Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 87

Chapter 87

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Tana fitowa duk an ragu sai yayarta Shemau. Za'ayi sirri na 'yan uwa ta nuna mata inda ta ajiye kayan gyaran da aka bata a wata drawer "Don Allah kada ki rinka yi musu shan koshi. Komai sama sama yafi ko don kada ki sha wanda zai illata ki. Ga wannan kuma ki saka" Asmau ta karbi kunshin ledar da Shemau ta bata. Doguwar riga ce abaya amma ruwan madara. Rigar ta tsaru karshe da mayafinta. Bude baki tayi zata fara godiya da dan hawayenta Shemau tace "indai tayi miki kyau shikenan. kiyi sauri ki shirya kiyi sallah kada ango yazo kina daure da tawul. Mu zamu tafi ga Zulaiha nan da Walida sune kawayen naki dama. Sabira da mijinta bai kamata ta zauna ba." Shemau bata fita ba sai da Asmau tayi sallah ta shirya. Wani turare mai maiko ta bata ta fara shafawa kafin aje ga sauran. Kamshi ne zai tarar da Jikamshi. Bayan tafiyarsu daga ita sai su Walida suka dawo falo don ba'a son wannan zuwa har uwar daki da abokan ango. Alamun bude gate ya sa hankalin Asmau tashi. Mayafinta ta gyara kafin su shigo. Su hudu ne harda angon. Biyu abokansa da kaninsa Ismail. Bata iya ganin kowa sai muryoyi da take ji. Ba wasa suka tsaya yi ba nasiha ce dai da addua. Sai a lokacin taji muryar maigidan nata yace Amin. Daga nan suka tashi yace akwai dreba zai ajiye su Zulaiha. Abokin nasa mai dauko amarya yace shi zai je. Ashe Walida ce ta dauke masa hankali. Tana ji ya fita rakiya ta kasa bude mayafin bare ta tashi. Lokacin da ya rufe kofar gidan kuwa zuciyarta ba karamin harbawa take ba. Anyi an gama yau ga Asmau a matsayin matar Ishaq. Motsi da kamshinsa taji a kusa da ita ta sake kankame mayafin. Shiru bata ji ya zauna ko yayi magana ba. A hankali taji an bude gaban mayafinta ya shigo da kansa ciki. Ashe a gaban kafafunta ya durkusa. Zatayi baya yasa hannu ya zagayeta ga mayafinta ya rufe su sai kamshin turaruka da numfashinsu. Babu abinda zata iya yi sai kawai ta rufe idonta cike da kunya. A hankali yake mata magana "Kinyi kyau Matar Jikamshi, yau so nake kamshinki ya rikita ni shiyasa zanyi ta like miki" Sake runtse ido tayi tana jin wata irin kunyarsa tana karuwa a zuciyarta. Ya dago kanta tare da matso da bakinsa kusa da nata ga hancinsu yana gugar juna "Ko na daukeki ne?" A nutse ta bude ido suka sauka cikin nasa. Murmushi tayi masa yaji gabadaya ta hargitsa masa lissafi. Irin wannan farincikin a karkashin inuwar aure halattaccen zama kawai Allah Yake sako shi. Bai dena kallonta ba ya rike mata hannu suka tashi. Mayafin ya cire ya ajiye a kan kujerar ya karewa rigarta kallo. Shemau ta iya zabe. Sai a lokacin ita ma ta kula da kayansa. Yau ma harda babbar riga a shaddarsa ruwan madara kamar kayan jikinta. Hular kuwa a kasa ta ganta kusa da inda take zaune. Yana rike da ita har suka je dakinta. "Shiga ki jirani naje nayi wanka. Kunyarki nake ji da nace ki rakani. Amma kiyi alwala kafin na dawo" Yana kashe ido tana sunkuyar da kai. Sai da ta shiga ya wuce yana murmushi. ***** Da abin sallah ya shigo harda mayafinta na falo sanye da kayan bacci riga da wando. Ya shimfida musu abin sallar tana kallonsa sannan ya nuna mata alamun ta tsaya suyi sallah. Kira'ar Jikamshinta ta tafi da ita don nutsuwa da bawa harufa hakki. Raka'a biyu suka yi sai shafai da wutri sannan ya shiga jero addua da larabci kamar bazai dena ba. Bayan ya kai karshe suka shafa ya dawo gabanta ya dafa kanta ya sake wata sannan ya tashi zai nade abin sallar. Karatun Uwargida ta tuna ta dan matsa a kunyace ta karba ta ninke. Ya ji dadin hakan kuwa sosai. Fita yayi daga dakin ya dawo yace ta biyo shi. Falo suka koma ya ajiye mata snacks, nama, juice da youghurt. "Wanne kika so" Jikinta duk ya fara sanyi ta ce ta koshi. Yayi murmushi wannan salihancin duk zatayi ta gama ne. "Ni zanci kinga ya kamata ki zauna a kusa dani har na koshi ko" Tace "uhmm" kamar wadda ta tauna flagyl bisa kuskure. Centre table din na gabansa ta zagayo zata zauna a kusa dashi kawai ya janyota kan cinyarsa tare da yi mata rikon da bazata iya gudu ba. "kada kice min kunyata kike ji kin san ni dai bani da ita indai a kanki ne. Kema kuma haka nake so ki zama." Ta rausayar da kai gefe guda tana kokarin zillewa. "Idan ba kya so muci abincin sai mu koma inda muka fito ni bani da matsala." Tace "To bari na matso da plate din ni ina jin yunwa" Hancinta yaja yana dariya "ace sai da dabara zan samu kici abinci." Bayan sun gama ta kwashe komai ta kai kitchen din da bata gaji da gani ba tun da su Walida suka nuna mata. Da ta dawo ya kashe duk kayan wuta suka shiga ciki. Dakinta zata shiga yace "muje namu dakin ki saka masa albarka" "Brush zanyi" "Can ma akwai duk abinda zaki bukata" hannunta ya kama suka tafi. Ni'imtaccen kamshi da sanyi ne suka doki hancinta. Komai na dakin sabo ne. Dama dakuna hudu ne a gidan. Aka saka mata gado a biyu dayan aka mayar mata karamin falo. Nasa dakin ya dauki hankalinta. Ya shiga bandaki ta tsaya dube dube. Wani bakin abu mai santsi ta gani akan gadonsa ta dauka. Baki ta bude da ta gane ko meye. Rigar bacci ce mai kyau da ta dace da amare. Tana jin zai fito ta ajiye sai dai ya ganta. Ya zo ya rungumeta ta baya "rigar tayi miki kyau ko? Hmmm nifa ban ganewa kamshin nan naki ba. Ji nake kamar na mayar dake jikina" Asmau ta janye jikinta kai a kasa. Rigar ya mika mata yace taje ta shirya yana jiranta don yaga taki sakewa a nan. Idan ta wuce minti goma zai biyo baya. Dakinta ta koma tana mayar da numfashi kamar wadda tayi tsere. Sai juya rigar take yi a hannu. Karshe dai ta sake shiri ta saka ta dora zani ta fito. Daga bakin kofa ya tareta ya dagata sai kan gado. Sai dai kuma yana ajiyeta ta soma hawaye. Zuciyarta tayi mata nauyi sosai. A take ya rude yana tambayarta ko me ya sameta. Duk yadda zaiyi Asmau taki magana sai kuka har yaji babu dadi a ransa. A sanyaye yace "Kin tuna Abubakar ne? Addua ya kamata kiyi masa ba kuka ba" Tayi saurin girgiza kai. Idan ya tabata kuma jikinta rawa yake sosai. Ganin taki magana sannan kamar tana tsoronsa sai kawi ya kwantar da ita yaja bargo ya lullubeta tare da yi mata kiss a goshi "kiyi hakuri idan nayi miki abinda bakya so ne. Just sleep bazan dameki ba" Daya gefen ya koma ya zauna yana kallonta. Asmau ta juya baya tana kuka mai tsuma zuciya da tada hankalin mai saurare. Dole tayi kuka a wannan rana ko taji sauki a ranta. Yana gefe yana jin kukan har ransa amma ya rasa me take

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});