Chapter 9
Chapter 9
Sun tausayawa Umma sosai Baba yace zai sa a bada cigiya a kafafen yada labarai. ***** Shiru Asmau na zaune a cikin mota banda addu'a babu abinda bakinta yake ambato. Tana daga gefe ta ja hijab dinta ta rufe rabin fuskarta. Sunyi nisa sosai taji wani daga gaba yana tsaki da zage-zage. Na kusa dashi wanda da alama abokinsa ne yace "ya dai kake tsaki kai kadai Bala?" Wanda aka kira Bala ya nuna masa wani hoto a wayarsa "ka duba don Allah yadda ake rashin imani a duniyar nan. Dubi fuskar yarinyar nan kai kace idan aka saka mata hannu bazata ciza ba...." Hankalin sauran 'yan motar ya koma jin jawabin Bala. Shi kuwa ya cigaba da magana cikin bacin rai "....wai yarinyar nan ce ranar aurenta ta kashe mijin saboda ya gano tana da ciki kuma yace ba nasa bane. A cikin gidansu fa aka tsinci gawar tasa a bandaki ta buga masa guduma a keyarsa bayan an kai ta, ance a halin yanzu tana hannun hukuma. Shegiya Allah Yasa su harbeta ma" A hankali Asmau ta daga kai ta kallo hoton da duk 'yan motar sai da suka karbi wayar suka gani. Gabanta ne ya fadi sosai da taga hotonta ne. Cikin dan lokaci an canja labarin gabadaya. Ba karamin mamaki tayi ba da taga hoton da ita kanta yanzu bata dashi a wayarta. Mutane kamar jira sukeyi abu ya faru sai ayita yayatawa ana ta kara gishiri da maggi a zancen. Kafin ka ankara zancen ya sauya daga ainihin yadda yake. Shiyasa ake so mutum ya kiyaye me yake saurin turawa mutane a kafafen sada zumunta (social media). Sake rufe fuskarta tayi don kada su ganeta. Wani daga kujerar baya yace "nima ina da wani hoton nata daban da wannan harda mijin" wayar tasa ya miko shima da hotonsu na dinner ita da Abubakar. Mutumin ya cigaba da cewa "ni a yadda aka turo cewa akayi kafin a daura auren aka tsinci gawarsa a bandakin hotel shine aka kalawa yarinyar. Ana tunanin wata yayiwa ciki ta kashe shi." Har zuciyarta zancen yayi mata daci sai dai kafin a gama ganin hoton wata tace itama taji labari amma cewa akayi rasuwa yayi a gidansu kuma a ranar aka gane amarya nada ciki. An rasa gane ko cikin waye nasa ne ko na yayansa don amaryar tana bin maza. Duk masu bayani na matar ne yayi kama da gaskiya. Duniya kenan, kowa da abinda zai ce ba tare da yasan gaskiyar lamari ba. Asmau tana ji motar ta kaure da tsine mata ita da Abubakar ga wadanda suka yarda ciki yayiwa wata. Rufe ido tayi kamar mai bacci tana kukan zuci har suka shiga tashar Azare ta jihar Bauchin Yakubu. ABINDA AKE GUDU ๐๐ฝ7 Batul Mamman๐ Ba karamin gudu Qasim yayi ba a hanya. Allah ne Ya kawo shi Shanono lafiya. Kai tsaye gidansu ya nufa. Gida ne irin ginin gargajiya amma yasha gyara ciki da waje ga sabon fenti. Duk shiririta irinta Qasim baya wasa da lamarin iyayensa. Shiyasa albashinsa duk wata a hidimar gidan yake tafiya ko tunanin aure baya yi duk da shine babba. Kanwarsa daya Jamila wadda ada yaso Abubakar ya nemi aurenta. A soro ya tarar da mahaifinsa Mal Musa zagaye da dalibansa samari da magidanta wurin su goma. Da dai-dai Qasim ya gaisa dasu sannan ya gaishe da mahaifinsa. Yana durkusawa gaban Malam sai hawaye ya kufce masa. Ganin haka daliban suka tashi gabadayansu suka yi sallama da malaminsu. Hankakin Mal Musa a tashe yace "Baba wata matsalar ka sake samu a wurin aiki ne?" Qasim ya girgiza kai. A lokacin Jamila ta fito zata je makota inda Inna ta aiketa. Ganin yayanta yana hawaye yasa ta koma ta sanar da Innar abinda ta gani. Kokarin tashi tayi da kafarta daya da tasha dori sakamakon karayar da ta samu a kafar bayan ta zame a bandaki. Kafadar Jamila ta dafa ta kaita soron. Suna shiga suke jin Qasim yana sanar da mahaifinsa mummunan labarin da ya dawo dashi gida. Inna ta saki kuka hade da salati "Abubakar din da na sani ko dai wani kake nufi Baba". Ido fal hawaye ya fada musu abinda ya sani dangane da rasuwar amininsa. Inna da Jamila sai kuka. Ba tun yau Abubakar yake dan gida a wurinsu ba. Yadda Qasim ke zuwa Kano hutu haka Abubakar yake zuwa Shanono. Lokacin da Mal Musa ya sami mutuwar barin jiki ba karamar hidima iyalin Kwamishina Adamu suka yi musu ba. Lalurar iyayensa da canjin aiki da ya samu yasa basu je wurin bikin ba. A can Kano kuma tashin hankalin cikin Asmau yasa basu tuna da sanar musu ba. Bayan sun gama koke-kokensu suka shirya duk da yamma tayi Qasim yasa kujerar guragun da ake tura mahaifinsa a ciki a bayan mota sannan suka kama hanyar Kano. Ana gab da magariba suka isa kofar gidan Kwamishina. Maigadi ya sanar dasu cewa gabadaya 'yan gidan suna makota wato gidansu Asmau. Gaba Qasim yayi da motarsa suka karasa can gidan. Ya taimakawa mahaifinsa ya fito jingine da jikinsa suka shiga gidan. Jigum suka tarar da Umma da Mama Yalwa kamar basu sami sabani sakamakon jin batun cikin ba. Baba Kwamishina yana gefe shi da Abdulhalim suna ta bige bigen waya. Kowa ka gani da abinda yake yi. Sallamar Qasim ta sa hankalinsu ya koma ga kofa. Kuka sosai ya zowa Mama saboda ganin Qasim. Shima bayan ya zaunar da mahaifinsa gabanta ya koma yana kukan. Mutuwar Abubakar ta dawo musu sabuwa. Da suka dan nutsu ne Qasim yace " Umma ina Asmau ne?" Kamar yace a fara wani kukan suka sake dasa sabo. A gigice yace " ba dai itama ta rasu ba?" Jafar ne ya bashi amsa da cewar ba'a ganta ba tun safe. Qasim ya share kwalla "amma me yasa Asmau bazata yi tawakkali ba. Ina ta tafi haka?" Boye- boye bashi da amfani shiyasa Shema'u ta sanar dasu abinda ya faru. Idan ma basu fada ba a waje wasu zasu fada musu. Labarin yayi matukar razana Qasim da iyayensa. Lallai iyalan biyu suna cikin tashin hankali. Jikinsa duk babu kuzari ya dubi wurin da Malam da Baba suke zaune "ko da ba a gabana akayi ba, ni shaida ne cikin Asmau na Abubakar ne." Mama ta dago jajayen idanunta tana kallonsa " Qasim abokinka fa ya rasu, yanzu ka kyauta kenan kana binsa da wannan mummunar shaida". "Mama na san inda yaje nima a ko wane lokaci zan iya tafiya. Fadin gaskiya shine adalcin da zanyi masa." Daga nan ya basu labarin abinda ya sani dangane da Abubakar da Asmau wanda babu wani mutum da ya sani. Shi kadai ne yasan wannan sirrin. Falon ya sake rudewa da kyar Baba da Malam suka samu aka yi shiru sannan suka ce a tashi ayi sallar magriba zasu karasa maganar idan sun dawo daga masallaci. ***** Tun kafin azahar mota ta sauke su Asmau a tasha. Kowa na ciki ya dauki kayansa yayi gaba, ban ita. Sai yanzu take tunanin inda zata je kuma bayan nan. Bata taba zuwa Azare ba kuma bata san kowa ba. Wurin da taga an kebe domin sallah taje tayi sallah sannan ta karasa wurin masu abinci ta sayi wake da shinkafa da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103