Chapter 49
Chapter 49
sai godiya da fatan alkhairi amma don Allah ka janye maganar aure a tsakaninmu. Maganar aure ba ta mace irina bace. Duk yadda zan so bani da wani mutumci da kima da zan kai gidan aure. Amatullah ko naki ko naso 'yarka ce amma don Allah mu bar maganar aure." Dama yasan da wuya ta amince kai tsaye. "Ba cewa nayi ki bani amsa yanzun nan ba. Zan baki lokaci kiyi tunani. Amma ki sani kamar yadda aure yake zama garkuwa ga kowace mace kema shine mutumcinki. Zamanki a haka shine zai janyo miki duk abinda kike gudu wato surutun mutane." "Ni dai....." Hannu ya daga mata alamun tayi shiru ya tashi tsaye "kiyi tunani nace kuma kiyi shawara da duk wanda kika san zai baki shawara tagari" Rasa abin fada tayi kawai ta sanar dashi batun tafiyarsu a washegari yayi mata addua sannan yace zai zo idan ta dawo yasan lokacin tayi duk wani tunani da zata yi. Bayan tafiyarsa Asmau ta shiga tashin hankali. Ko zata yi aure ba dai da Qasim ba. Idan ta amince tamkar taci amanar Abubakar ne. Kana ganinta kasan tana cikin damuwa ta tafi daki da niyar kwanciya wayarta ta soma kara. Sai da gabanta ya fadi da taga sunan mai kiran. Kwana biyu tun ranar da taki amsa wayarsa bai kara kiranta ba sai yau. Zuciyarta ce ta rinka bugu da sauri da sauri amma ta kasa amsa kiran. Text taga ya turo mata _Idan Safina batayi bacci ba ki hadani da ita. Taki muryar ma ina son ji amma ba a waya ba, so wayar ba taki bace._ Wani dan murmushi ne ya subuce mata. Sai kuma ta dan dake tana yiwa zuciyarta tuni da cewar ta manta da maganar aure. Babu wani namiji da zai aureta a yanayin da take ciki komai tsahon lokaci ace wata rana bai goranta mata irin rayuwar da tayi a baya ba. Dakin Umma taje ta bawa Amatullah dake aikin wasa da Husna wayar da ya sake kira. Kusan minti ashirin tana ta yi masa hira sannan mikawa Asmau. Da ta karba sakawa tayi a kunnenta tayi shiru tana so taji ko ya ajiye. Yanayin yadda take saukar da numfashi ne ya tabbatar masa ta karbi wayar. Murmushi yayi kamar tana kallonsa yace "Ana so ana kaiwa kasuwa" Da sauri Asmau ta kashe wayar tana dariya. Me ya kaita saka wayar a kunnenta ne. Umma tace "ke lafiyarki kuwa?" Tayi saurin daidaita kanta. Yanzu fa ta gama cewa babu zancen aure a sauran rayuwarta. Me yasa take jin wani daban idan al'amarin ya shafi Jikamshi. ***** Col. Ishaq yana zaune ya saka abinci a gaba bai ci ba ya soma wayar. Dariyar da yake yiwa Asmau ce tasa Hajiya kallonsa. "Yaya dai kake dariya kai kadai? Kwana biyu na fuskanci wani nishadi kake ji." "Hajiyata babu komai" abincin yaci dan kadan ya sa Bilkisu ta kwashe kwanukan. Wai shine tunanin mace ya mayar haka. Abin da mamaki, duk dakiya irin ta soja yanzu baya jimawa sai Asmau ta fado masa. ****** Da wuri suka tashi aka karasa shiri saboda Yassar yana son dawowa a ranar. Kafin karfe goma na safe sun hau hanya bayan sun biya gidan Mama sunyi mata sallama. Aina'u tana gaba Asmau na zaune a baya da baby Husna da Amatullah. Sunyi nisa Qasim ya kirata. Har kunya taji saboda yace ta kirashi kafin su fito taki kira, a cewarta kada ta sa masa rai yayi zaton zata amince nan gaba. Adduar neman tsari yayi musu sannan ya gaisa da Amatullah. Ba dadewa kuma Col. Ishaq yayi mata text. Lokacin bai dade da shiga office dinsa ba. _Zan kira ki yanzu ki fara dauka kafin ki hadani da princess dina._ Ya zata yi ne da Jikamshi. Duk irin wannan abubuwan da yake yi mata kara kashe mata jiki yake yi. A daya bangaren kuma tana ganin gangancinta da har ta bari yake tasiri a zuciyarta haka. Idan har aure ya zama dole a kanta ma bashi ya kamata ta aura ba. Qasim yafi kusanci da ita, yafi sanin dukkan matsalarta. Amma Jikamshi shine a ranki zuciyarta ta tuna mata kafin wayar ta fara ringing. A kasalance ta daga wayar ta kara a kunnenta kamar tana jin tsoron amsawa. Shi kadai ya sauke ajiyar zuciya da yaji ta dauka. "Just wanted to let you know how much I miss you." Muryarsa da komai nasa daban take jinsa. Ga wani girmansa da take gani a kullum. Lumshe ido tayi batare da tayi koda gyaran murya ba. "Idan kin janye yajin aikin yi min magana ki fada min zan zo na ganki. Ina Princess dina?" Mika mata wayar tayi ta fara bashi labarin tun dazu suke cikin mota suna ta tafiya. Ina zasu je da safen nan ya tambayi kansa. Sai kuma ya tambayeta waye yake tuka motar tace Uncle Yassay ne. Yana son jin inda zasu je amma kuma baya son tilasta Asmau tayi masa magana. Karshe yace tace masa ya kirashu idan sun tsaya. Bata ajiye wayar ba ta fadi sakon. Yassar yasa Ainau ta danna speaker a wayar. Gaisawa suka yi ya fada masa inda zasu je. Col. Ishaq yace to a kula masa da 'yarsa. Sai da ya ajiye wayar ya hau tunanin ko kwana nawa zasuyi. Kwana biyun da baiji murya ko yaga Asmau ba baya jindadi. ***** A gidan Anti Bintu yau tun safe suke kitchen ita da 'ya'yanta. Yadda kasan bata ga Asmau ba bayan dawowarta haka take ji. Maman mijinta Kawu Yuduf tana gidan ana gyara a nata gidan. Tun da taga suna aikin nam take tabe baki tana kananan surutai. Bata tashi yin magana sosai ba sai da taji tsayuwar mota taga duk sun fita tarbarsu Asmau. Suna shigowa ta ganeta don dama ta santa. Yar tsohuwa tace "Yanzu duk wannan doki da murnar na ganin shegiya ne da uwarta, banda lalacecar zamani yaushe 'ya zatayi zina sannan a rinka rawar jiki don ta dawo kamar wadda tayi wani abin arziki" Anti Bintu ta rasa me zata ce don tsabar kunya. Asmau kuwa tuni ta soma zubar da hawaye. Babbar 'yar Anti Bintu da ake shirin aurarwa bata rai tace "haba Gwaggo" "Wane irin haba, barni nayi magana son raina. Ba 'yar zinar bace ko kuwa uwarta bata bar mata abin kunya ba na 'ya'ya da jikoki?" Ba Asmau ba hatta Aina'u sai da tayi kuka. Allah Ya rufa musu asiri ma Kawu Yusuf yana gidan ya fito daidai sanda babarsa ke yabawa Asmau maganganu. "Gwaggo me ya kawo wannan maganar kuma. Kaddara ce wacce bata wuce kan kowa" "A'a wallahi irin wannan kaddarar sai 'ya'yan da basu da tsayayye a kansu. Nawa jikokin Allah Ya tsare min su. Kowacce zata kai budurcinta gidan miji" Kuka wiwi Asmau take yi. Kukan nata ba don abinda Gwaggo ta fada bane ai duk abinda tace gaskiya ne. Gaskiya kuwa akwaita da daci. Lallai sun tafka babban kuskure a rayuwarsu kuma muddin tana numfashi tasan wannan abu bazai taba gogewa daga zukatan mutane ba. Mutumci madara ne idan ya zube ba'a taba iya kwashe shi gabadaya. Anti Bintu ta kaisu dakinta tana ta rarrashi da bata baki. Yassar ya kasa zama ya fice ya koma mota rai a bace.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103