Chapter 12
Chapter 12
kaya masu kyau. Haka aka yi biki aka kawo amarya Kano ita da kanwarta Bintu saboda bazata iya barin kanwar a hannun matar kawunsu ba ta cigaba da azabtuwa. Wani bangare aka gyara musu a cikin gidan iyayensa suka tare a ciki. Zaman lafiya sosai suke yi da mijinta sai dai a wurin Hajjo da 'yan uwansa tana ganin wulakanci mara misaltuwa. Daga ita har kanwarta basu da sunan da ya wuce Mayya. Gashi dama duk suna da idanuwa Tubarakallah. Duk wani aiki na gidan ya dawo wuyansu amma bata taba korafi ba. Kullum Shu'aibu sai dai ya bata hakuri lokacin yana ta fafutukar neman aiki. A haka ta samu ciki har sau uku yana barewa saboda aikin wahala. A karo na ukun ne da safe Hajjo ta shigo taga Bara'atu bata sha kunu da kosan da ta aiko mata dashi ba wanda babansu Shu'aibu ne ya tilasta mata dama. Fuska babu walwala tace "Au baku karya ba har yanzu saboda ki jawo min fada wurin Malam yace bana kula dake?" Daga kwance inda take saboda rashin kuzari Bara'atu tace "Kiyi hakuri na koshi ne". Hajjo tayi dariya "yo ba dole ki koshi ba, kunyi kalaci da jikana ke da kanwarki. Ai Shu'aibu ya gama janyo mana masifa. Nan gaba kadan ma mu zaku bi ku lamushe." Bayan ta gama fadanta ta fita Bara'atu babu abinda take yi sai kuka. A wannan yanayin Shu'aibu yazo ya sameta. Hakuri ya bata kamar kullum tare da kyakkyawan albishir na cewa ya sami aiki a jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria a matsayin lecturer matakin farko. Kuma har da gida aka bashi. Murna a wurin Bara'atu ba'a magana. Kafin su tattara su koma Zaria ne mahaifinsa ya fara cuta yana ta ramewa. Hajjo tasha kuka tana rokon Bara'atu akan ta sakar mata kurwar miji. ABINDA AKE GUDU🙆🏽12 Batul Mamman💖 *BAYAN SHEKARA DAYA* Anti Bintu tazo Kano wurin yayarta yawon arba'in. Tunda tazo kullum sai sun fita kasuwa siyayyar kayan amfanin gida. Duk wani kudin Bara'atu na albashi, kasuwanci da abinda ta samu na gado ta hada shi a gini da zuba kayan bukata a sabon gidan. A lokacin falo da dakuna biyu kawai ta gama sai kitchen amma bahaushe yace da babu gara ba dadi. Hatta sutura da Hajjo ke yi mata gorin bata siyawa yaranta duk ta siya. Dama tara kudin take sai ta gama da abinda yafi mahimmanci. Sai da ta gama shirinta tsaf sannan wata juma'a bayan su Asmau sun dawo daga makaranta tasa sukayi wanka duk ta basu sababbin kaya sannan ta hada sauran 'yan kayansu suka tafi dakin Hajjo. Duk yaran mamaki ya ishe su ina Umma zata kaisu sun kwashe duka kaya. Kwadon zogale take ci yaran Rabe suna zaune suna wasa a gefenta tana dariya. Shigowar Bara'atu da 'ya'yanta yasa ta hade rai. Dan Rabe na biyu sarkin gulma ya ruga ya fadawa babansa ga Anti Bara da su Jafar zasu fita yau sunyi kwalliya. Daga shi sai dogon wando haka ya fito da sauri jin kwaf. Bara'atu na dauke da jaririyar Bintu tace " Hajjo albarkacin zaman tare a yafemu Allah Yayi zamu tashi" Zaro ido sukayi ita da Rabe. Shi a son ransa idan Bara'atu ta gaji da takurata da akeyi ta yarda da aurensu. A ranar ma zai saki Sagira. "Ina zaki kai min yaran da kike cewa zaku tashi? Idan tafiya zakiyi ke kadai dai ga hanya nan." "Ba nisa zanyi ba Hajjo, nan layin gidan sabon kwamishinan 'yan sanda zan koma. Cikin ikon Allah na kammala gini na." Ashar Rabe ya fara saki sannan yace "kika kammala wane ginin? Waye ya baki filin da kudin ginin?kada ki raina mana wayo wani saurayin kika yi kuke zaman....." Katse shi tayi kafin yayi barambarama gaban yara. "Fili dai tare muka siya da wannan da kuke ciki ni da babansu Yassar. Ina sana'a ina aiki. Allah Ya buda min gashi nayi gidan kaina. Wannan da kuke ciki kuma har abada ku sani cewa gidan marayu ne. Allah SWT kuma Yace wanda yaci dukiyar marayu tamkar yana ciwa cikinsa wuta ne." Hajjo ta bata rai "nufinki mune 'yan wutan..Bara'atu ki kiyayeni wallahi. Kuma idan kika fita da yaran nan to ki sani babu ni babu su." "Ai aikin gama ya gama. Yara dai ke kika haifi babansu saboda haka jininki ne. In Allah Ya yarda zasu rinka zuwa gaisheki tunda ba nisa mukayi ba." Daga haka suka fice Rabe yana binsu a baya yana kiranta. ***** *Sabuwar Rayuwa* Wannan tashin nasu shine ya kara kiyayya tsakanin iyalan mariyayi Shu'aibu da gidan Hajjo. Kamar yadda ta fada duk juma'a bayan masallaci take tura yaran gaishe da Hajjo. Manyan kullum sai sun dawo rai a bace ko da hawaye a idonsu. Amma hakan baisa ta dena turasu ba saboda tasan su din dai suka rage musu dangin uba. Rayuwa sabuwa suke yi cike da 'yanci da jindadi. Bara'atu ta dage wurin bawa yaranta tarbiya. Sannan tana nuna musu soyayya irin wadda bazata sa su sangarce ba. Shakuwa mai karfi ce a tsakaninta da 'ya'yanta. Washegarin tarewarsu suka shiga makota domin gabatar da kai. Lokacin da suka shiga gidan Kwamishina Mama Yalwa tayi musu tarba ta karramawa. Dama sun saba da Umma. Duk yaranta suna gida ta kirasu ta gabatar dasu ga 'yan uwansu kamar yadda ta fada musu. Abdulhalim, Nasiba da Abubakar dai duk sun girmesu amma suma sunyi kokarin jansu a jiki. Bayan 'yan kwanaki ne Mama Yalwa taje gidan Umma take sanar da ita Baba yace ta rinka turo su Asmau ana yin magariba masallacin gidansu akwai Malamin da yake koyar dasu Sadiya karatun Qur'ani zuwa karfe tara. Umma taji dadi sosai,duk da suna zuwa islamiyya amma wannan ma zai taimaka kuma ba nisa suka yi da gida ba. _Asmau S. Yahya_ Ranar farko da zasu je makarantar kowa yana doki banda Asmau. Haka take da tsoron mutane. Duk gidansu ita ce ta kasa sakewa da yaran Mama. Kowa ya shirya ta kwanta ciwon cikin karya saboda taji ance kowa karatunsa shi kadai malam zai biyawa. Yadda zata yi karatu a gaban su Suwaiba ne yake kara tsorata ta. Umma na ganinta tasan ciwon karya ne. Da rarrashi ta lallabata suka tafi suna idar da sallar magriba. Cikin gidan suka fara zuwa suka gaishe da Mama sannan suka fito waje. Suwaiba 'yar Mama ta hudu ita ce kusan sa'ar Shema'u amma duka ita da Sadiya sun zama kawaye da Shema'un. Tare suka fito zuwa masallacin Asmau na bin bayansu rike da hannun Aina'u. Malam Hadi yana zaune tare da Abdulhalim, Abubakar da Umar. Suna zuwa gaishe shi suka yi kowa ya sami wurin zama. Sai da ya gama da manyan sannan yaji karatun su Suwaiba. Daga nan ya fara jin inda su Asmau suka tsaya yace kowa sai ya biya surar karshe inda ya tsaya. A nan ake yinta ana zuwa kan Asmau da ta fuskanci idanu sun dawo kanta tana yin Bismillah sai hawaye. Malam yace ta barshi ya gama da sauran .Shema'u tayi tsaki tace " malam wallahi ko a islamiyya haka take yi sai taji bulala take kawo hadda." Murmushi yayi "ni bana duka kinji Ma'u. Bari na gama da kannenki sai ki biya min." Hatta Aina'u sai da ta karanta suratul Ikhlas
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103