Chapter 69
Chapter 69
naji ka shiru." "Ki kular min da kanki." Ya iya cewa zuciyarsa babu dadi ya ajiye wayar. Motsi yaji a wurin kofa ya juya. Hajiya ce a tsaye bai san tun yaushe take a wurin ba. Abin mamaki sai yaji 'yar kunya kadan ba da yawa ba. Itama basarwa tayi ta shigo ciki kamar bata ji komai ba. "Zaka je asibitin ko kaji sauki? Ni a yadda Bilkisu ta fada min na zata ciwon sosai ya kamaka" "Sosai ne mana Hajiya. Kamar kan zai tsage haka nake ji" Tayi dan murmushi kawai "ai naga kamar ka sami magani." Dariya ta bashi ya tashi zaiyi alwala. Fita tayi tace idan anyi magriba lallai yaje asibiti don tasan ciwon kan baya masa da wasa. ***** Bayan isha Asmau da Amatullah suna gwada sabon dinkinsu da Yassar ya karbo musu taji waya. Ringtone din Jikamshi daban yake shiyasa ta gane shi. Da fara'a ta dauka don tun wayarsu ta dazu hatta su Umma sun ga canji a tare da ita. Kafin tayi magana yace "fito ina jiranki" Har wani faduwar gaba taji. Tayi kewarsa sosai amma tana jin kunyar hada ido dashi kuma. A waya ta iya nuna masa soyayya sai an hadu bakin ya mutu. Ga mamakin zuwansa shi da bashi da lafiya. Amatullah ta tura wurin Yassar tace ta fada masa suje babanta ya zo. Ita kuma ta zauna ta gyara fuskarta ta sami mayafi ta yafa sannan taje ta fadawa Umma. Addua tayi mata tace ta gaishe shi. Da ta fita Umma tace ashe ga dalilin sauyin da ta gani a tare da ita. Allah Yayi mata zabi mafi alkhairi. Mai son naka dole ka so shi. Tunda ta fito daga cikin gidan yake kallonta. Samun kansa yayi da yin godiya ga Allah da ya hada jininsa da Asmau. Yarinyar akwai nutsuwa da kamala. Tana bukatar miji nagari saboda samin ingantacciyar rayuwa da nutsuwar zuciya idan aka yi laakari da kaddarar da ta fada mata. Kuma tana burge shi saboda ta karbi jarabawarta hannu biyu. Har ta iso wurin da yake zaune a gefen mota shi da Yassar da Amatullah kanta na kasa tana murmushi. Da sallama ta karaso ta dan rissina ta gaishe shi. Ya amsa yana kare mata kallo. Tayi kyau sosai. Shi kuma ta lura ya dan fada. "Yassar ka shigo dashi falo" Yace "kiji min mata, ni gurgu ne?" Ita da Yassar suka yi dariya sannan suka koma falon. Da kyar Yassar ya yiwa Amatullah wayo suka shige ciki. Daga inda take zaune Asmau ta dan dago kai suka hada ido da Jikamshi. Karuwa sonta yake a zuciyarsa amma dole yayi abinda ya kawo shi. Tattaro duk nutsuwarsa yayi yace...... ABINDA AKE GUDU🙆🏽48 Batul Mamman💖 Ta kagu sosai taji abinda zai fada shi kuma nauyin maganar yake ji. Idan ya fada shikenan yayi musu katanga daga wannan lokacin. Ganin babu amfani yayi ta jan abin yasa yace "Banda sunan sunan matata ta fari baki san komai game da ita ba ko"? Asmau ta dan turo baki kishi na cinta duk da bata san matar ba. "Ni sunan nata ma na manta. Kawai kazo bayan sama da sati daya ka fara min da hirarta" Yadda take hade rai ya bashi dariya. Ya gyada kai "kishi gareki haka, mun dade da rabuwa fa har ma tayi aure". "To ai kaine sai ka rasa hirar da zaka yi sai tata" Ya gyara zama tare da harde kafafunsa "saboda abinda zan fada miki yana da alaka da ita. Ina so ki saurareni da kyau ki fahimci abinda zan fada miki." Hankalin Asmau ya fara tashi. Wani abu ne ya darsu a zuciyarta ta soma hawaye babu shiri tace cikin murya mai nuna rauni "ba ma sai kace komai ba na gane abinda kake son fada. Aurenta ya mutu zaka mayar da ita ko. Babu komai zan iya zama da kishiya. Don Allah Ka kwatanta adalci a tsakaninmu" ta kare tana jan hanci. Col. Ishaq bai san lokacin da dariya ta subuce masa ba. Ita kuwa Asmau tayi kicin kicin da fuska. Hankici ya dauko daga aljihun wandonsa ya bata "kinci sunanki Idon kuka. Daga fara magana ji yadda fuskarki ta kumbura. Ai dai kya bari na fadi abinda ya kawoni kafin ki soma zubar da hawaye. Mata na gidan mijinta zaki kashe mata aure da baki" Dan sanyi taji a ranta kila ba abinda zai fada ba kenan. Har tayi murmushi sai kuma wani tunanin yazo mata "maganar aurenmu ne?" Ya daga kai yana kallonta. Tausayinta yake ji sosai a ransa. Murmushi tayi mai ciwo "Hajiya bata amince ka aureni ba ko? Dama nayi tunanin haka zata faru. Ba kowace uwa bace zata iya daure zuciyarta ta bari danta ya auri mace irina. Ko nice kila nayi sama da haka ma. Abinda kayi mana na kyautatawa Allah Ya saka da alkhairi. Nagode sosai wallahi. Ko a haka ma nagodewa Allah da Ya hadani da kai har ka nuna min so ka zama cikin masu nuna min na kara hakuri da kaddarar rayuwa" Hawaye ke zubo mata tana magana bata ko tunanin tare shi. Dago kansa yayi daga cikin kujerar ya dan matso gaba. "Ya Salaam, Matar Jikamshi haka kike? Lokaci daya duk kin rikita kanki. Kada ki dauki alhakin Hajiyata wallahi ta amince da aurenmu" Jikinta duk da haka a sanyaye yake tace "sauran 'yan uwanka ne basu amince ba?" "A duniyar nan Hajiya ce kadai zata hanani aurenki na hanu. Banda ita babu wanda ya isa. Yara kanana akeyiwa haka ba ni ba. Kamata kowa yasan ina da hankalin da zan san abinda ya dace da rayuwata. Ki saurareni da kyau kiji abinda zan fada. Kamar yadda na fara magana kafin ki katseni da dan bakin nan naki mai bani shaawa..." ya fada yana kashe mata ido. Kunya taji sosai harda rufe fuska da hannuwanta. Yayi murmushi ya cigaba da magana "na taba aure, shekarunmu shadaya da Badar babu haihuwa. Munje asibitoci da dama ana cewa bamu da matsala. Har maganin gargajiya mun sha. Daga karshe mahaifiyarta tasa na saketa kuma cikin ikon Allah a shekarar da tayi aure ta haihu" Asmau ta dan girgiza kanta "Allah sarki, dama haihuwa ta Allah ce. Wani baya haihuwar dan wani" Kallonta yake da mamaki kamar bata fuskanci inda ya dosa ba "haihuwar Badar ya tabbatar min da inda matsalar take. *Matar Jikamshi, bana haihuwa*. Saboda haka kiyi hakuri da na bata miki lokaci amma na _janye maganar aure a tsakaninmu_." Tamkar wadda aka watsawa ruwan zafi haka taji saukar maganarsa ta karshe. Shiru tayi na dan lokaci yana ta kallonta yana jiran ta fara kuka sai yaga idanunta ko alamar hawaye babu banda wanda ta zubar dazu. Shirunta tsorata shi yayi yace "kice wani abu mana." Murmushi take yi kamar bata ji abinda ya fada ba ma. "Jikamshina" Jiran amsarta yake na nuna masa bacin rai da bai fada mata tun da wuri ba. "Lokacin da ka fara sona tausayina kake ji ko kuwa sona kake fisabilillah" "I love you Asmauna, and I will always do" Tayi sassanyar ajiyar zuciya "duk macen arziki bata da burin da ya wuce idan zatayi aure ta kai budurcinta gidan miji. Jikamshina na rasa wannan damar har abada. Na fada tarkon shaidan har ya zamana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103