Chapter 67
Chapter 67
magana ta karshe da Alh Adamu sai ga Garzali ya shigo yana ta fara'a suka hadu a bakin kofa. Umma tace "kanina mijin 'yata irin wannan fara'a haka. Ko dai Zubaida ta haihu" Yana murmushi yace "yanzu daga asibitin nake. Ko awa daya bata yi ba. An sami namiji." Umma sai murna ta koma ciki tana mita akan me bai fada musu ba tun lokacin da suka tafi asibitin. Sai da suka je dakin Hajjo bayan ta fada mata kyakkyawan labari tace "ina kuka kai su Walid?" "Kai Yaya Bara'atu sai faman fada kike yi. Tsakar dare fa ta fara nakudar. A makota na ajiyesu muka tafi." Asmau ce ta shigo dakin daga kitchen bayan taji muryar Kawu Garzali. Tayi murna sosai tace bari ta dora ruwan zafi sannan ta hada abinci. Kawu Garzali yace ta barshi makociyarsu duk tayi wannan. Yana jin bazata dade ba za'ayi sallama. Tace to bari tayi wanka sai su tafi. Tana tafiya Umma ta soma fada masa halin da suke ciki ga Qasim kuma da yake jira a sake basu lokaci. Hajjo tace "Allah mai iko, wallahi idan aka ce min yarinyar nan zata sami manemin aure sai in karyata. Gashi yanzu an samu har an rasa na zabe. Ni dai shawarata kada ayi mata dole. Yaron nan Qasim dan mutumci ne gaba da baya amma bana son ayi auren dana sani. Asmau ba kankanuwar yarinya bace da zaa ce bata san me take yi ba. Kai Garzali mu zamu je asibitin. Kaje ka sami Alhaji kuyi magana. Idan za'aji ta bakin Ishaq din ne ya kamata a hanzarta. Idan kuma da Qasim din ne ma duk yadda akayi babu matsala." Umma ta dan sassauta murya tace "Bintu fa ta fada min shi Ishaq din yace ya janye saboda baya haihuwa." "Baya haihuwa?" Hajjo ta fada tana daga murya. Umma tace "Asmau bata sani ba. Yace zai fada mata da kansa. Nima ban nuna mata na san wani abu ba" Kawu Garzali ya shiga jimami. Zubaida ta fada masa irin yadda ta ga Col. Ishaq da Asmau suna son juna ranar da taje yini a gidan. Anya akwai ranar da Asmau zata ga haske a rayuwarta kuwa. Daga wannan matsalar sai wannan. "Wai ya taba aure ne ko tuzuru ne shi Ishaq din" "Kaima dai Garzali in bai taba aure ba yaushe zai san da matsalar rashin haihuwar. Shekararsa shadaya da matarsa ta farko" Gefen gado Hajjo ta samu ta zauna "ni dai kaina duk ya kulle. Haihuwa ba abin wasa bace duk da mutum baya bawa kansa amma kowa yana so. Muje dai wurin maijegon, kai kuma duk yadda kuka yi da Alhajin ka fada mana. Ai ita shawara tana da dadi. Bana son azo ana cizon yatsa nan gaba shiyasa cikinsu babu wanda zan ce lallai sai ta zabe shi." ***** A nan suka bar zancen su Umma suka wuce asibiti daukar Zubaida. Kawu Garzali ya tafi gidan Alh Adamu. Bayan sun gaisa ne Alhajin yace "ina Hajiya Bara'atun? Tace zata zo. Ashe tare ma kuke" "Ni kadai ne Alhaji. Sun tafi asibiti mai dakina ta sauka dazu bayan asuba" Barka Alh Adamu yayi masa sannan suka fara tattauna abinda yake gabansu. Zancen Col. Ishaq ma sai da Alh Adamu yayi ya ce Mama ce ta fada masa. Ashe shiyasa yaga shi da mahaifiyarsa da 'yan uwansa sun zo duba Amatullah. Daga Shanono kuma jiya ya sami waya suna bukatar a sake basu lokaci. "Alhaji wannan abu duk mai sauki ne. Yanzu nake ji cewa shi Ishaq din yace zai janye saboda yana da lalura ta rashin haihuwa. Idan haka ne kaga Qasim ya kamata ta aura" "Banki taka ba Garzali. Duk abinda aka riga aka sani yafi sauki idan za'a tunkare shi. Amma menene tabbacinmu na cewa shi Qasim yana haihuwa ko ita Asmau zata sake haihuwa? A zahiri nafi sonta da Qasim saboda kusancinsa da Abubakar. Gani zanyi kamar dana ne ya aureta. Sai dai kuma bana son mu saka son zuciya a cikin al'amarin nan. Tana gida ne yanzu?" "A'a tare suka fita dasu Hajjo" Garzali ya bashi amsa. "Idan ta dawo kace ina nemanta jibi bayan azahar in sha Allah. Zan je daurin aure ne gobe Gashua. Tambayarta zanyi don kada abin yazo da daukar alhaki. Wanda ta zaba sai mu duba mu kuma muga dacewar hakan. Aure ai ba'a yi masa garaje. Rashin karasa karbar kudin wancan karon ma daga Allah ne." "Shikenan Alhaji, Allah Ya zaba mata mafi alkhairi." Daga nan suka yi sallama Kawu Garzali ya tashi ya tafi. ***** Inna mahaifiyar Qasim ce ta saka shi a gaba suna magana akan aurensa. "Baffanka yace sunyi magana da Alhaji Adamu yace a dan kara musu lokaci zasu sanar da ranar da za'aje kai kudi" "Eh munyi maganar. Dama Asmau nace ta fada musu da farko to ashe ma Baffa ya kira shi" Rai a bace Inna tace "yanzu ita Asmaun har sai an bukaci lokaci kafin ace an yarda a kai kudin? Naga dai ita ce ma me abin bincike a kanta. Yarinyar da ta bar gidansu tsahon shekara biyar." Murmushi kawai yayi. Inna bata son auren nan nasa duk irin yadda zaiyi mata bayani tace su rayuwarsu ba irin ta birni bace. A nan duk wanda yaji Asmau tana da 'ya sai ya tambaya mijinta rasuwa yayi ko sakinta yayi. Wasu ma suyi ta cewa mai zai sa Qasim ya fara da auren bazawara. Babu yadda za'ayi su boye gaskiyar lamari. Wasu ma sun dade da sanin rasuwar abokin Qasim da cikin da yayiwa budurwarsa. Gulma da kananan maganganu sai yawo suke. Ko kadan Inna bata jin dadin hakan duk da tana kokarin yiwa Malam biyayya ta nuna ta amince da auren. "Sai anyi magana kayi ta murmushi kamar wani bazawari. Ya dai kamata kafin komai ya kankama kuje ayi mata gwajin 'yan cututtukan nan na zamani musamman kanjamau" "Inna ba fa karuwanci taje tayi ba. Aikin asibiti tayi duk tsahon lokacin nan" Tabe baki tayi "haka dai ta fada muku ku kuma kuka hau kuka zauna. Mace babu mai kwabarta ai sai ta mike kafa. Ni dai ba wani abu nace ba. Ayi mata gwaji ko don taka lafiyar. Gurbacewa ce dai ka gama gurbata mana dangi. Ko me kuka haifa nan gaba sai ance yayarsu shegiya ce" Har ransa Qasim baiji dadi ba. Innarsa ta lura da yadda ya hade rai tayi murmushi "Baba kenan, kada ka daukeni muguwar uwa wadda bata son danta yayi aikin neman lada. Duk wata uwa komai shedancin danta tana son ya auri mace tagari. Abubuwan da kaga suna ta faruwa da yarinyar nab kadan ne daga *abinda ake gudu* a zina. Bana muku fata amma wata rana idan kunyi aure zata iya yin abu da zuciya daya amma saboda sanin da kayi na rayuwarta ta baya kawai sai shaidan ya kitsa maka zargi ka hau kai ka zauna. Karuwai da yawa sun yi aure. Wasu ma a gidan mijin suke sheke ayarsu. An sani amma da yake aure rai gareshi sai kaga ba'a sake su ba. Kasan halina bana boye abinda yake raina. Idan ka auri Asmau kayi mata halacci kuma ka rike amanar abokinka. Ka gyara abinda ya bata. Sai dai bazan fasa nanata maka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103