Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 5

Chapter 5

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

mutanen cikinsa. Karar fanka kawai ake ji sai jefi jefi wannan ya kalli wannan. Suna shigowa likitan ta karbi report din daga hannun Nasiba ta karanta. Ita ma abin ya bata mamaki domin kuwa Abdulhalim yayi mata bayanin dalilin suman Asmau. Ta bukaci kowa ya fita suka fice babu musu. Sirinji ta dauko daga aljihun rigar asibitinta ta sake daukar jinin Asmau. Bayan ta gama tace "Asmau yaushe ne lokaci na karshe da kika ga al'adarki?" Tun dazu kwakwalwarta ta kulle babu wani tunani da take iya yi sai yanzu ta dawo hayyacinta da taji wannan tambayar. Hankali a tashi tace " biyu ga watan da ya wuce na gama". "Yanzu kuma gashi ana karshen wata na gabansa. Yau kinga ashirin da takwas ga wata." Likitan ta fada tana rubutu a wata takarda. Fuskarta na kan takardar tace " ki fada min gaskiya kin taba tarayya da namiji?" Kasa bada amsa tayi sai jikinta da ya kara mugun yin sanyi. Fatan mutuwa kawai take yi akan bala'in da yake tunkaro ta. Da taki magana likitan ta fita su Umma suka dawo har yanzu babu mai cewa uffan kowa zuciyarsa na sake-sake. A haka likitar ta dawo kana ganin fuskarta kasan labarin da ta kawo bashi da dadi. Ita kanta ta tausayawa mutanen ta dan sunkuyar da kai "a bisa binciken da nayi da kuma amsar da Asmau ta bani ya nuna tana da CIKI na kusan wata biyu." La haula wala quwwata illa billah....a rana daya duk wani farincikin gidajen biyu ya koma kishiyarsa. Umma tayi kan Asmau wadda dama tasan haka zata faru. "Asmau me nayi miki zaki yi min muguwar sakayya irin wannan? Uban waye yayi miki ciki? Har kinsan ki kebe da namiji ba tare da aure ba a tsakaninku?" Tana magana tana dukan Asmau ko ta ina. Su Anti Bintu ne suka yi kokarin riketa tana fada tana kuka. Shema'u ma gefe ta koma tana nata kukan. Wane irin abin kunya ne wannan Asmau ta janyo musu a wannan halin da suke ciki? Umma na dukanta duk da rashin lafiyar da take ciki amma ta kasa yin kuka. Biyewa son zuciya na 'yan mintuna ya wargaza dukkan wani farinciki da ta taba sani a rayuwarta. Irin ABINDA AKE GUDU kenan. Yau asirinta ya gama tonuwa. Sirrin boye ya fito fili bata da abinyi sai yadda Allah Yayi da ita. Mama ta rike hannun Umma da take shirin sake dukan Asmau "ba da duka zamu tambayeta ba Bara'atu. Kada ki bari bacin rai yasa kiyi aikin dana sani." Muryar Umma har ta dashe tace "akwai wani dana sani daya wuce haihuwar wannan yarinyar? Fyade aka yi miki ko kwaya kika sha da har zaki yarda da namijin da ba naki ba?" A hankali Asmau ta sakko daga kan gadon har allurar da ake yi mata karin ruwa ta fita daga hannunta bata sani ba jini ya rinka zuba daga hannun. Ranar wanka ba'a boyon cibi. Sai a lokacin ta soma kuka ta durkusa akan gwiwoyinta a gabansu Umma. "Tsautayi ne da sharrin shaidan. Don girman Allah ku yafe mana. Wallahi sau daya ne kawai. Idan har ina da ciki na Abubakar ne". Cikin tsawa Mama tace "kin ma isa ki dora masa. Wallahi nasan karya kike yi saboda kinga kasa ta rufe masa ido shine zakiyi masa irin wannan mummunan kazafi?" Magana take tana haki saboda bacin rai, sai kuma hawaye. "Yanzu kinyi masa adalci kenan? Ko kwana baiyi a kabarinsa ba kike binsa da mummunar shaida bayan kinsan mala'iku suna tsayawa karbar shaida akan mamaci. Allah Ya isa tsakanina dake. Har yaushe kika ga Abubakar din ma? Mutumin da sau biyu yake zuwa Kano a wata. A can makarantarku dai kika hadu da wanda yayi miki" Anti Bintu ta kama hannun Asmau ta tayar da ita tsaye cikin jin haushin maganar Mama gashi Umma taki cewa komai "wannan magana bata asibiti bace. Mu bari idan an sallameta sai ayi a gida. Amma kowa yasan bata da wani saurayi bayan Abubakar." "Babu wata magana da zamuyi a gida. Kai, ku wuce mu tafi." ta fadawa Abdulhalim da Nasiba. Dukkaninsu an rasa mai bakin magana. Tabbas Abubakar ne kadai saurayin Asmau. To amma kowa yayi shaidarsa wurin kyaun hali. Mutum ne mai kawaici da kunya. Ita kanta Asma'un ba don a gabansu aka yi komai ba sai su karyata saboda itama ko 'yan unguwa zasu shaideta da kyaun hali. Abdulhalim yaso ya tsaya domin a kare maganar a nan Mama ta daka masa tsawa dole yabi bayanta suka fita tana ta bambami. Bude kofar dakin kenan suka hadu da mata sun kai shabiyar daga gidan rasuwar suke sun taho jin halin da Asmau take ciki. Kana ganinsu kasan duk abinda ake yi a cikin dakin sun gama ji. Mama ko kallo basu isheta ba tayi gaba su Nasiba na bin bayanta. Matan dai tunda har an gansu dakin suka shiga suna tambayar ya mai jiki. Anti Bintu tace da sauki suka tashi ko minti daya cikakke basu yi ba suka fice ana ta mayar da zance. Bayan fitarsu Anti Bintu tace "Yaya Bara baki ce komai ba kina jin abinda Maman Abubakar take fada." "Me zance Bintu? Kin taba ganin cikin shege yayi uba kai tsaye a kasar musulmi? Duk abinda Mama Yalwa ta fada tayi min daidai. Nima da namijin ne nawa bazan yarda a kakaba masa cikin shege ba." Hada ido suka yi da Asmau Umma ta sakar mata wani mugun kallo. Abinda yafi wannan ma tasan zata gani tunda haka ta faru. Kusa da Umman ta dawo ta sake durkusawa a kasa ga wani irin jiri da take ji, kirjinta kuma kamar ana hura wuta. "Umma ki yafe min. Wallahi sharrin shaidan ne kuma muna ta istigifari kullum. Wallahi bazan kara ba wannan ma kaddara ce. Umma...." Ture ta Umma tayi ta dubi inda Shema'u da Jafar suke tsaye suna hawaye "Jafar fita ka samar mana abin hawa mu koma gida." "Asma'un fa?" Anti Bintu ta tambaya. Tamkar da dutse tayi maganar haka Umma ta shareta. Bayan Jafar ya dawo Umma ta rike hannun Shema'u saboda kafarta data rike suka yi hanyar fita. Asmau na ganin haka ta tashi tabi bayansu Anti Bintu na kiranta bata tsaya ba. Haka suka fice daga asibitin ga dare suka shiga tasi din da Jafar ya tsayar. Har suka isa gida babu mai magana a cikinsu. Abin mamaki nasu gidan a cike suka same shi bayan tunda aka yi rasuwar aka koma gidansu Abubakar. Bacin ran Umma ya sake karuwa don tasan labari ya riga ya iske duka umguwar. Sai cewa akeyi ya jikin Asmau. Aka rasa me amsa musu tunda sun san ainihin abinda ya kawo su. A cikin falo Umma zata wuce dakinta taji ance "Ke Bara'atu dakata." Ta gane muryar mai maganar ta san ba karamin rashin mutumci yazo yi mata ba. Alh Rabe ne kanin marigayi. Kin tsayawa tayi sai da taji muryar Hajjo mahaifiyar maigidanta sannan ta juyo. Kuka ne ya kwace mata yadda taga duk 'yan uwan mijinta a wurin mazansu da matansu ga kuma mahaifiyarsu. Allah Yasa itama akwai nata 'yan uwan wadanda suka zo biki daga Wushishi ta jihar Niger. Dangin mijinta basu taba kaunarta ba gashi Asmau ta sake shafa

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});