Chapter 90
Chapter 90
bai dade da tashi ba. Yayi murmushin keta ganin duk sun daburce da ganinsa a haka suka gaisa, manyan cikinsu ma sunji kunya. A ransa yace gobe ma ku sake zuwa kallon kwakwaf. Basarwa yayi yace "tana shiryawa ne bari na kirowata" Kafin ya karasa shigewa korido din ya soma jin suna kuskus ana cewa dama ba yanzu suka zo ba sai anjima. Dakin Asmau ya shiga tana kokarin zuge zip din riga. Tana ganinsa ta juya kada ya ga bayan ya shigo ya rungumeta ya zuge mata zip din yace "sarkin kunya kin gama shiryawa, muna da baki a falo" A rude tace "baki kuma, yaushe suka zo. Ban duba kitchen din ba ko akwai wani abu mai sanyi da zamu bawa baki" tunanin yadda zatayi ta soma. Dama ransa ya baci da zuwan bakin ganinta yanzu ya sa ya dan manta. Gashi yanzu duk an ruda masa mata. Ita ma bata gamawa sanin kan gidan ba an zo mata mutane sunfi goma. "Shiyasa tun dazu da suka zo nace kada a bude gate din" "Sun dade da zuwa? Meyasa kace kada a bude yanzu sai ace laifina ne" A zatonsa zata ji dadin yadda yayi bai san mu mata mun saba da irin wannan bakin na bayan kai amarya ba. Idan ba'ayi sa'a ba ma kawayenta ke zuwa jin ya aka kwana. Amarya mai bakin aku tayi ta bayani dalla dalla. Gani yayi duk ta damu da bakin da bata san ko su waye ba yace "nayi miki gwaninta shine kike bata rai. To kije wurinsu ina daki idan kun gama" Asmau taji wani iri. Maganarsa kadai ta sanar da ita ransa ya baci. Ya juya zai fita ta riko hannunsa "kayi hakuri Jikamshina" Ya danyi murmushi "babu komai akwai lemo a fridge kuma ina jin da cake sai ki basu" Fita yayi ya barta ta rasa yadda zatayi. Gashi yayi fushi sannan ga bakin da idan bata je ba zasu tafi da ita a baki. Haka ta yafa mayafi ta fita wurinsu. Su a takure ango ya basu kunya ita kuma ta kasa sakin jiki saboda kunyar an shanyasu a waje ga Jikamshinta yana fushi. Basu dade ba suka tafi ko irin leken gidan amarya basuyi ba tunda ansan yana gidan. Suna tafiya ta koma dakinta ta canja kays zuwa wasu riga da siket da suka fiddo da jikinta sosai. Tasha turare da kwalliya ta tafi bawa angonta hakuri. Zaune ta same shi akan wata doguwar kujera ta dakin ya gama shiryawa yana waya da alama Mami ce. Tunda Asmau ta shigo ya ganta da kwalliya da kamshin da take zubawa ya nemi fushinsa ya rasa. Hannu ya mika mata alamun ta karaso. Tana ji ya sallami Mami ya dubeta "apology accepted" Tace tana jindadi "tun kafin na bada hakurin" "Ganinki ya kori fushin amma ki sani bazan yarda da bakin nan ba. Sati biyu kawai aka bani a wurin aiki. Bazanyi sharing dinsu da bakin nan ba. Anjima zamu hada kaya gobe in sha Allah zamu je Yankari Game Reserve" Ta sunkuyar da kai ta kara bashi hakuri sannan tace "ko naje na fara hada kayan yanzu?" Ya ja hancinta "yanzu kuma ai lok[truncated by WhatsApp] ABINDA AKE GUDU🙆🏽56 Batul Mamman💖 Bai san irin yadda take jin kunyarsa ba. Ta rufe ido tana noke kai. Jin kanta take a takure kamar tayi tsuntsuwa ta gudu. Dama ya tabbatar da wuya yaji tayi magana. Duk da burinsa kunyarta ta ragu idan suna tare amma ya lura kamar karuwa tayi. Matsowa yayi daidai kunnenta yace "zaki iya tashi muyi sallah?" A hankali ta gyada masa kai sannan tace cikin wata karamar murya "asuba tayi?" Mamaki tayi domin gani take kamar yanzu ta rufe idonta ta fara bacci. Kamar yasan me take tunani yace "kina mamaki ne? Bayan kin cinye daren da kuka da ....." Da sauri ta rufe masa baki kafin ya fadi abinda yayi niyya. Ai kuwa ya ciji tafin hannunta a hankali ta cire shi daga bakinsa ta saki kara tana kwabe fuska zata yi masa kuka. Dariya ya fara da yaga da gaske kukan zata yi harda guntun hawaye ya kama hannun yana hurawa. "Yi hakuri my darling Asmau, matar soja bata kuka. Matar Jikamshi kuma ba raguwa bace" Kyale shi tayi yana rarrashinta ta daidaici kafadarsa sai saukar cizo yaji. Ta soma dariya da taga ya shige shi sosai ai kuwa suka fara kokawa yana cewa sai ya rama. Ga tsoron kada ya rama din da gaske ga dariya tana cinta. Tun yana zai rama har ya koma yana kallon yadda take dariya da hawaye a idonta. Ji tayi ya rungumeta a hankali "Allah Yayi miki albarka Matar Jikamshi. Yadda kike faranta min nima Allah Ya bani ikon yi miki haka." Nutsuwa tayi ta dena dariyar tana cewa amin ga adduarsu sai ga kiran assalatu. Col. Ishaq yayi saurin tashi "Kinga zaki sa mu makara ko? Na tashi da niyar nayi shirin zuwa masallaci sai na tasheki ne" "Ka tashi dai kana cin zalina daga zuwana gidanka" "Haka ma kika ce? Ji yadda kika cije ni fa. Ki zauna cikin shiri idan na dawo zan rama." Sai da ya fito daga bandaki ya saka doguwar riga zai tafi masallacin dake bayan layinsu yazo inda take kwance don bazata tashi yana dakin ba yace "ki kular min da kanki sai na dawo" ya kusa bakin kofa yaji tace "Allah Ya tsare min kai Ya dawo da kai lafiya" Yaji dadin adduar sosai har bazai iya kwantatawa ba "nagode Matar Jikamshi amma hakan bazai hanani ramawa ba idan na dawo." Daga haka ya fita itama ta tashi ta kimtsa tazo ta fara nafila. Bayan ta idar da sallolinta zama tayi tana ta mika godiyarta ga Allah. Hakika ta sami babban rabo da Allah Ya nufeta da yin aure duk da abubuwan da suka faru a rayuwar ta. Mata irinta nawa ne suke cikin tashin hankali da muguwar kyama. Kuma wasu da gaske sun tuba amma hakan bai sa mutane raga musu ba. Ta san dai komai bazai taba gogewa kamar bai faru ba amma duk da haka auren da tayi yafiye mata komai. Ta auri irin mijin da kowace mace zata so kasancewa dashi. A take ta yanke shawarar neman izininsa na yin azumi duk ranakun litinin da alhamis domin neman karin kusanci da Allah da kuma tuba. ***** A nan ya dawo ya sameta tana kuka da addua. Ya zauna a gefenta suka karasa tare sannan ya kuma bata baki akan ta cigaba da hakuri da rayuwa. Daga hira ya dawo da maganar rama cizo. Ta soma bashi hakuri yace bai san zance ba. Daga baya yace "nuna min inda bakya so a jikinki sai na rama a nan" "Gaskiya ina son ko'ina" Dariyar mugunta yake mata don yaga tsoro take ji. "To bari na saukaka miki. Rinka nuna min inda kika fi so, duk inda kika bari karshe shine ba kya so din. Sai ki bar min nayi yadda na ga dama". Asmau ta hau tunani gashi ya kureta akan gado. Duk inda tasan ana jin zafin cizo ta fara lissafawa a cikin zuciyarta. Yace ita yake jira tace "to bakina nafi so" Col. Ishaq ya dan bata rai "ni kuma nan ne bana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103