Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 88

Chapter 88

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

so. Sai da tayi mai isarta yaji tana ajiyar zuciya. A zaune ma yake jingine da pillow yana kallonta ya rage hasken dakin sai fitilar gefen gado. Baiyi fushi ba ya matso kusa da ita ya sanyata cikin jikinsa. Fuskarta duk hawaye ta matsa kusa dashi itama don kokari harda zagaye hannuwanta a jikinsa ta kwantar da kanta a kafadarsa tana mayar da numfashi. Hankalinsa ya dan kwanta da yaji ta a jikinsa ya shafa mata kai "kukan me kika yi, dama akwai abinda zai saka ki kuka ki zabi yinsa ke kadai ki kasa fada min?" Saukar hawaye mai dumi yaji a kirjinsa tace "Jikamshina don Allah da gaske kana sona?" "Kinfi kowa sanin amsar tambayarki" Ta dago kanta tana fuskantarsa kunya sosai a tare da ita. Muryarta ce take nuni da rauni da ciwon dake cikin ranta "a yau na kara tsanar kaina da biyewa zuciya, nayi aure a matsayin budurwa amma na dade da rasa wannan darajar. Ban san na gama cutar kaina ba sai yanzu, lokacin da duk wata mace take jin ta isa a wurin mijinta idan ya sameta cikakkiyar budurwa. Na rasa wannan damar, bazan taba yi maka tinkaho da abinda bani dashi ba. Ina jin kunyarka ina jin kamar na cuceka ma...." Allah Sarki, tausayinta yaji ya kama shi sosai har tasa zuciyar ta raunana ya hanata karasa maganar ta hanyar da yasan dole tayi shiru. Sai da ya gama kissing dinta ya sanya yatsansa a saman bakinta. Tana kallonsa da fuskarta mai hawaye "ba karya kika yi min ba game da rayuwarki. Nasan komai kuma duk da haka Allah Ya sanya min sonki a zuciyata. ASMAU yarda da kaddara shine cikar musulunci. Abinda kika rasa bazai taba dawowa ba. Tunda kinsan baki da iko akansa babban abinda zaki yiwa kanki gata dashi shine hakuri da dangana. Mata da yawa suna aure a irin wannan yanayin kuma wasu sai kiga asirinsu ya rufu. Ke da naki ya fito fili kin zama misali ne ga sauran mata. Kinyi nadama kin tuba, kuma wannan ake nema daga dukkan musulmin kwarai. Allah Ya kara kare sauran mata daga haduwa da fadawa irin wannan sharrin." Wani kukan mai karfi yazo mata tace "wallahi sau daya ne...sau daya tsautsayi ya fada mana. Ka yafe min don Allah." Rungumarta yayi sosai a jikinsa duk dauriya irin tasa sai da yaji hawaye ya zubo daga idonsa. Ya Allah Ka nesanta mu daga tarkon zina. Mai zubar da kimar mai kima, ta zubar da girman babba, ta wulakanta mai daraja. Idan aka yita Allah zai iya yafewa wanda ya tuba amma wallahi tayi tambari kenan a rayuwar wanda yayi. A daidai kunnenta yace "Ashe duk yadda nake fada miki ina sonki baki taba yarda ba tunda har kike kokwonto a yau. Ban taba karyata zancenki ba. Da kinso tun ranar farko zaki iya cewa Safina ba 'yarki bace kuma zan yarda. Fatana Matar Jikamshi shine mu kasance ma'aurata har a aljannah." Ya kwantar da ita akan pillow yana kallon fuskarta "A daren yau nake so na goge miki duk wata damuwa da kika tsinci kanki a baya. Ina so na zama farincikinki. Ina so tarihin Asmau da Ishaq ya fara. A yau nake son rubuta kaina a zuciyarki. Ki yarda cewa kema abar so ce kuma da yardar Allah zakiyi rayuwar aure cikin jindadi kamar kowace mace. Abu daya kawai nake bukata yanzu daga gareki" Maganganunsa sun sanyaya mata zuciya. Tsoron da take ji na zata wayi gari taga canji daga gareshi saboda rashin cikarta yasa ta kuka. "me kake so" "Kice kina son mijinki" Sai da ta kalle shi tayi murmushi sosai sannan tace "I love you Ishaq, I love you Jikamshina. Ina sonka mijina" Ya riko fuskata a tafin hannuwansa ya matso da ita daidai da tasa yana mata wani irin kallo. "Lokacina da kika cinye kina kuka zaki fara biya yanzu" Kokarin guduwa tayi ya janyota ya danne tare da rufa musu bargo. Amarya da ango....asuba ta gari. _Mrs Othman Maman Jannah gaisuwa mai tarin yawa gareki_ ABINDA AKE GUDU🙆🏽55 Batul Mamman💖 Juyi Asmau tayi wanda yasa ta bude ido. Cikin na Col. Ishaq suka sauka da yake ta kallonta. A kwance take shi kuwa ya dora habarsa akan hannunsa daya ya zuba mata ido tana ta bacci. Ba karamar kunya taji ba tayi kasa cikin lallausan bargon da suka rufa dashi. Yana murmushi ya bude mata fuska tare da cewa "Na tasheki da kallo ko, duk laifinki ne da kika sa nake jin dama tun ranar da muka fara haduwa aka daura mana aure." Bai san irin yadda take jin kunyarsa ba. Ta rufe ido tana noke kai. Jin kanta take a takure kamar tayi tsuntsuwa ta gudu. Dama ya tabbatar da wuya yaji tayi magana. Duk da burinsa kunyarta ta ragu idan suna tare amma ya lura kamar karuwa tayi. Matsowa yayi daidai kunnenta yace "zaki iya tashi muyi sallah?" A hankali ta gyada masa kai sannan tace cikin wata karamar murya "asuba tayi?" Mamaki tayi domin gani take kamar yanzu ta rufe idonta ta fara bacci. Kamar yasan me take tunani yace "kina mamaki ne? Bayan kin cinye daren da kuka da ....." Da sauri ta rufe masa baki kafin ya fadi abinda yayi niyya. Ai kuwa ya ciji tafin hannunta a hankali ta cire shi daga bakinsa ta saki kara tana kwabe fuska zata yi masa kuka. Dariya ya fara da yaga da gaske kukan zata yi harda guntun hawaye ya kama hannun yana hurawa. "Yi hakuri my darling Asmau, matar soja bata kuka. Matar Jikamshi kuma ba raguwa bace" Kyale shi tayi yana rarrashinta ta daidaici kafadarsa sai saukar cizo yaji. Ta soma dariya da taga ya shige shi sosai ai kuwa suka fara kokawa yana cewa sai ya rama. Ga tsoron kada ya rama din da gaske ga dariya tana cinta. Tun yana zai rama har ya koma yana kallon yadda take dariya da hawaye a idonta. Ji tayi ya rungumeta a hankali "Allah Yayi miki albarka Matar Jikamshi. Yadda kike faranta min nima Allah Ya bani ikon yi miki haka." Nutsuwa tayi ta dena dariyar tana cewa amin ga adduarsu sai ga kiran assalatu. Col. Ishaq yayi saurin tashi "Kinga zaki sa mu makara ko? Na tashi da niyar nayi shirin zuwa masallaci sai na tasheki ne" "Ka tashi dai kana cin zalina daga zuwana gidanka" "Haka ma kika ce? Ji yadda kika cije ni fa. Ki zauna cikin shiri idan na dawo zan rama." Sai da ya fito daga bandaki ya saka doguwar riga zai tafi masallacin dake bayan layinsu yazo inda take kwance don bazata tashi yana dakin ba yace "ki kular min da kanki sai na dawo" ya kusa bakin kofa yaji tace "Allah Ya tsare min kai Ya dawo da kai lafiya" Yaji dadin adduar sosai har bazai iya kwantatawa ba "nagode Matar Jikamshi amma hakan bazai hanani ramawa ba idan na dawo." Daga haka ya fita itama ta tashi ta kimtsa tazo ta fara nafila. Bayan ta idar da sallolinta zama tayi tana ta mika godiyarta ga Allah. Hakika ta sami babban rabo da Allah Ya nufeta da yin aure duk da abubuwan da suka faru a rayuwar ta. Mata irinta nawa ne suke cikin tashin

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});