Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 3

Chapter 3

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tsakiyar kanta. Jinin Abubakar kuma? Abubakar din da ta tabbatar yana tare da abokansa yanzu suna shirin zuwa wurin reception din da zasuyi. Cikin rashin fahimta tace "wane irin jini? A ina kaga Abubakar din?" Umar yace "yana toilet dina ya suma". Mama bata jira ya sake magana ba ta fita daga dakin da sauri yana binta a baya. Matan dake cikin gidan suna ta tambayar abinda ke faruwa. Ganin basu tsaya basu amsa ba suka bi bayansu. A kofar dakin Umar suka tsaya ya saka mukulli zai bude kofar Abdulhalim ya shigo yana fadan Abubakar ya bar mutane suna ta cigiyarsa har Baba sai da yayi ta fada. Umar dai bai kula shi ba ya bude kofar Mama ta ture shi ta shiga da gudu. Inda ya barshi a kwance suka sake samunsa. Abdulhalim ya karasa gabansa da sauri yana tambayar Umar me ya faru. Da taimakon Umar suka dora shi a kan gado daga shi sai dogon wando a jikinsa. Mama ta fada kanshi tana jijjiga shi tana kuka. Matan dake kofar dakin suma suka soma kukan. Nan da nan aka kirawo 'yan uwansa mata. Abdulhalim ya kira wani abokinsa likita da yazo wurin daurin auren ya bukaci ya karaso gidansu da gaggawa. Dakin duk ya rude da kuka duk da har yanzu basu san ainihin me ya same shi ba. Sai da Abdulhalim yayi da gaske ya iya sawa suka fita. Cikin mintuna kadan likitan ya karaso. Yayi mamakin ganin angon kwance jini har ya soma jika zanin gadon. Umar ne yayi masa bayanin yanayin da ya tsince shi a ciki. Abdulhalim yace "bari mu saka shi a mota mu tafi asibiti. Bana so mutane su ganmu. Zanyi kokarin kawo motata baya sai a fita dashi." yana gama magana ya fita. Kabiru ya duba kan Abubakar inda ya fashe sannan ya taba kirjinsa da tsintsiyar hannunsa. A razane ya dago kai Mama ta kalle shi da jajayen idanu tace "ya cika ko?" Yadda ta tsare shi da idanu bai isa yayi mata karya ba. Sunkuyawa yayi ya sake bincika shi sosai sannan cikin murya mai rauni yace "Mama sai dai muyi hakuri....". A take ta zube a jikin Abubakar a sume. Su Suwaiba sai kuka suke yi suka dagata. Kabiru ya fara kokarin taimaka mata. Kuka kowa na dakin yake yi sosai. Tun kafin Abdulhalim ya karaso yaji sautin kukan ya shigo a guje. Umar ya fara hangowa durkushe yana kuka ya shigo ya tarar Kabiru yana danna kirjin Mama. Wani irin numfashi taja sannan ta bude ido da kyar. Mikewa tayi tana kuka ta koma bakin gadon inda har ansa gefen zanin gadon an rufe Abubakar. "Allah Ya jikanka Abubakar. Na yafe maka duniya da lahira. Allah Ya sa mutuwa hutu ce gareka." Ana amsawa da amin kuka yana karuwa. Duk dauriya irin ta Abdulhalim shima kukan yake yi ya kama hannun Kabiru suka fita. Suna fitowa ya fara hango kawunansa da sauran abokansa da na Abubakar. Wurinsa suka taho suna tambayarsa ina ango. Bai iya cewa komai ba sai hawayen da yake zubarwa. Kabiru ne ya iya basu amsa ya sanar dasu halin da ake ciki. Gabadaya farfajiyar gidan ta rude da addu'a. Tashin hankali mara misaltuwa aka tashi dashi. Abubakar ya rasu daidai lokacin daurin aurensa. Maza sai kai kawo suke yi cikin dan kankanin lokaci labari ya isa kunnem Alh Adamu wanda dama suna hanyar shigowa gidan da abokansa. A gigice ya shigo ya wuce dakin Umar inda su Yalwa suke da sauran 'ya'yansu. Suna ganinsa kuwa su Nasiba suka rungume shi suna kuka. Duk wanda yake gidan sai ya tausaya musu wannan tashin hankali da suke ciki. Shi kanshi Alh Adamun da kyar yayi ta maza da taimakon dattijai abokansa suka sa duka matan suka fita domin a yiwa Abubakar wanka idan sun sauko daga sallar Juma'a sai a kai shi. ***** Jafar shine wanda yake bin Shema'u ita kuma Asmau take binsa. A gabansa Kabiru yake fadar rasuwar Abubakar. Saboda firgice bai san da yadda kafafunsa suka kawo shi gida ba. Masu kidan kwarya ya hango suna ta jera kayan kidansu. Zuciyarsa ta sake tsinkewa da ya tuna halin da kanwarsa zata shiga. Dama tun a bakin gate ya goge hawayensa saboda gudun tambaya. Yana shiga falo aka fara tambayarsa ko 'yan daurin auren sun watse ana son kai Asmau wurin kakarta tayi mata nasiha kafin 'yan yini su kara cika gidan. Jafar yace akwai sauran mutane sannan ya nemi jin inda Umma take. A bayan gida ya ganta suna magana da kanwarta Anti Bintu. Umma na ganinshi tace "baban Yaya har kun dawo? Ka ce zaku reception ko kaya ka dawo canzawa?" Jafar ya ji kamar ya fasa fada sai dai kuma babu yadda zaiyi. Idanunsa suka kada sukayi jazur yace "Umma Allah Yayiwa Abubakar rasuwa". Daga ita har Anti Bintu a tare suka ce "Me?" Jafar yace "yanzu muka dawo daga wurin daurin aure Yaya Abdulhalim yake fada...." maganar tasa makalewa tayi saboda kukan da ya zo masa. Suma kukan suka fara. Wannan tashin hankali da yawa yake. Fuska sharbe da hawaye tana salati Umma ta shiga ciki ta tafi daki. Anti Bintu ta daure ta leka dakinsu Asmau ta kirata. Tun da ta taso gabanta ke matsanancin faduwa tana ta karanta Hasbunallahu wa ni'imal wakil. Kafin ta shiga dakin Umman taji muryoyi suna cewa Innalillahi wa inna ilaihi rajiun.....a razane ta shiga Shema'u ta taso ta rungumeta. Kokarin ture yayarta tayi bakinta har rawa yake yi tace "waye ya rasu?" Bazata iya tuna muryar wadda tace "sai dai hakuri Abubakar ya rigamu gidan gaskiya" ba. Kamar saukar aradu haka Asmau taji zancen sannan numfashinta ya fara kokarin daukewa. Daga nan bata sake sanin inda take ba sai farkawa tayi a gadon asibiti. ABINDA AKE GUDU ๐Ÿ™†๐Ÿฝ3 Batul Mamman๐Ÿ’– _Afuwan Qasim Inspector ya zama ba ACP please_ *GA MASU NEMAN BOOK IDAN AN WUCE KU SAI A DUBA www.fikrahwriters.com.* Kusan minti biyar kenan da ta farfado amma ta kasa bude idonta. Tsoro take ji idan ta bude za'a sake fada mata wannan mummunan labarin da take tunanin taji a mafarki. Kasakasa take jin muryar su Umma a dakin ana ta tambayar ya jikin nata. Wannan ya tabbatar mata ba mafarki take yi ba. Lallai ta rasa Abubakar har abada. Ji tayi inama daga wannan kwanciyar itama mutuwar ta dauketa. Ya zata yi da rayuwarta ba tare dashi ba? Ita da Abubakar masu rikon sirrin juna ne. Mutuwarsa komai daren dadewa zata fallasa sirrin da suka boye. Sirrin da ya kara musu soyayya da mutunta juna saboda rashin gudun juna da suka yi. Hawaye ne ya zubo ta gefen idonta. Walida ce ta lura da hawayen tace "Umma ta farfado". Haj Bara'atu ta dawo gefen gadon ta zauna tare da rike hannun Asmau. "Ki bude idonki Asmau kinji. Ko ruwa ne ki tashi ki sha. Kin dade a kwance gashi har la'asar ta wuce". Subhanallah! Ta tabbatar ta rasa Abubakar kenan. Garin yaya aka barta a kwance har ta kai yanzu ba'a bari ta sake ganinsa ba? Ko bata tambaya ba tasan tuni Abubakar yana makwancinsa. Sake runtse idonta tayi. Gara ta cigaba da kwanciyar har nata lokacin ya yi. Umma ta kalleta da tausayawa kwalla ta cika mata ido

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});