Chapter 62
Chapter 62
basu tausayi. Ace har rubutun cikin waya ya isa ya sa mutum aikata zina. Abin da ban tsoro da firgici saboda babu wanda ya isa ya tserewa kaddara sai dai komai akwai sila. Hajiya Lubabatu tace tunda zata je dubo Amatullah tana so dukkansu suyi mata rakiya. Kukan Bilkisu suka ji Hajiya ta tashi da kanta sai dai kafin ta fito Bilkisu ta koma dakinta tana kuka. Bata taba sanin wannan labarin ba. A iya tunaninta baban Amatullah ya rasu ne ko ya saki Asmau. Tsoro ne ya kamata saboda akwai wani saurayinta da suke chatting a facebook. A hankali ya fara sako mata zantukan banza tun bata amsawa har ta dan fara sakewa yanzu. Wai har ya iya tambayarta ta kwatanta masa kayan baccinta da daddare. Tayi saurin dafe kirji, yanzu idan da abin yayi nisa kila itama ta shiga sahun masu bawa samari jiki. Kuka take sosai tana tausayawa Asmau kuma har ranta tana fatan Uncle Ishaq ya aureta ko don ya rufawa rayuwarta asiri. Sabon saurayin da suke dan satar kallon juna dashi ta kira a waya tana sheshshekar kuka. Numbar ma a wayar Uncle ta dauka batare da saninsa ba. Da sallamarsa ya dauka cikin muryar da ta dashe da kuka tace "Yassar ne?" ABINDA AKE GUDU🙆🏽45 Batul Mamman💖 Mamaki ne ya kama Yassar, kamar ya san muryar amma bashi da tabbas. "Da wa nake magana don Allah?" "Bilkisu ce" Tsorata yayi, shima yana neman numbarta amma yanzu da ta kirashi da alamun kuka sai yaji hankalinsa ya tashi. "Bilkisu me ya faru?" To me kuma zata ce masa? Tausayin kawunta take yi amma tana tsoron yi masa shishshigi. Uncle Ishaq yana da dadin sha'ani amma babu mai son ganin bacin ransa. Fasa maganar tayi na son ta roke shi ya lallaba yayarsa kada ta ki Uncle dinta tace "babu komai, anjima zamu zo duba Amatullah" tayi masa sallama ta ajiye wayar. A ransa yasan don zasu zo ba shine dalilin kiran ba. Tashi yayi ya shirya ya tafi asibitin. Zai jira su zo ya sami damar tambayarta. Ko dai ta lura da yawan kallonta da yake yi ne? Yayi murmushi, tun zuwansa gidansu na farko ranar da kare ya biyo Asmau ya fara jin wani abu game da Bilkisu. Sai dai duk hayaniya ta Yassar bai taba yin budurwa ba. Ta nan bangaren tsoro ne dashi kamar farar kura. ***** Col. Ishaq na shiga dakinsa ya fada kan gado ko takalmi bai tsaya cirewa ba. Kansa ne yake wani irin ciwo kamar ana buga masa kusa. Ga zuciyarsa ta gama tafasa da bacin rai. Wai yau shine kannensa har da Mussadiq dan karamin cikinsu suke fada masa magana son ransu. A gidansu akwai tsari na girmama na gaba sosai. Sun tashi da so da kaunar juna. Lalurar kowa tare suka haduwa suyi maganinta. 'Ya'yan Ismail biyar duka maza karamin ma bai shekara ba. Amma saboda yadda suke bashi girma duk shi yake sakawa yaran suna. Haka yaran Dahiru guda uku. Gidansu gwanin sha'awa baka ce babansu ya dade da rasuwa ba. Amma yau akan auren Asmau duk sun ture wani girmamawa da shakuwa kowa ya fadi son ransa. Da akanta kadai suka tsaya ya tabbatar da har yanzu yana dakin suna cacar baki. Sai gashi saboda irin rayuwar Asmau ta baya har gori Ismail yayi masa. Gori da abinda yafi so a rayuwarsa, haihuwa. Shi da kullum yake kwantarwa da yayansa hankali. Kafin rabuwarsa da Badariyya ma yaransa biyu manyan a wurinsa suke. Dumi yaji a idonsa yayi saurin mayar da hawayen dake neman zubo masa. Duniya ta Allah ce kuma ba wurin tabbatar bayi ba. Da ace babu lahira sai yace rayuwar Asmau ta wuce abinda ake gudu domin komai daren dadewa sai an ambaceta ko 'yarta a matsayin mazinaciya ko 'yar zina. Ya tabbatar ko shugabar malaman duniya Asmau ta zama sai kaji mutane suna cewa "Wance kamar ba ita ce tayi cikin shege ba" "Ji yadda take nuna mana ita ta Allah ce kamar bamu san tarihinta ba" Amatullah kuwa ita ma bazata tsira ba. Komai kyawun rayuwarta sai an ce "kaga wance kamar ba shegiya mara uba ba" "wance fa da kuke gani babu aure aka haifeta" Irin haka da maganganun da suka fisu zafi mutane zasu fada a kansu. Babu ruwan kowa da yaya tsakaninta yake da Allah. Shin ta tuba ko kuwa. Zina ta zama mugun tabo mara gogewa. Tashi yayi ya zauna tare da daga hannuwansa sama. Hawayen da baya son yi ne suka zubo masa "Ya Allah Ka karbi tuban baiwarKa Asmau da sauran al'umma da suke cikin hali irin nata. Allah Ka basu rayuwa mai albarka su ji dadin tuban da sukayi bisa laifukansu, Ya Allah Ka bata miji nagari wanda zai zame mata alkhairi kuma mai wanke mata bacin rai da bazata taba dena fuskanta ba a dalilin kuskurenta na baya. Ya Allah Ka karemu da sauran musulmi daga fadawa alfasha kowace iri ce. Amin" Sai yanzu yaji saukin kuncin zuciyarsa ya tashi zaiyi wanka kafin a kira magariba. Abu daya ne a ransa yanzu, shine hakuri da Asmau da zaiyi. Ba karamin so yake mata ba amma dole ya barta ta auri wanda zata iya haihuwa dashi. Zafin soyayya ya rufe masa ido har ya manta yana da nakasa a rayuwarsa. Tunda baya haihuwa bazai cutar da kuruciyarta ba ta zauna da 'ya daya. Wanka ya shiga ya fito ya sanya riga da wando na yadi mara nauyi. Ya saka hula kalar adon rigar ya sha turare sai gashi ya fito a Jikamshinsa. Idan ka ganshi bazaka ce yana da damuwa ba saboda tunda yayi adduar nan babu abinda yake sai tasbihi ga Allah. Wannan ne ya saukaka masa damuwarsa yaji kwarin gwiwar niyarsa ta rabuwa da Asmau idan suka koma gida. Kafin ya fito text dinta ya shigo wayarsa. Yaa budewa yaga ta rubuta _missing Jikamshina_. Wani sabon sonta yaji ya ratsa shi. Kasa yi mata reply yayi ya tura wayar a aljihu. Yana fitowa ya tarar da kannensa jugum a falo domin kuwa Hajiya tana gama basu labarin Asmau tace su fice mata daga daki. Da ya fito duk da ransa babu dadi haka ya basar ya dubi mazan "Kuzo mu wuce masallaci" Suka tashi jiki a sanyaye. Mami tace "Yaya don girman Allah kayi hakuri da abinda Ismail ya fada. Wallahi duj don bama so ka auro wadda zata gurbata mana dangi ne" Suma sauran suka soma bashi hakuri. Ismail kuwa ko kallon yayansa ya kasa yi. Murmushi yayi wanda dukkansu sun san irinsa yake idan ransa ya baci "Magana ta wuce, bazan auri Asmau ba kamar yadda kuke so. *Amma ba don kun nuna rashin amincewarku bane, don baku isa ba*. Saboda kaddara ta fada mata ba zan ce sai na aureta ba duk da ni din bana haihuwa ko Ismail?" Ismail ji yayi kamar yayi kuka. Idanunsa tuni sun canja launi. Yayansu yana da kirki matuka, bai san yaya akayi shaidan yaja shi yayi wannan katubarar ba. "Yaya ka yafe min, wallahi Hajiya yau har zagina tayi bayan fitarka. Yanzu ma cewa tayi zamu rakata asibiti duba yarinyar Asma'un daga nan kowa ya fice mata daga gida. Hatta Mami Hajiya tayi rantsuwa bazata kwana a gidan nan ba." Col.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103