Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 76

Chapter 76

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Idonsa kyam a bakin kofa har Asmau ta fito. Ji yake inama dai anyi auren. Yayi kewarta sosai, ga wani haske da kyau da ta kara saboda mayuka da sabulun gyara jiki da Zubaida ta hada mata da kanta. Itama ganinsa ba karamin dadi yayi mata ba. Tana zama yace "Yi a hankali kada na narke da wannan kallon da kike yi min" Sam ta kasa boye murnarta shiyasa yake ta tsokanarta. Da ta gaji da kunyar ta soma ramawa. Yaci abinci ya kuma yaba da iya girkinta. Daga nan ne suka dasa hira har ta fada masa cewa ita dasu Umma zasu je Azare da Jos nan da sati daya. "Wannan tafiyar dani za'ayi in sha Allah. Dole naje har gida na godewa mutanen da suka taimaka wurin kare min martabar iyali." "Kuma har gidan Uwargida zamu je. Umma tace dole Zubaida ta ga mahaifiyarta" "Tabbas uwa komai munin halinta ba'a canja mata suna. Kila kiga rabon shiriyarta ne idan taga 'yarta tayi aure har da 'ya'ya. Ki fada min da wuri ranar da aka yanke yin tafiyar sai na shirya da wuri." Ta danyi ajiyar zuciya "Yaya Qasim ma yace zashi" Murmushi Jikamshinta yayi "Matar Jikamshi bazan taba rabaki da Qasim ba. Ina son halayensa kuma nasan mutum ne nagari. Ko jiya munyi waya dashi. Yasan Asmau matar Jikamshi ce wannan ya isheni kwanciyar hankali. Ke dai Allah Ya kaimu muje mu dawo a fara biki " ABINDA AKE GUDU🙆🏽51 Batul Mamman💖 Shirin tafiya sosai suke yi. Umma ta nemi Shemau da Jafar su kawo abinda ya sauwaka wanda zasu kaiwa mutanen Azare da Jos tsaraba. Duk da bata san Zulaiha ba amma ta yaba da taimakon da tayiwa Asmau. Sune suka rufawa 'yarta asiri ba don haka ba Allah kadai Yasan irin rayuwar da zata tsinci kanta a ciki yanzu. Shemau dai katan din taliya hudu ta kawo da maggi. Shi kuma Jafar galan din mai da katan din macaroni bibbiyu. Suna zaune a falo ana ganin kayan tana saka musu albarka. Idon kuka sai da tayi sana'ar tata kafin tayi godiya. 'Yan uwanta sun rufa mata asiri. Bata san mata nawa bane irinta a duniya wadanda kyama da hantara ta dangi ta kara tura su ga aikata sabo. Umma tace "na bawa Yassar ya siyo min buhun shinkafa biyu sai a bawa su Rashida daya ita ma Zulaiha daya." Asmau ta kara yi musu godiya "nima zan duba cikin kayan da kuka bani wanda ban dinka ba na daukar musu." "Hakan yayi kyau" inji Hajjo "kai Yassar ina naka ne? Ka zauna sai washe baki kake yi ban ga wani abu daga gareka ba" "Hajjo ni da ban fara aiki ba ina ni ina gudummawa. Ai ma na kyauta tunda zan tuka mota." Sai ya kara fadada murmushinsa "ashe da Yayanmu za'ayi tafiyar." Shemau tace "haka Umma ta fada min. Ni fa har kunyar Qasim nake wallahi. Nutsuwarsa tayi yawa. Gashi dai bashi zata aura ba amma ko kadan bai bari hakan ya zama sanadiyar bacin zumunci ba" Yassar ya dan tabe baki "au shima zuwa zaiyi? Ni da mutumina nake yallabai baban Amatullah" Umma ta rike haba "oh ni Bara'atu, nagode Allah a namiji kazo Yassar da ina tsammanin sai kunyi fada da yayarka. A take takenka da gani zaka iya kwacen saurayi. Idan Ishaq yazo gidan nan aka yi rashin sa'a kana nan kayi ta rawar kafa kenan. Jiya ina jin ku kana mita wai Asmau taki fitowa da wuri" Dariya suka yi, Yassar ya sosa keya "wallahi Umma burgeni yake yi. Nifa gaskiya idan an gama bikin nan zan nemi short service nima na zama soja. Baki ga ba idan yana tafiya ko magana....kai" Hajjo tace "anya Bara'atu kin tabbatar yaron nan namiji ne ba mata maza ba?" Su Jafar sai dariya Yassar ya tashi yana tura baki. Shi ba'a kyauta masa ba. Yabonsa fa kawai yayi saboda ya burge Asmau. Da taga anyi masa taron dangi sai ta koma bayansa tana kare masa. Yace "rabo dasu sai sun ga matar da zan aura ma sis. Kowa sai ya yaba harda tsohuwa mai ce min mata maza" aka sake dariya. ****** Lokacin da Col. Ishaq ya fadawa Hajiya zaiyi tafiyar nan dasu Asmau ta dage itama sai taje. "Ke da kike fama da kafa Hajiya" "Kada kaga laifina. Ba wai na karyata abubuwan da Asmau ta fada mana bane amma ance gani ya kori ji. Kai sonta kake da aure ni kuwa son 'ya nake mata. Ina so idona ya gane min inda ta rayu kafin haduwarku. Ina son samun hujja ga mutanen da tuni suka fara kawo min sukar auren nan. Da yawa cewa suke karuwanci tayi lokacin da ta bar gidansu. Bazan tura kowa a dangi ba bare a sami na gutsiri tsoma. Kai dai kawai ka hadani da dreba idan motarka ta cika" Ji yayi jikinsa yayi sanyi. Mutum ba'a iya masa. Mahaifiyarsa kuma da gaskiyarta. Da yana da yayye kila su zata wakilta tasan bazasu yi mata karya ba. Kuma gara taje din akan ta tura wani. "Shikenan Hajiya Allah Ya kaimu. Bilkisu sai ta koma gidan Safiyya ko su Dahiru" "Tare zamu je kasan rabonta da gida tun haduwarmu da Asmau. Ita ma gara taje ta kwana biyu kafin bikin tunda ta gama jarabawa" Da ya kira Asmau ya fada mata ko kadan bata nuna damuwa ba. Har zuciyarta dadi taji ko babu komai idan akwai wani zargi da yake ransu zasu ganewa idanunsu cewa ba karya tayi ba. Ranar da zasu tafi sammako suka yi. Yaran Shemau duka ta kawosu gidan Umma zasu zauna da Amatullah da Hajjo. Asmau da ita taso tafiya Shemau tace gara ta barta ta fara sabawa da rashin ganinta saboda idan anyi biki sai kamar bayan sati biyu ko uku za'a kawo mata ita. Ta dai amince don babu yadda zatayi ne. Basu saba rabuwa da juna ba. Wani abin ma sai sunje kwanciya ta mayar da kanta yarinya ta biyewa Amatullah suyi ta hira tana sauraron shirmenta. Burinta ta dasawa kanta babban matsayi a zuciyar Amatullah yadda nan gaba yarinyar bazata nuna mata kyama ba idan taji tarihin haihuwarta. Soyayya kuwa zata nuna mata hadda wadda take tunanin da Abubakar yana raye shima zaiyiwa 'yarsa. Allah Sarki bai ma san da cikin ba bare haihuwarta. Sun gama loda kayansu a motoci aka fara shiga. Asmau, Bilkisu da Zubaida suna motar Jafar da yaran Zubaidan. A motar Umma kuma kawu Garzali ne a gaba Yassar zai tuka. Baya ita da Mama ne. Shi kuma Col.Ishaq drebansa ne zai tuka su. Yana gaba a baya kuma Hajiyarsa da Shemau. Tun zuwansu gidan ya samu Asmau ta dan fito kafin a fara shiga mota "yanzu ina kallo zamu je wuri daya amma ba motarmu daya ba? Wannan tsarin baiyi ba gaskiya ki dawo motarmu Shemau ta koma ta Jafar. Wa zan rinka satar kallo ta madubi" Zaro ido tayi "sai na zauna kusa da Hajiya don rashin kunya kai kuma kana kallona?" Yace "to meye a ciki? Naga auren danta zakiyi karewa." Ta kawar da kai tana murmushi "ni dai kayi hakuri don Allah kada a fito ka fara cewa na dawo motarku. Kada ka sani jin kunyar da ban shirya ba". "Dama kina

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});