Chapter 79
Chapter 79
giya ya bugu yayi mata duka cikin jikinta ya bare. A yanzu haka babu irin wukakancin da basa gani ita da 'ya'yanta a wurin Zinaru da amaryar Gidado. Yi sukayi kamar basa ganin su Zinaru suka shiga hirarsu da Asmau da yan uwanta. Col. Ishaq ba karamin haushinsa yaji ba bare da ya fito yana tangadi alamun mayen jiya bai sake shi ba. Ya dubi Zulaiha da take gaishe da su Umma. Wahala ta mayar da ita wata iri. Idan za'a bashi dama daga Gidadon har uwarsa sai ya kullesu. Zulaiha tace "Ummi kinji dadi iyayenki sun yafe miki. Ji yadda kika koma nayi miki murna" Hajiya ce ta ce "kema in sha Allah bazamu tafi ba sai mun hadaki da naki iyayen. Asmau ta fada mana komai game da rayuwarki" Zibaru ta cafe "to tace muku tana bukatar taimako ne? Yarinya tana zaman auren soyayya da mijinta zaku shiga tsakani" Qasim ya taso mata "idan baki kiyaye bakinki ba wallahi idan nasa aka rufeki babu wanda ya isa ya fito dake" "Kaiiiiii, babar tawa kake yiwa tsawa" Gidado ya fada. Darajar 'ya'yansa tasa duk mazan nan su Jafar, Yassar, Abdulhalim ga soja da dan sanda basu rufeshi da duka ba. Zulaiha tana kuka tace "nasam bazasu yafe min ba. Shekarun da yawa. Kara na kaisu na zabi wannan rayuwar akan su" Asmau tayi ta bata baki ta amince da shawararsu ta zuwa gida. Zinaru tace "idan kika fita a bakin aurenki" Yau da Zulaiha ta sami masu tsaya mata bata ji maganar Zinaru ba tayi gaba 'ya'yanta na binta. Tana ji Zinaru tace Gidado ya sake ta. Dama me ya rage mata a auren nasa. Suna kallo duk suka fita. Zinaru tasan sun gama yawo domin kuwa korarsu zaayi daga gidan. Zulaiha ke kwatance har suka iso bakin gate din wani makeken gida. Gida ne babba na gani a fada. Asmau tace cikin tsantsar mamaki "nan ne gidaku?" "Nan ne Asmau" su Humaira ma duk mamaki suke wai daga nan mahaifiyarsu ta fito amma suke ganin kuncin rayuwa. Daga bakin gate kenan ma. Maigadi yayi musu iso akan cewa bakin mamanta ne. Jikinta a sanyaye suka shiga. Gidan ya kara fadi gashi ya dace da zamani. A wurin ajiye motoci ta hango kaninta da Alhajinsu. Zuciyarta tana dar dar Alhaji na hangota ya taho wurin da suke yana kallon Zulaiha. Shekarunta sha bakwai rabonta da gida. Ana jiran aji da wacce zai tarbi yarsa. A hankali yace "sai yau uwata? Sai yau kika iya tunawa kina da iyaye?" Abin tausayi Zulaiha ta fada jikin mahaifinta. Saboda yadda ta kode sai ka zata wa da kanwa ne ba uba da 'ya ba. Farinciki yake ji mara misaltuwa. Allah Ya karbi adduarsa 'yarsa ta dawo. Ba karamin fushi yayi da ita ba a da amma daga baya ya hakura sai dai yayi alkawarin babu mai zuwa gareta idan bata kawo kanta gida ba. A ciki ma wurin Innarta sai murna da kukan farinciki. Ga 'ya'yanta duk aka taru ana kallonsu. Duk 'yan uwanta suka taru ana murna. Alhajinsu yayi ta godiya ga su Umma da suka dawo da ita gida. Zama suka yi ana jajanta irin wannan hali da yara ke jefa kansu a dalilin soyayya sun yarda su rabu da kowa. Asmau da Zulaiha sun zauna suna ta mayar da zancen halin da suka tsinci kawunansu a ciki. Ta yanke shawarar nema takardarta a wurin Gidado. Ita da aure kuma sai a aljanna. Asmau tayi dariya tace "zaki yi ne tunda na sami miji kema zaki samu in sha Allah" ta bata labarin Jikamshinta da bikinsu da za'a fara nan da sati biyu. Zulaiha tace biki kam da ita za'ayi komai in sha Allah. Ranar ma a gidan Mami suka kwana washegari sai Kano ta Dabo tumbin giwa. Biki ya gabato ana ta rabon kati ABINDA AKE GUDU🙆🏽52 Batul Mamman💖 Daga 'yan uwan Asmau har na Col. Ishaq kowa shirin biki yake yi sosai. Ita har mamaki suke bata. Hala sun manta wace ce ita suke son yi mata biki irin wannan. Mutanen da zasu zo karshenta duk 'yan kallo ne wadanda zasu tafi da ita a baki. Sake yiwa Jikamshi korafi tayi akan haka yace shi bai taba damuwa da biki ba sai yanzu. Idan suka yi abin shiru shiru a gida shine mutane zasu sami na magana ace dama ansan dole ayi abin kamar na marasa gaskiya. Yanzu kuwa biki zasuyi su nunawa duniya farincikinsu da ni'imar Allah garesu. Dama tasan tuni yabi zugar su Shemau da Ainau shiyasa batayi mamakin amsarsa ba. Kwanansu biyu da dawowa Walida tazo gidansu har ta rakata karbo dinkunanta na fitar biki. Kokari suke su ajiye komai su mayar da kawancensu na da. Bata da niyar gayyatar sauran kawayen makaranta don basu nemeta ba a baya kuma dama bata dasu da yawa. Yanzu ma bata san ina yawancinsu suke ba. Duk wadda tazo bazai wuce bawa ido hakkinsa ba. Dinkuna sunyi kyau sosai. Kayan Amatullah ma ba'a magana. Musamman da yake kayan yara akwai daukar ido. Ita da su Mimin Shemau da Nanan Kawu Garzali mai sunan Hajjo duk anko akayi musu. A bangaren gyaran jiki da abinda ya shafi lalle kuwa takanas Nasiba yayar Abubakar tayiwa aminiyarta ta Nijar magana. Massouda kenan, matar da a Nijar din ma ji suke da ita. Taji labarin Asmau kaf a wurin kawarta kuma ta tausaya mata shiyasa tayi mata hadin kayansu masu kyau da tsada sosai don tace Asmau dole a gyarata a saya mata kima a wurin mijinta. Shi kanshi mijin wani girmansa take gani. Duk mutumin da zai iya auren mace kamar Asmau lallai ya cancanci yabo da jinjina. Dole a taya shi da adduar Allah Ya saka masa da alkhairi bisa wannan kyakkyawan aiki da yayi. A wannan lokacin idan kaga Asmau zaka so sake kallonta. Duk da dama can ita bata sahun farare amma fatarta ta kara kyau sosai tayi haske. Kuma duk wahalar nan ta baya da tasa ta rame yanzu cima ta canja ga kwanciyar hankali. Shiyasa jikinta ya dan dawo ta ciko. Idan Umma ta kalleta sai dai tayi godiya ga Allah. Bata ma so tayi tunanin halin da Asmau zata fada da bata hadu da mutanen kirki ba ko ta dawo gida. A dan tsukun lokacin Col. Ishaq ya damu sosai da rashin ganin Matarsa. Massoudan Nijar ta saba da irin wannan aikin na gyaran amare ta taho har gida ta murjeki da kyau. Saboda haka gidan Umma akayi mata masauki. Safe, rana, dare daga wannan turaren sai shafa wancan abin. Sau uku yana zuwa ana ce masa bazata iya fitowa ba. Ransa a bace a karo na hudu yace da Yassar idan bata fito ba wallahi bazai tafi ba komai dare. Yassar yayi murmushi wannan soyayya tana daukar hankalinsa sosai "ka bani dan lokaci zan fito da ita. Umma da matar da Anti Nasiba ta kawo ne basa bari ta fita. Yau kwana biyar ko kafar gidan nan bata fito ba" Fuskarsa sam babu walwala yace "Ka fadawa matar zan kara mata kudi amma gobe tayi shirin komawa garinsu aikin ya isa haka" Yassar ya kalli yadda yake magana kamar bashi yayi ba ya wani hade rai. Shi dai ya sosa keya ya tafi. To
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103