Chapter 59
Chapter 59
ga Amatullah babu lafiya yanzu ko me zata fada masa zai zamto babu nutsuwa a tare da ita. Tare da su Alh Adamu suka fita raka 'yan uwansa zasu biya gidan Umma su dauko sauran. Kayan ciye ciye da aka tanadar musu Umma tasa Sabira da Shemau su bi bayansu sai su hada a basu su tafi dashi. ***** Suna zaune har akayi magariba sannan su Umma suka tafi aka bar Hajjo da Asmau. Kayan kwana za'a hadu musu sai Mama ta dawo su kwana tare. Col. Ishaq yana dakin amma shima yaki kallon inda Asmau take, shima bata da abin fada masa. Ba don ciwon Amatullah ba da yanzu an gama magana tsakaninta da Qasim sai batun saka rana. Biyewa Amatullah yayi tana ta shagwaba son ranta, sai Hajjo dake dan yi masa hira itan ma kunyarsa take ji tunda tasan komai. Duk yadda Asmau taso su hada ido yaki. So take ta bashi hakuri tunda tasan yanzu bata da sauran mafita. Karshenta kafin sati ya zagayo ma mutanen Shanono su sake dawowa. Shigowar Jafar da Qasim yasa shi tashi yayi musu sallama ya fita. Damarta kenan ta bashi hakuri a yau tunda wayarta tana gida. Bai dade da fita ba tace zata je tambayar likita ko zata iya bawa Amatullah abinci. Jafar yace ta bari yaje ta wayance "barshi Yaya Jafar so nake na dan fita na gaji da zaman wuri daya" Shi kuwa Qasim tuni ya gane inda take son zuwa sai kawai ya dauke kansa. Yana kallo ta fita cikin sauri don kada ya bar asibitin kafin ta karasa wajen. Tana fitowa ko alamunsa babu ta kara sauri harda dan gudunta. Tsoronta bai wuce kila daga yau yaki dawowa ba. Garin sauri tabi wata hanyar da zata kaita wurin ajiye motoci ta kusa karo da mutum har sai da taji tsoro saboda rashin wadatar haske a wurin. Tsaye yake ya sanya hannuwansa a aljihun wando yana kallonta. Kallo ne na tuhuma wanda har ranta sai da taji babu dadi don bata kyauta masa ba. Bai motsa daga inda yake ba yace "me yasa kika wahalar da kanki da yin gudu bayan kinsan dole zan jira fitowarki. You have alot of explaining to do" Fuskarsa yau babu fara'ar nan da take kara saka mata sonsa. Yau a sojansa ya fito sai ta daburce ta rasa ta ina zata fara bayani. "Kinyi shiru, na tafi ne?" "A'a don Allah kayi hakuri" sai ta soma kuka. "Matar Jikamshi" sai yanzu ta danji sanyi a ranta saboda yadda ya kirata. A hankali ta dago ido ta kalle shi. "Why?" Ya tambaya shima duk dakewarsa yana jin babu dadi. Idan ya rasa Asmau gani yake bazai taba samun madadinta ba. Yana mamakin irin wannan so da yake mata wanda ya shige shi lokaci daya. Idanunta cike da hawaye ta soma fada masa yadda abin ya faru." Kayi hakuri da ban sanar da kai ba. Babu yadda zanyi ne tunda duk iyaye sun amince" Ya gyara tsayuwarsa yana fuskantar ta "ki dena kukan nan kinji ko. Idan nace miki everything is ok nayi karya because it is not. Kinji kunyar sanar da Qasim da wuri kinga abinda hakan ya janyo. Magana kuma tunda ta hada da iyaye zan hakura kamar yadda kike so. Dazu ma naga ya kamata ya sani ne shiyasa na fada masa." Wani kukan ne yazo mata sai zubar da hawaye take. Tana sonsa fiye da yadda take tsammani a baya. "Jikamshi to yaya zanyi?" Tausayi ta bashi. Asmau ta fuskanci abubuwa da dama a cikin 'yan shekaru. "Da ace babu ni a cikin manemanki sai na baki shawara. Amma tunda ina ciki bana so a zargeni da son kai. Shawara tana gareki Asma'una. Idan Allah Yayi Qasim ne mijinki alfarma daya nake nema kada ku rabani da Safina. Atleast ko school fees dinta ku bari ya zama responsibility dina." Meyasa Qasim bai sanar da ita iyayensa zasu zo da wuri ba. Ji tayi gabadaya auren ya fice mata a rai. Kuka kawai take yi mai ciwo. Muryarta a shake tace "To yanzu shikenan?" Murmushi yayi mata, sai da taji shi har ranta. "Shikenan Matar Jikamshi. Maybe daga yau bazan kara kiranki da wannan sunan ba. Ki rike duk abinda Allah Ya kaddara miki da hannu biyu. Qasim mutumin kirki ne a yadda na fahimce shi. Ban taba ganin mutum mai kokarin rike amana kamarsa ba" "Na sani wallahi, shiyasa na kasa fada masa gaskiyar abinda ke zuciyata. Ina gudun bata masa rai saboda nasan duk abinda yake yi don ya kyautata mana ne." "Kada kiyi ja in ja da iyaye akansa. Idan shine alkhairin rayuwarki bamu da zabi da ya wuce karbar kaddara." Juya mata baya yayi zai tafi. Yana jin sautin kukanta ya karu. Yasan yana sonta ba da wasa ba, amma duk abinda aka ce iyaye sun shiga ciki a matsayinsa na babba bai kamata ya nuna mata bijerewa alkhairi bane. Duk da kuwa yana ji a ransa kamar gobe ya turo nasa iyayen. Asmau ta wuce a kirata wani bangare na jikinsa. Shine ita, itace shi. Da haka kawai zai iya kwatanta kaunar da yake mata. A sanyaye yaji muryarta yadda bata zaton zai ji tace "Jikamshi ina sonka" a hankali Wannan kalmar ta tsaya masa sosai a zuciya har ya fasa tafiya. Sake juyowa yayi ya ganta durkushe tana kuka. Shima durkusawa yayi a gabanta suna fuskantar juna "Matar Jikamshi kina so na hakura dake"? Girgiza kai tayi tana fitar da hawaye mai dumi. "To bazan hakura ba. Jikamshi yana son matarsa. Ki tashi ki koma ciki. Gobe in sha Allah zanyi magana ta fahimta da Hajjo tunda ita ce babba. Zan fada mata bazaki iya rayuwa da kowa ba sai Ishaq. Nima da ke kadai nake son karashe rayuwata. Duk shawarar da ta bayar da ita zanyi amfani." Tana hawayen amma murmushi take yi tana kallonsa. Yayi dariya "to dena kallona haka kada ki cinyeni kafin a daura auren" Ta sunkuyar da kanta kasa cikin kunya. "Ba fa kallonka nake yi ba." "Kallo na nawa kuma, a ciki ma ko kunyar Hajjo baki ji ba kika rinka satar kallona. Anya yarinyar nan baki fi karfina ba. Da ina yi miki kallon saliha amma yanzu ajinki daban ne" Murmushi kawai tayi ta rufe fuskarta da tafukan hannuwanta tace "zama da kai ne" "Indai nine baki ga komai ba. Kinga koma kada a fara cigiyarki. An saba maza ke zuwa zance amma yau kin kasa hakuri kin biyo ni. " Sai da ya rakata har kusa da dakin sannan ya dawo. A daidai inda suka gama magana yaga kamar alamar mutum. Ya dan juya yaji shiru sai kawai ya tafi. Qasim ne a wurin kuma duk yaji maganganunsu. Tun bayan fitowar Asmau ya biyo bayanta a zatonsa Col. Ishaq ya riga ya tafi. Rasa inda zaisa kansa yayi saboda a yau ya tabbatar ko kadan bata yi masa soyayya irin wadda yake fata. Duk wani tunaninsa ya kulle a yanzu shiyasa kawai ya shiga motarsa ya bar asibitin. ABINDA AKE GUDU🙆🏽44 Batul Mamman💖 A daren nan Qasim ya wuce Shanono. Abin duniya duk ya ishe shi. Dama wani lokacin baka sanin kana son abu sosai sai kaga alamun zaka rasa shi. Da gaske yake jin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103