Chapter 71
Chapter 71
na zauna dashi ko na fito duniya ta zageni ace kila ma halin da nayi a baya ya sake kamani dashi." Umma tace "yanzu ke kina ganin zaki iya zama dashi a hakan. Bai fiye miki ba ki amincewa Qasim." "Umma ba karamar alfarma yayi mana ba da yace yana sona. Babu wata alaqa da ta hadamu fa. Rana tsaka ya ganni kuma yace yaji ya gani duk da abinda ya faru dani. Sai nake ganin bai dace ba naki shi saboda rashin haihuwa. Abinda bashi yayiwa kansa ba. Yaya Qasim kuwa nafi alakanta da tausayinmu yake ji " Jafar ji yayi Asmau ta burgeshi ba kadan ba. Kanwarsa ta ga rayuwa ta kuma hankalta da ita. A yanzu tasan so ba shine samu ba. Duk yadda ake son haihuwa a aure indai tana son kanta da arziki dole ne ta ajiye son ranta ta karbi abinda Allah Ya azurta dashi "Umma ni dai ina ganin indai tana sonsa kuma ta amince da lalurarsa a barta ta aureshi. Wallahi shi da Qasim bazamu manta dasu ba har abada. Duk da sun san komai game da ita suke son aurenta. Umma mu akayiwa alfarma ba mune zamuyi musu ba. A matsayina na yayan Asmau na bawa Col. Ishaq ita har abada" ya fada da murmushi. Shemau ma ta fahimci kanwarta yanzu ta kai masa duka a baya "to sannu waliyyin Asmau. Ai dai akwai manya gaba da kai" Nasiha mai ratsa jiki Umma tayi mata tare da bata goyon baya. A karshe tace "bamu ba wasu ma zasu hankalta idan suka ji labarin rayuwarki Asmau. Auren Ishaq zai iya rage miki gori da surutan mutane saboda wasu zasu ga kema kinyi masa hallaci. Shi Qasim sai a bashi hakuri tare da godiya domin ba karamin mutuntamu yayi ba. Allah Yayi muku albarka. Allah Ya kara kare mana zuria daga fadawa ga tarkon shaidan Ya yafe mana kurakuranmu baki daya." "Amin" suka amsa su uku. Bayan azahar kuwa da Asmau taje gidan Baba bata yi nauyin baki ba ta sanar dashi wanda ta amince wa. Sai da yayi ta tambayarta zata iya zama dashi babu haihuwa. Amsarta ko sau daya bata canja ba tace eh. Addua yayi mata shima da fatan alkhairi. Da rayuwarta bata zama yadda take yanzu ba bazasu yarda da wannan aure ba. To amma yanzu sun san cewa ba karamin arziki Allah Yayi musu ba da ya bata manemi kamar Col. Ishaq Muhammad Jikamshi. Zai rufa mata asiri itama ta rufa masa. Allah Mai hikima ne kuma Masani akan komai. Zuwa Shanono ya kama shi dole zai je yasan irin dabarun da zaiyi a warware maganar Qasim batare da zumunci ya sami rauni ba. ***** Su Asmau na zaune a tsakar gidan Kawu Garzali suna hira ta dauki waya ta turawa Jikamshi text. _Na zabi Jikamshina a matsayin miji. Na yarda na bashi amanar sauran rayuwata. Na amince babu wanda nake so sai shi kadai. Ina fata zaka amince ka karbi soyayyata. Kuma ina so ka sani cewa ba tausayinka nake ji ko auren alfarma nake nema ba. So ne kawai, Matar Jikamshi sai da Jikamshinta_ ***** Zaune yake gaban Hajiya tana yi masa nasiha saboda damuwa da tayi masa yawa yaji shigowar text din. Yana karantawa ya dago kai ya kalli Hajiyarsa yana murmushi mai burgewa "Hajiya ki fadawa su Kawu su shirya zuwa nema min auren Asmau" ABINDA AKE GUDU🙆🏽49 Batul Mamman💖 Bayan tayi text din duk da hira suke mintuna kadan sai ta duba wayar ko ya aiko mata da reply. Ganin babu bai sa taji komai ba. Naci zata kafa masa har sai ya amince don dole. Wannan shine abinda ta yankewa kanta zata yi masa. Haka kawai bazata bari Jikamshinta ya kasance cikin bacin rai da sadaukarwa ba shi kadai saboda wata lalura da bai isa ya yayewa kansa ba. Wani guntun murmushi tayi ta sake daukan waya. Kafin ta fara rubuta text din taji an kwashe mata da dariya. Shemau da su Sabira ne a wurin. Asmau ta dago kai tana kallonsu. Maijego Zubaida da Ainau shayar da yaransu suke amma suna tayawa wurin yi mata dariya. Ta dan ware ido "Me aka yi?" Sabira tace "me kuwa akayi banda kallonki da muke yi. Gaskiya wannan sojan ya cancanci a kira shi da gwarzon namiji." Ainau ta amshe "ai baku ga komai ba ma. Sai suna tare wallahi, abin sai ya baki shaawa. Shiyasa tuni na canja takuna wurin Yaya Umar. Muma mun zama Laila Majnu" "Lallai yaran nan kun koshi, a gaban nawa ko" Shemau ta fada amma fuskarta a sake. Sai yanzu Asmau ta gano wai da ita suke dariyar. Ta murmusa "to me nayi yanzu" Wannan karon Zubaida ce tayi magana "ke kadai kike ta kallon waya kina murmushi kamar yana kusa dake. Don Allah a bawa Qasim hakuri idan ya rabaku karshenta ku kamu da ciwon zuciya." Aka sake yin dariya. Shemau tace "da dai Asmau akwai kunya amma yanzu sai a hankali. Akan _Jikamshinta_bata gane su waye a kusa. Allah Ya kaimu lokacin buki a kaiki tun asuba kafin mu laluba muji amarya ta kai kanta. Suna dariya Asmau ta turo baki "amma kun gama dani wallahi. Kuma har yanzu da kunyata fa. Daga yau na dena magana ma" Sabira tace "Yi abinki Asmau, idan mutum na sonka kaima ka nuna masa baka da tamkarsa. Bari nima na kira Abban Abid mu dan taba hira. Yau tunda muka fito banji muryarsa ba" sai da ta gama magana ta tuna da Shemau. Tashi tayi da gudu ta shige daki. Tsakar gidan kuwa sai dariyar su Asmau. Sai yamma suka tashi tafiya gida. Hankalinta kwance kamar an cire mata dutse a zuciyarta. Duk da bata ga amsarsa ba ta gama yanke shawarar jurewa har sai ta shawo kansa ya amince. Ainau da Shemau tare suka tafi. Ita kuma ta bi Jafar da yazo daukar Sabira suka ajiyeta a gida. A bayan motar tana zaune da waya a hannu Amatullah tana wasa da Abid. Text din da bata sami damar yi ba dazu ta rubuta ta tura masa. _Don Allah kace kana sona....zanyi kuka fa._ Daga bakin gate suka sauka don lokacin har anyi magariba suna hanya. Tana tura gate din ta ga wata bakuwar mota a kusa da ta Umma. Bata damu da sanin mai motar ba ta shiga ciki tana sauri taje tayi sallah. Amatullah tace "Ummina muyi yige yigen shiga falo" Ta bi 'yarta da murmushi "idan na riga me zaki bani?" "Zan siya miki mota idan na giyma. Kuma zan kaiki Makkah da Madina" "Idan kuma kika rigani me kike so?" Amatullah tayi dariya harda alamar tunani "zaki goyani yau har nayi bacci." "Kin girma fa Ama ga nauyi" "to bazan ci abinci daye ba. Don Allah Ummi ki goyani" ta karashe da buga kafa. Asmau tace "naji shirya 1, 2....." kafin ta kai 3 Amatullah ta kwasa a guje. Dariya tayi kawai tabi bayanta. Yarinya sai son goyo bata san ta girma ba. Kyaleta tayi sai da ta kusa shiga sannan ta bita da gudu. Tana sane ta bari ta rigata. Da dariyarsu shiga falon Amatullah tana cewa ta riga. Asmau ma ta shigo da dariya sai tayi turus daga bakin kofa. Kamshin turarensa ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103