Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 40

Chapter 40

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

masu kudi. Yanzu dai ko da safe ne sai kayi yadda nace." Asmau ta jinjina bakin hali irin na Zinaru. Gashi Zulaiha laulayi take yi babu wanda ya sani sai ita. Har kuka tayi saboda bata son cigaba da haihuwa ga talauci da rashin gata. Sauri tayi taje dakin Zubaida ta fada mata abinda taji sai tayi tuntube da kwaftareren takalmin Gidado. Zinaru ta fito da sauri taga ko waye suka hada ido da Asmau. Ta dan ji tsoro da farko sai kuma ta dake ta soma kwalawa Zulaiha kira. Cikin bacci taji kiran da Zinaru ke yi mata ta fito tana murza ido. Zinaru tace "munyi magana ne da Gidado akan yadda Asamau ta raina ni da irin rashin jituwar dake tsakaninmu shine yace zai koreta. Ni kuma sai na tuna masa cewa gidan nan ba namu bane. To yanzu yake fada min wai ko dai ki sallameta da kanki ko kuma ya sakeki mu tafi mu bar miki gidan." Zulaiha ta rude "me yayi zafi Gidado har da zancen saki? Zinaru ki bashi baki don Allah." Asmau tace "wallahi karya take yi Zulaiha. So take ya sakeki ki bar musu gidan". Zinaru ta kalli Gidado "Ince dai kaga irin yadda take yi min. Ni bazan zauna a gidan nan ana wulakanta ni ba". "Zinaru kiyi hakuri indai Zulaiha ce yanzu zan saketa mu tafi" Yaransu duk suna kallo ita Asmau har ta soma jindadi sai kawai Zulaiha ta durkusa a kasa ta rike masa kafa tana kuka"ka rufa min asiri Gidado kada ka sakeni. Ina zani da yaran nan." Muhsin ya dagata tsaye "Umma kawai ki bari ya sakeki kema kya huta da duka da wankin amai. Dama don ke kike yi ne nake tayaki amma daga yau sai muga mai wanke masa" Bakin Muhsin din ta daka "waye ya saka bakinka. Ku bar wurin nan kafin na bata muku rai." Suna tafiya ta cigaba da rokonsu shi da babarsa. Zinaru ma tasa kukan karya ita dole su bar gidan. Ganin haka Asmau tace "indai saboda ni ne to in sha Allah da safe zan tafi. Zulaiha ki tuna da gatan da Allah Yayi miki ki koma gaban iyayenki. Gobe nima gidanmu zan tafi na roki nawa iyayen gafara". Daga haka ta bar wurin. Wannan wane irin so ne Zulaiha ke yiwa Gidado. Tausayi take bata don wannan ba karamar jarabawa bace. Mutum ya mayar da kai bolarsa amma ka kasa rabuwa dashi. Da kuka Zulaiha ta biyo bayan Asmau."kiyi hakuri Asmau ki zauna gobe zan sake rokonsu." "Zulaiha a kaina bazan so kiyi ta zubar da mutumcinki a gaban su Humaira ba. Ni dai shawarata ki koma gida ki roki gafarar su Inna". Zulaiha tayi shiru. A yadda zuciyarta ta karaya bata jin zata iya zuwa gaban iyayen da ta yiwa rashin kunya harda kaisu kara. ***** Karfe goma na safe Asmau ta gama hada 'yan kayanta da na Amatullah. Tayi mata wanka suka shirya tafiya. Daga kan Humaira har Ali kuka suke yi basa son tafiyarta. Itama kukan take yi amma gara ta koma gida. Kewar iyayenta ta dameta gashi duk inda ta zauna sai wani dalili ya koreta. Kamar bazasu rabu ba ita da Zulaiha kowa kuka ta rike hannun Amatullah suka fita. Tasha suka je bata dade ba motar Kano ta cika suka fito. Sunyi tafiya mai dan nisa sun wuce wani gari Saminaka ba jimawa suka ga wani mutum yana daga hannu alamar neman taimako. Gefensa mace ce babba da dogon hijab sai wata 'yar budurwa da bazata kai shekara ashirin ba. Dreban farko kamar kada ya tsaya sai kuma yaji tausayin dattijuwar suka tsaya. Motarsu ce ta lalace ga makanike yana dubawa amma yace injin ya buga sai an sauke shi. Su Asmau suka marmatsa matar da yarinyar suka shigo. Aka bar dreban da makanike. Sallama tayi musu suka gaisa tare da yi musu godiya. Ta kalli Amatullah da ke zaune a cinyar Asmau tayi mata murmushi. "Yan mata yaya sunanki" "Safinatu Abubakay. Amma Ummina Amatullah take ce min ko Ummi" Asmau tayi dan murmushi kawai. Fargabar zuwa gida ce fal a zuciyarta. Ita kuwa dattijuwar tace "Safinatu Abubakay ko Abubakar" tana yar dariya. Amatullah tace "Abubakay nace ba Abubakay ba" Mutane da yawa a motar sai dariya. Can ta dan taba matar nan "kema aljannah zaki je? Ni da Ummi can zamu wurin Babana. Ban taba ganinsa ba, Zinayu zai zane saboda tana duka na." Asmau ta dan kai mata duka saboda suruta sannan ta share hawaye. Matar nan tana kallonsu sai taji tausayinta ya kamata. A hankali yadda Asmau zata ji tace "Allah Ya jikansa" Asmau ta dago kai tace "Amin" wani hawayen yana fita a idonta. Sun iso Kano garin da hadari ga kura. Tana kokari daukar kayansu ne ta ga Amatullah ta dafe kirji numfashi baya sauka. A gigice ta saki jakar ta rungumota tana kuka. Yau kam ta tabbatar asthma gareta saboda yadda take kokarin numfashi yaki sauka. Wannan matar da wasu maza suka taho wurinta. Dreban da yazo daukar matar yana zuwa tace Asmau ta tashi su tafi asibiti. Kuka take yi kawai ga Amatullah ta sandare. Wani asibitin kudi suka je aka karbi Amatullah. Tana ji matar tana waya tana sanar da wani inda suke. Bayan kamar awa daya an samu Amatullah ta dawo hayyacinta suna wani daki Asmau sai godiya take yiwa matar taji an turo kofar dakin tare da sallama. Wani daddadan kamshi ne ya mamaye dakin kafin ta kula da mutumin da ya shigo cikin shigar sojoji masu babban mukami. Amatullah dake kwance ta tashi zumbur tace " Ummi wannan ne baban nawa?". ABINDA AKE GUDU🙆🏽29 Batul Mamman💖 Dan tsayawa yayi yana kallon kyakkyawar yarinyar. Tana daga zaune harda ware hannuwa ta dan bata rai "Baba bazaka yi min oyoyo ba? Nima bazanyi maka ba. Shine ka taho aljannah ka barmu ni da Ummi." Asmau kunya ta isheta ta kai hannu zata hana Amatullah sai matar ta girgiza kai. Taku yake mai cike da kamala da kuma kwarjini ya karasa daya barin gadon ya zauna yana murmushi. Asmau ta kasa daga ido ta kalle shi. A kan gadon ya zauna ya janyo Amatullah ya dorata akan cinyarsa. "Oyoyo baby din Baba. Kiyi hakuri bazan kara tafiya na barki ba kinji" Amatullah ta kankame shi ya dago kai ya kalli mahaifiyarsa yana murmushi. Juyowa yayi inda Asmau take zaune suka hada ido ba shiri ta kara sunkuyar da kanta. Mutumin ba karamin kwarjini yayi mata ba. A kalla zai kai shekara arbain. Kayan jikinsa sun kara masa kyau. Shi kuwa mayar da hankalinsa yayi ga Amatullah yana shafa mata kai. Girmansa da matsayinsa bai sa ya kyamaceta ba. Muryarta ya sake ji tace "Baba idan anje aljannah ba'a zuwa gida ne. Kullum ni da Ummi bamu ganka ba. Kuma Zinayu sai tayi ta dukana baka zuwa ka yama min". Sake hada ido suka yi da Asmau ya kula da kwallar da ta cika mata ido. Wani tausayinsu ne ya shige shi a lokaci daya. Ko ba'a fada ba yasan baban yarinyar nan ya rasu. Wannan ne dalilin da zaisa yarinyar ta rinka ambaton an tafi aljannah an barsu. Tana daga jikinsa yace "daga yau duk wanda ya sake tabaki sai na rama miki

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});