne kinga babu?" "Babu amfanin gwajin nasan babu" Walida bata gaskata ta ba tace "kina tsarin iyali ne, me ya kaiki daga aure ki fara da bin tsarin nan na sai an gama amarci" Asmau tace "kema kinsan bazan soma ba" "To mene ne, Asmau kinsan dai zaki iya fada min. Ni na iya karanta miki nawa sirrin amma ke..." Ganin bata ji dadi ba Asmau ta fada mata komai game da Col. Ishaq "Wannan sirrinmu ne daga mu sai iyaye muka sani." Sosai Walida taji tausayin Asmau. Su kuma kullum sai sun hadu da wani nau'i na jarabawa. "Naji yar uwa kuma ba fahimta. Amma haihuwa ta Allah ce. Shi ya tabbatar bazai taba haihuwa bane? Ki gwada yin test a gida idan babu shikenan. Sai da kika fara aman ma na kula kinyi haske kin kara jiki. Da na zata duk na amarcin ne" "Walida ina son haihuwa da Jikamshina amma shekarun da yayi a auren fari sun ishemu shaida. Kada ki saka min rai da abinda yayi min nisa" Walida ta tashi ta dauki mayafi da purse dinta daga cikin jaka "kinga bari naje can wurin titi naga kamar akwai pharmacy. Zan siyo miki PT strip ki gwada. Idan babu komai ba sai ya sani ba" Bata saurari wani batu daga Asmau ba ta fita. Wurin mintuna ashirin sai gata ta dawo tayi uban gumi. Tasha yawo domin inda ta zata pharmacy ne ba shi bane sai da aka kwatanta mata wani. Asmau ta dage bazata yi gwajin ba Walida ta ji haushi sosai. "Ko albarkacin tafiyar da nayi ai kya yi min kara ki gwada." Da kyar da nuna bacin rai Asmau ta karbi tsinken gwajin guda biyu ta shiga bandaki. Bata fi minti uku ba Walida taji ta kwalla kara. A razane ta tashi tayi hanyar bandakin suka yi karo da Asmau da ta fito. Walida na cewa me ta faru ta rungumeta sosai sai kuma kuka da dariya a hade. "Kin gani Walida *ciki* *cikin haihuwa* gareni. Wayyo Allah Jikamshina Allah Yana sane da bayinSa" Wayarta ta tafi daukowa suna ta dariya ita da Walida. Har ta nemo sunansa zata kira Walida ta karbe wayar. "Mutumin da ya kwashi shekaru yana neman haihuwa zaki fadawa kina da ciki a waya? Haba kawalli, ai yau ranarsa ce. Tashi zakiyi mu shiga kitchen ki hada masa special abinci mu sake gyara gidan nan. Idan da hali tambaye shi muje gidan kunshi naga naki ya kusa ficewa. Ana yi miki zanyi miki kitson barebari kanana" Asmau tayi dariya tana shafa ciki. Wai cikin Jikamshinta ne a tare da ita. "Nayi girki sai dai na kara masa wani abin ko farfesu haka. Bari na tambayi kunshin" Sai da tayi da gaske ta iya boyewa bata fada masa a waya ba. Bai hanata zuwa ba yace su je da Mal Sabo amma idan akwai layi sosai ta dawo gida baya son dawowa dinnan ya tarar bata nan. Cikin sauri sauri suka sake kimtsa gidan suka tafi. Ana gama saka mata lallen Walida ta kama kanta tayi mata kitso. Shuku ne wani sabon style mai kyau da yake gashin nada cika sosai yayi mata kyau fuskarta ta kara fitowa. Sai da aka dauko Amatullah daga makaranta aka zo daukarsu. Har gida suka kai Walida Asmau tana ta yi mata godiya. Suna zuwa gida tayiwa Amatullah wanka ta saka mata wasu kayan sannan ta barta a daki saboda zata kunna turaren wuta kada ya dameta. Tana gamawa taje ta bata lokaci wurin wanka da shiriyawa. Karfe tara a gida tayiwa Col. Ishaq. Asmau da Amatullah suka taro shi tun daga bakin kofa. Binta yayi da kallo ya kasa dauke idonsa. Kullum tana masa kwalliya amm yau kam ba don Amatullah na wurin ba bai san me zaiyi ba. Tana rike da hannunsa suka tafi daki zata taimaka masa yayi wanka yace "Kamar na cinyeki Matar Jikamshi. Kinyi kyau da yawa" Tayi murmushi "nagode amma ko zaka cinyeni ka bari ka fara cin abinci" Kusan tura shi bandaki tayi don yaki tafiya sai tsokanarta yake. Da ya gama ya dawo falo inda ta zuba musu abinci a plate daya har Amatullah wanda hakan tsarinsa ne cin abincin dare tare. Suna ci yana kallon yadda take ta murmushi da fara'a ya ajiye cokalinsa yace "ki taimakeni ki fada min abinda yake ranki ya saka min ke cikin irin wannan farincikin." "Sai mun gama cin abinci" Ya kwabe fuska "bazan iya cigaba da cin abincin nan ba duk dadinsa. So nake kawai ki fada min. Tun dazu kin sa kwakwalwata ta tafi dogon bincike ta kasa samun amsa" "Ka bari mu gama please" Shi kam hakurinsa ya kare. Tun dazu yana kallo ko abincin kirki bata ci ba sai murmushi. Ya dan tabata ta kallo fuskarsa. A hankali yadda ita kadai zata ji yace "ko ki fada min yanzu ko mu kwashi kunya a gaban 'yarmu" Asmau ta gane me yake nufi duk da tana tunanin bazai iya ba amma Jikamshinta bashi da tabbas. Tashi tayi ta tafi daki ya bi bayanta da sauri. Kafin ta rufe kofar taji ya rungumota suna kallon juna "Rada min idan baki so dakin ya sani bazan fadawa Safina kinyi yada ba" Tayi dariya sannan ta kai bakinta saitin kunnensa "Allah Yayi mana kyautar da har abada bazamu taba dena gode maSa ba, Jikamshina..." Kasa fada tayi sai ta kama hannunsa ta dora akan cikinta "Akwai kyautar Allah a cikin nan" Ya ware ido sosai yana jiran karin bayani "go on" Rungume shi tayi saboda kunyarsa take ji sosai a wannan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103