Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 75

Chapter 75

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

idan baka dena kallona na ba" "Tashi ki tafi ban hanaki ba. Amma ki sani zan je na sami 'yan matan Warri na kalla son raina" A shagwabe tace "don Allah ko da wasa ka dena fadin haka. Kada kasa na kasa bacci yau" "Shine kike son hanani baccin? Daga gobe fa zanyi sati uku ban sakaki a ido ba. Ji nake kamar a daura auren nan na tafi dake. Idan mun dawo sai ayi bikin, kada kice wani abu nasan kema haka kike so ko Matar Jikamshi" wannan lumshe idon yake mata. Ita kuwa ta soma dariya. "Wane irin aure ne amarya da ango zasuyi tafiya bayan an dawo ayi biki." Yace "to kawai idan mun dawo mu wuce gidanmu ko. Tsayawa bikin duk bata lokaci ne." Dariya Asmau take yi kawai. Jikamshinta yau sai wani marairaicewa yake. "Kada ka damu ni dama ba wani biki nake so ba. Zuwa za'ayi ayi ta kallona. Na fadawa Umma ayi komai a rana daya. Bayan daurin aure mata kadan su zo a kaini." Col. Ishaq ya gane sarai dalilinta na yin haka. Yadda mata ke son biki amma tace bazatayi komai ba saboda surutun jamaa. Dena wasan yayi yace "Matar Jikamshi ko me kika yi na fada miki dole za'a sami masu magana. Bakiji ance Dan Adam mai wuyar gane hali ba. Idan kinyi biki ace baki da kunya ko makamancin haka, idan kin ki biki ace ko dan bikin nan batayi ba don kada mutane su je. A wurin Dan Adam bazaka taba fita ba. Saboda haka biki da akeyi abu na lokaci daya zukatan masoya suji dadi na makiya su fashe...." Da har ta fara kwalla sai yanzu tayi dariya. Shima biye mata yayi. "I am a soldier Matar Jikamshi. Dole nayi aure irin na sojoji. Su Safiyya suna can suna tsare tsare kamar yadda su Ainau suke yi. Zamuyi aure da biki kamar kowa kinji ko. Duk wanda ya fada miki mara dadi ki rinka tuna ranar asabar din da zaki tare a gidana. Ranar da Jikamshinki zai nuna miki matsayinki a rayuwarsa. Wannan ya isheki maganin duk wani bacin rai. Look forward to being Mrs Jikamshi a zahiri." Gyara zama yayi bayan ya gama maganar yana son ganin yanayinta. Kasa take kallo tana wannan murmushin da ta saba idan tana jin kunyarsa. Bai barta haka ba sai da ya tabbatar mata lallai bikinsu za'ayi taro kamar na kowa. Masu farinciki da 'yan saka ido kowa ana gayyatarsa. Addua zasu cigaba Allah Ya kare duk wani tashin hankali da abin ki har ayi a gama lafiya. Da zai tafi Asmau harda kuka. Tana ta cika masa baki sati uku ba komai bane zata iya jurewa ko basu hadu ba akwai waya. Hoto ya rinka daukarta fuska a kumbure saboda kuka. Da ya shiga mota ya tayar tace "Jikamshina don Allah kada ka kalli kowace mace. Ai ni kadai na isheka ko?" Ya murmusa "anya kuwa? A haka kinsan bazan tabbatar ba sai nan gaba. Idan rabon na hadu da kishiyar matar jikamshi ne a can sai ki tayani addua" Ranta a bace ta zamo dankwalinta ta kasan mayafin da ta lullube kanta ta jefe shi dashi. Dariya yayi mata ya dauki dankwalin ya dora akan fuskarsa tare da rufe idanu. Muryarsa can kasa yace "Ina son kamshinki" Kunya taji ta mika masa hannu "don Allah ka bani" "Haba yarinya, dama ba roka nayi ba kika bani. Yanzu kuma yazo kenan. In sha Allah ke dashi sai a gidanki. Love you, kiyi min adduar tafiya" Tana kallo ya rataya dankwalin a wuyansa yaja mota kamar baya jin magiyar da take masa. Dafe kai tayi tana tunanin me zata ce idan aka tambayeta dankwalin. Tayi sa'a babu wanda ya kula. Kafin ta kwanta ya turo mata hotunansa ya ware dankwalin akan fuskarsa ya rungume da hannuwansa. Ranar har tayi bacci shi take tunani. Da sassafe ta kira shi bayan sun gaisa tayi ta jero masa addu'o'in neman tsari da sa'ar tafiya. Dadi kamar me haka ya rinka ji yana saka mata albarka. Haka suka yi ta waya yana hanya har suka isa. ***** Kwanci tashi sun je Zaria an sha biki lafiya. 'Yan uwansu na Wushishi sun zo sosai suna cewa saura zuwa Kano bikin Asmau. Bayan an kai amarya Kaduna da suka dawo da daddare kafin su kwanta Anti Bintu ta kirata dakinta. Ita dama bata je kai amarya ba kamar yadda al'adar bahaushe take. Wata jarka karama ta dauko ta bawa Asmau. "Ga wannan zuma ce da aka yi mata hadi mai kyau. Kullum a kalla kisha cokali biyu. Kada ki sakata a gaba kiyi ta sha da yawa. A hankali zata ratsaki." Ta hado mata da wasu kullin magani duk na sha ne. Tace da kanta ta hadasu kayan amfanin jiki ne. Tunda ta fara bayani kan Asmau a kasa. Da farko kunya take ji daga baya sai hawaye. Anti Bintu ta rude "menene kuma Asmau?" "Anti yanzu a matsayin budurwa fa zanyi aure amma ....." Fadawa tayi jikin Anti Bintu ta rungumeta tana kuka. Itama ta biye mata tana kukan tana rarrashi. Umma dake bakin kofa tana jinsu itama da nata hawayen. Babu wani abu a duniya da zasu bawa Asmau ya dawo mata da budurcinta. Shi kam idan ya tafi ya tafi kenan. Shiyasa ake so mata mu kiyaye. Kada ki sayar dashi a waje wasu suci kudinki da sunan zai dawo. Halittar Allah da 'yan dabaru na mutane basa taba zama daya. "Ki dena kuka Asmau. Shima Ishaq din yasan komai ba yaudararsa kika yi ba. Amma dole ki gyara jikinki saboda rayuwar aure zakiyi yanzu. Ki cire yawan tunani don Allah. Bashi da fa'ida. Yawan kukan nan tamkar baki godewa Allah ba da ya ni'imtaki da samun masoyi. 'Yan mata da zawarawa nawa ke kwadayin irin wannan sai gashi ke Allah Ya kawo miki don Ya saukaka miki matsalolinki na baya." Haka ta dauki jakar da magungunan jiki a sabule. Yadda 'yan mata ke rawar kafar shan magani idan bikinsu yazo sai gashi ita jin abin take kawai wani iri. Yanzu haka za'a daura auren budurwa mai 'ya. Allah abin godiya. ***** Sun fi sati da dawowa Kano sannan Col. Ishaq ya dawo. Yana zuwa gida wanka kawai yayi tunda yayi sallah ko abinci ya kasa nutsuwa yaci ya fice. Hajiya ta girgiza kai, Allah Ya kara hada kawunansu su zauna lafiya. Asmau ta zauna ta hada abinci mai rai da lafiya wanda ya dace da tarbar bako. Bata taba yi masa abinci ba. Idan yazo lemo kawai take bashi da snacks saboda tana kunyar irin wannan. Yau ma Umma ce ta bawa Yassar kudi akan a siyo abubuwa na abinci yau kwadayi take ji. Tasan yau Ishaq zai dawo amma saboda kunya Asmau bazata yi yunkurin yi masa wani abu daban ba. Itama kuma hakan yafi mata. Bata taba bawa 'ya'yanta kofar idan saurayi zai zo ayi ta girke girke kamar maigida ba. Sai kaga 'ya'ya basa kunyar iyayensu. Bayan ta gama Umma tace "ki dibarwa Ishaq mana kinsan matafiyi kila yayi sha'awa." A kunyace ta diba ta ajiye masa nasa. Da ya iso Amatullah ta dafe shi tana ta murnar ganinsa. Yayi musu tsaraba ta doya da sauran abubuwan kudancin kasarmu.

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});