Chapter 97
Chapter 97
ran da bai gani ba saboda yana da sa abu a rai. Ko yaya aka fadi maganar haihuwa mai kama da gori sai ka gani a fuskarsa. Duk yadda Asmau taso taya Hajiya aiki hanata tayi tace ta koma daki ta kwanta. Yadda take ji da ita da cikin jikinta ai bazata yi sake wani abu ya faru ba duk da komai na Allah ne. Da Bilkisu ta dawo daga makaranta ne ma ta tayata har suka karasa. A falo suka zauna su ukun suna hira Bilkisu ce mai yin fiye da rabin zancen. Hajiya ta sa ta zubawa Asmau tuwo mai yawa tace kuma sai ta cinye. Zuwa lokacin hankalinta ya fara tafiya ga inda Jikamshinta ya tsaya gashi har anyi isha bai dawo ba kuma wayarta tana gida. Haka ta rinka cin tuwon a hankali sai taji sallamarsa. Wani sanyi taji ya ratsata amma ta basar ta cigaba da cin abinci tana kallon plate a dole bata so ta kalle shi kada Hajiya ta gani. Wata jaka ce yar madaidaiciya ya shigo da ita mai dauke da kaya. Bilkisu ta gaishe shi sannan ta karbi jakar ta kai dakin Hajiya kamar yadda ta bata umarni. Hajiyan ma tashi tayi "Bari naje nayi sallah duk kunyi kun barni. Ki tabbatar kin cinye tuwon nan kafin na dawo. Kai kuma sai da safe nasan kila kafin na idar ka tafi" Col. Ishay yace "to Hajiya Allah Ya bamu alhairi" a ladabce Tana tafiya ya dauke plate din gaban Asmau sannan yaja hannunta. Ta bude baki zata yi magana taji ina zai kaita ya marairaice fuska "please Matar Jikamshi magana zamuyi kafin Hajiya ta fito" "A ina?" Ta tambayeshi tana waigen kofa. Bai bata amsa ba ya ja hannunta suka bi wani korido suka je wani daki. Dakin a share yake kamar ana kwana sai dai ko ba'a fada mata ba ta gane dakinsa ne na da kafin aurensu. Bakin gado ya zaunar da ita ya janyo kujera irin ta aiki a gaban wani tebur gabanta ya zauna shima "Har abinci kike iya ci tun dazu baki ganni ba amma ko a jikinki" "Allah Sarki Jikamshina kalli ka gani kadan naci saboda na rasa inda ka tsaya gashi babu waya a hannuna" Murmushi yayi mata yana kara godewa Allah wai Asma'unsa ciki gareta. "Yanzu dai ki bani abincin nan yunwa nake ji. Amma gaskiya bazan yarda ki rinka bawa baby na tuwo ba." Ta dan sha kunu cikin wasa "sai na fadawa Hajiya kuma ka tashi ka tafi gida kada dare ya kara yi" Wani kallo yayi mata mai nuni da zancenta wasa ne "babu inda zani, ke yanzu sai ki kwana a nan ba tare dani ba?" Ta girgiza kai "da Hajiya tace kayan sati sai da zuciyata tayi tsalle.....amma na murna" "Zakiyi bayani ne. Ni dai bani abinci naci." Da hannun ta rinka bashi itama tana ci. Sunyi kusan minti shabiyar saboda cin tuwon ma wani sabon salo ake masa. Idan ta bashi sai ya lashe mata yatsu ko ya cijeta. Tayi ihunta a hankali tace zata rama sannan su cigaba. Bayan sun gama ta wanke hannu a bandakin dake cikin dakin shima yazo suna kuskure baki don brush dinta yana cikin jaka. Ya rike fuskarta da hannuwansa yana shirin kissing dinta suka ji kamar muryar Hajiya. Nan da nan Asmau ta rude ta rasa yadda zatayi. Shima uban gayyar yau dai ya rasa abinyi don kuwa duk abin sa Hajiyarsa yana jin kunyarta. Idon Asmau harda hawaye da taji Hajiya tana tambayar Bilkisu ina ta shiga daga cikin korido din. Taku kadan zasu kara su iso dakin. Duka ta kaiwa Col. Ishaq a kirji "Duk laifinka ne da ka jawo ni dakin nan. Yanzu da wane ido zan fita don Allah" "Kinji ki da wani zance, ba fa daukoki nayi ba da kafarki kika taho ke dadi miji. Ai da sai ki fada min ba dadewa zatayi a dakin ba" "Yanzu laifina kake gani, ba a gabanka tace mana sallah zata yi ba." Sosai ta gama rudewa. Col. Ishaq ma dai ya rasa mafita don bai san yadda zaiyi ba idan Hajiya ta bude kofar dakin nan. Ganin sunyi tsuru ga Bilkisu tana ta kiranta yasa ta saddakar kawai. Gara ta fita da tayi ta zama tana tsoron su bude ayi zaton wani abin ma suke yi. Bude baki tayi tace "Haji..." Yayi maza ya toshe bakin da hannunsa yana magana a daidai kunnenta duk ya riketa saboda tana kokarin kwacewa "tona mana asiri zakiyi kuma" Ta soma cizon hannunsa yana runtse ido yau ba na wasan da ta saba bane da gaske mai zafi take masa. "Matar Jikamshi zan rama kuma kada ma kiyi tunanin zan hakura idan kika fara wannan hawayen karyan" Tana ji ya saketa bayan takun su Hajiya ya bar wurin ya soma tsokanarta "kunyar karya ma kike yi, kin gama saita baki zakiyi kissing Jikamshinki shine daga jin muryar Hajiya kika wani rude bayan kinfi kowa sannin a gidanta kike" Duk yadda suke dashi har yanzu wani abin idan yayi ko ya fada sai taji kunya. Ta rufe idonta tayi hanyar kofa batare da ta amsa masa maganarsa ta farko ba tace "sai da safe" Ai kuwa ya rikota yana bata hakuri kada ta fita yanzu. Bayan dan lokaci kadan ya fita wai zai duba mata idan Hajiya ta kwanta sai taje ta kwanta kawai itama. Jinsa kawai take amma da wane ido zata kalli Hajiyan da safe. Shigarsa falon ke da wuya ta fito ya sunkuyar da kansa kasa. Yi tayi kamar bata gane me yake ba tace "kaje dakina ka dauko jakar Asmau ka kai mata ko akwai abinda take bukata. Kuma ka rufe gidan. Sai da safe" daga nan ta juya ta koma ciki. Yafi minti uku a tsaye sai da ta sake kiransa tana cewa zata rufe kofar dakinta idan bai zo ya dauka ba. Ya shiga kamar salihin gaske ya dauko ya fita. Hajiya tayi murmushi kawai. Yaran zamani sai addua. Basa kunyar idon manya idan suna son juna. ***** Asmau na kai kawo a tsakar dakin ya shigo da jaka yana murmushi. Bai zata Hajiya zatayi saurin barinsa da Asmau ba amma dama niyarsa ya kwana a gidan don nasa kayan na mota. Idan ta ga yaki tafiya yasan zata barsu su koma nasu gidan. "Bukatarki ta biya Hajiya tace ki kwana a nan." Ta zaro ido "da gaske? Jikamshina ka gama dani. Daga yau bazan kara fita daga dakin nan ba. Ranar da zan tafi ma sai Hajiya bata nan zan fito" Ya soma dariya "ke dai kinji dadi kawai. Bari naje na dauko nawa kayan dama da shiri nazo. Ki kunna mana heather sai muyi wanka duk zafi ya isheni." Harara ta wurga masa ya fice yana mata dariya. Da ya dawo duk suka yi wanka ta haye wata doguwar kujera da yake kwanciya ya huta da. Yace ta dawo gadon ta noke kafada "da kunya fa, Hajiya na gidan nan na kwanta kusa da kai" Tasowa yayi daga gadon ya dawo ya hau kujerar ya matseta a karshe don tayi musu kadan. Cikinta ya shafa yana lumshe idanu "duk yadda kike so haka za'ayi, iyaka dai gobe muce ba kwanan gado muka yi ba
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103