Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 2

Chapter 2

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,196 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Abubakar ya fada yana saka takalmi. Har bakin mota ya raka Qasim. Dukkaninsu basu ji dadin zuwan canjin aikin a wannan lokacin ba. ****** Kwalliyar Asma'u ta yau har tafi ta jiya. Kawaye da 'yan uwanta kowa yayi irin nasa adon. Anti Shema'u, 'yarta Mimi da Aina'u kayansu iri daya. Mazan gidan su biyu suma shadda suka saka iri daya. Suna gama shiryawa motar ango tazo daukar amarya. Shima kayansa ya dace da nata. Tun a gida ake daukarsu hotuna haka a wurin dinner din. Abin ya kayatar saboda komai anyi shi cikin nutsuwa irin na 'yan boko. Duk motsin Asma'u idon Abubakar yana kanta suna hada ido sai suyi murmushi. Soyayya ce da ta samo asali tun farkon tarewarsu Asma'u a unguwar su Abubakar shekaru tara da suka wuce. Sai wurin shadaya da rabi aka tashi daga taro kowa ya tafi gida. Wani abokin Abubakar ke tuka motar suka ajiyeta a gida sannan suka wuce. ****** Washegari Juma'a gidan commissioner kamar yadda duk 'yan unguwa suka sakawa gidansu Abubakar sun tashi a makare saboda gajiyar da suka kwaso a wurin dinner da kuma sanyin da aka tashi dashi. Mahaifinsu Alh Adamu Matawalle tsohon dan sanda ne har commissioner ya taba yi. Da taimakonsa Qasim ya sami aiki ma. Matarsa daya Yalwa wadda suke kira Mama. Su shida ta haifa. Babban danta sunansa Abdulhalim yana da mata daya da 'ya'ya biyu sai mai binsa Nasiba itama tana gidan nata mijin. Abubakar ne na uku amma kannensa mata biyu Sadiya da Suwaiba duk sunyi aure. Su biyu suka rage shi da autansu Umar. A gaggauce suka tashi domin baifi awa daya da rabi ya rage musu ba lokacin daurin auren ya yi. Mata suka tashi aka shiga kitchen saboda abokan Baba kamar yadda suke kiran mahaifinsu a gidan zasu ci abinci idan an taso daga wurin daurin auren. Ga samari 'yan uwa da suka kwana a gidan su ma shiyasa aka yi ta layin shiga wanka a bandakuna biyun dake bangaren maza. Da gangan suka ki barin Abubakar ya fara shiga a cewarsu shi ango dole a jira shi. Baifi minti talatin ya rage ba Umar ya fito daga bandaki kumfar jikinsa bata gama fita ba Abubakar ya shiga ya rufe kofar da mukulli. Sauran samarin babu wanda ya tsaya cin abincu suka fita dama wurin daurin auren babu nisa daga gidan ko a kafa zasu iya karasawa kofar gidan kakan Asma'u tunda bayan layi ne. Duk an gama taruwa iyaye suna daga cikin katon soron gidan sauran mutane suna daga waje duk an cike layin. Alh Adamu ya kira Abdulhalim yana tambayarsa ina Abubakar. Abdulhalim yace "inajin yana waje kasan halinsa da kunya karshenta ya ki shigowa." A waje kuma abokansa ke tambayar juna ko ya shige ciki ne domin basu ganshi ba. Babu wanda ya saka damuwa a ransa har aka gama daurin auren kowa yana tunanin yana wani wurin. A can gidansu kuma Haj Yalwa ce ta kira wata yarinya cikin 'yan uwansu tace ta duba mata kowane bandaki na gidan ta dauko bota a cika su da ruwa a ajiye a waje saboda abokan Baba. Idan sunci abinci zasu yi shirin sallar Juma'a. Yarinyar tayi ta zagaye tana dauko buta. Kofar bandakin dake cikin dakin Umar ce ta kasa budewa sai ta koma ciki ta fadawa Nasiba. Tare suka dawo suka yi ta kokarin budewa suka kasa ga ruwa kuma ya fara fitowa ta karkashin kofar bandakin. Nasiba ta saka kunne jikin kofar taji alamun famfo yana zubar da ruwa. Mama suka sanarwa tace a samo wani ya balle kofar saboda kada ruwan bangaren ya kare tunda tanki ne. Abu ya hada da mata suka kasa budewa ga ruwan yana yawa. Dole suka hakura har Allah Yasa aka fara dawowa daga wurin daurin auren. Lokacin duk sun tsince kayan dake kasan dakin saboda ruwa. Umar na shigowa Mama ta hau shi da fada shi bai ma san laifin da yayi ba sai da tace yaje ya bude kofar bandakin shi. Yayi mamakin jin kofar a rufe ya saka iya karfinsa ya soma dukanta. Babu kowa a dakin sai shi kadai don Mama tace babu mai taya shi gyarawa. A bugu na hudu kofar ta bude yayi tozali da abinda yayi matukar razana shi. Abubakar ne kwance cikin ruwan da ya hade da jini daga kasan kansa ga sabulu can a gefen kafarsa ta hagu alamun zamewa yayi. ABINDA AKE GUDU ๐Ÿ™†๐Ÿฝ 2 Batul Mamman๐Ÿ’– Lokaci guda Umar ya gigice jikinsa ya hau bari. Da sauri ya shiga bandakin ya zauna cikin ruwan kusa da Abubakar sannan ya daga kansa ya dora a kan cinyarsa. Da kyar ya iya cewa "Yaya". Babu wata alamar motsi a tare da Abubakar. Umar ya shiga jijjiga shi yana kiran sunansa. Duk da haka Abubakar bai motsa ba. Iyakar tsorata Umar yayi don ji yake kamar zuciyarsa zata buga. Wasu zafafan hawaye ya soma yi a hankali yace "Yaya Abubakar ka tashi an daura auren." Nan ma dai shiru yaji. Tunaninsa gabadaya ya kulle ya rasa me zaiyi ya taimakawa dan uwansa. Da sauri ya tashi ya fara kokarin daga shi ya fitar dashi daga cikin ruwan, amma yayi masa nauyi domin duk jikinsa a sake yake. Ya sake gwadawa yaji tabbas bazai iya ba sai ya tashi ya fita tare da rufe dakin da mukulli. Duk wanda ya ganshi da kaya a jike ga alamun jini a gaban sabuwar shaddarsa da tasha dinki sai ya tambaye shi ko lafiya. Babu wanda ya bawa amsa ya wuce dakin Mama. A tsaye ya ganta a gaban mudubi tana saka sarka. Kafin yayi magana ta juyo da sauri saboda ganinshi da tayi ta mudubin. Gaban rigarsa ta nuna tare da zuwa gabansa ta tsaya "Umar me ya faru? Ciwo kaji garin gyaran bandakin? " Maimakon yayi magana kawai sai ya rungumeta yana kuka mai tsuma zuciya. ***** Duk akwatunan kayan Asmau an gama hadasu a wuri guda. Daya daga ciki ta bude ta dauko wata atampa zata saka Aina'u ta shigo dakin da gudu sai haki take yi. "An daura auren. Daga yau dakin nan ya zama nawa ni kadai" ta fada iyakar karfinta tana murna. Tana gama fadar abinda ya kawota ta sake ficewa da gudu. Su Walida suka soma guda suna yiwa Asmau tsiya. Harda masu yi mata wakar ta zama dauko riga....ta zama dauko hula....ta zama dauko wando.... Duk baki irin nata jikinta sai da yayi sanyi ta kasa biye musu kamar yadda ta saba. Ji tayi zuciyarta tana bugawa da karfi har abin ya bata tsoro kawai sai ta soma kuka. Hankalinsu ya fara tashi. Walida ce ta rungumeta maimakon ta bata hakuri itama sai ta fara kukan. Wata 'yar kanin baban su Asmau ce tace "haba Walida maimakon ki bata hakuri sai ki biye mata. Yau ai ranar farinciki ce ba kuka zakiyi ba. Ki tashi kiyi nafila ki godewa Allah da Ya nuna miki wannan rana." Jiki a sanyaye Asmau ta saka kayanta ta dora hijab ta tayar da sallah. ***** Gaban Mama ya fadi ta dan ture Umar daga jikinta. Ta soma kokarin daga masa riga ta ga ko ciwo yaji ya zubar da jini da yawa haka. "Mama jinin Yaya Abubakar ne". Jin maganar tayi har

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});